Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-21 16:39:32    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Kwanan baya, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da takardar bayani mai suna kiyayewa da bunkasa al'adun Tibet. Wannan ce takardar bayani a kan jihar Tibet ta bakwai da gwamnatin kasar Sin ta bayar.

Takardar bayani ta yi amfani da hakikanin abubuwa da alkaluma wajen gabatar da ayyukan kiyayewa da bunkasa al'adun Tibet da gwamnatin kasar Sin ta yi a cikin rabin karnin da ya wuce musamman ma bayan da aka fara gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida. Ban da haka kuma, ta nuna nasarorin koyo da yin amfani da harshen Tibet da kiyaye kayayyakin tarihi da abubuwan tarihi na al'adu da aka gada daga kakanni kakanni da kiyaye hakkin bin addini cikin 'yanci da bunkasuwar sha'anin ba da ilmi da yin nazari kan kimiyya da sauransu da kasar Sin ta samu tun daga zamanin 'yantar da Tibet cikin lumana a shekarar 1951 musamman ma bayan da aka fara yin gyare-gyare ta hanyar demokuradiyya.

---- Kwanan baya, babbar hukumar watsa labaru ta rediyo da sinima da talabijin ta kasar Sin ta bai wa jihar Tibet da ta Xinjiang kyautar filim din wasannin kwaikwayo na talabijin fiye da 40 wadanda aka fassara cikin harsunan kananan kabilu, wadannan wasanni kuma sun kasu kashi fiye da 1,000 wadanda suke samun kyakkyawar maraba daga wajen 'yan kallo bayan da aka nuna cikin talabijin, daga cikinsu har da wasannin kwaikwayo na talabijin da kasar Sin ta kaddamar wadanda ke da take da halaye da kuma jinsuna daban-daban.

An ce tun daga shekarar 2005, babbar hukumar watsa labaru ta rediyo da sinima da talabijin ta kasar Sin ta bai wa jihar Tibet da ta Xinjiang kyautar filim din wasannin kwaikwayo na talabijin fiye da 40 a kowace shekara wadanda aka fassara cikin harsunan kananan kabilu, wadanda kuma suka kasu fiye da kashi 1,000, wato yawan rukunan wasannin kwaikwayo na talabijin da aka ba da kyauta cikin shekaru 4 da suka wuce ya kai fiye da 4000, sabo da haka an warware matsalar karancin shirye-shiryen talebijin na harsunan kananan kabilu da ake da su a jihar Tibet da ta Xinjiang. Sa'an nan kuma kasashen da ke makwabtaka da Sin ciki har da Indiya da Kazakstan da Mongolia su ma suna iya kallon wasannin kwaikwayo na talabijin da kasar Sin ta watsa ta hanyar tauraron dan adam.