Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-20 17:06:11    
Bayani ne game da "Daolang Mukam"

cri
A karkashin dutsen Kalakulun na jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur da ke arewa maso yammacin kasar Sin, akwai wani kogi mai suna "Ye'erqiang", 'yan kabilar Uygur da ke zaune a yankin bakin kogin daga zuriya zuwa zuriya sun kiran wannan kogi da "Kogin Daolang", haka kuma ana kiran wadannan 'yan kabilar Uygur "Yan Daolang", wakokin da suke rerawa kuma ana kiransu "Daolang Mukam". A cikin shirinmu na yau kuma, za mu kawo muku bayani ne game da "Daolang Mukam".

Masu sauraro, wakar da kuke saurare a yanzu ita ce "Daolang Mukam" da "Yang Daolang" suka tsara. Fasahar wasanni ta "Mukam" wata babbar fasahar wasanni ce mai cikakken tsari da ke hade da kida, waka, da kuma rawa, ta kasance kide-kide iri goma sha biyu. Saboda halin musamman da fasahar "Mukam" ke da shi, a shekaru fiye da dubu da suka wuce, ta samu yaduwa ta hanyar sauya hannu daga baki zuwa baki a tsakanin 'yan kabilar Uygur. A ranar 25 ga watan Nuvamba na shekarar 2005, hukumar kula da ilmi da kimiyya da fasaha ta M.D.D. ,wato UNESCO ta mayar da "Mukam ta kabilar Uygur ta jihar Xinjiang ta kasar Sin" da ta zama "Wakiliyar al'adun gargajiya na tarihi da aka gada kaka da kakanni " a karo na uku. Fasahar Mukam ta kasance tamkar lu'u lu'u na fasahar wasannin kabilar Uygur, ita ce kuma abu mai daraja daga al'adu na kasar Sin.

A gun babbar gasar rera wakoki ta samari ta duk kasar Sin a karo na 13 da aka shirya a shekarar 2008, masu kallon gasar sun nuna mamaki sosai kan wakar "Daolang Mukam" da manoma 11 daga gundumar Maigaiti ta jihar Xinjiang suka rera, ta wannan waka kuma wadannan manoma sun samu lambar azurfa ta fasaha ta asali.

A 'yan kwanakin da suka wuce, wakilin gidan rediyonmu ya kai ziyara ga garin Yantake na gundumar Maigaiti ta jihar Xinjiang, wato wani wurin da fasahar "Daolang Mukam" ke yaduwa a ciki.

Wadannan masu rera wakoki asakinsu manoma ne, suna aiki a gonaki, amma a waje daya kuma mawaka ne na jama'a, su kan rera waka bisa ra'ayoyinsu, kuma suna mayar da rera waka, da raye-raye a matsayin ransu. Lallai sun nuna farin ciki, da fushi, da bakin ciki ta fasahar "Daolang Mukam".

An ce, a garin Yangtake na gundumar Maigaiti ta jihar Xinjiang, mawakan jama'a da ke iya rera waka tare da yin kide-kide sun wuce 200, ciki kuma Yu Shan Yaya, 'dan shekaru 69, da 'dan uwansa Ai Shan Yaya sun fi kwarewa kan wannan. Tun daga lokacin kuruciyarsu, 'yan uwan biyu sun soma koyon fasahar "Daolang Mukam" daga wajen mahaifinsu. Daga baya kuma, 'ya'yansu da jikokinsu su ma suna iya rera "Daolang Mukam" a karkashin tasirin da suke kawo musu. A 'yan shekarun da suka wuce, 'yan uwan biyu, da wasu abokansu sun fita waje bisa gayyatar da aka yi musu, don yin wasanni, kuma fasahar "Daolang Mukam" da suka nuna ta burge mutane daga kasashe daban daban.

Taliph Maimaiti, shugaban sashen al'adu na garin Yangtake na gundumar Maigaiti ta jihar Xinjiang ya bayyana cewa,

" Fasahar 'Daolang Mukamu' ta fi kyau bisa wasanni na asali. Na fito ne daga kauye, don haka ina jin farin ciki sosai saboda duk jama'ar kasar Sin sun san 'Al'adun Daolang", har ma jama'ar duniya kuma sun san al'adunmu."

A jihar Xinjiang, 'yan kabilar Uygur da yawa suna iya rera wakoki da yin raye-raye, ciki har da yaran da ke da shekaru 2 ko 3 na haihuwa, da kuma tsofaffin da ke da shekaru fiye da 80. Ana iya cewa, dukkansu su yada fasahar "Daolang Mukam tare".

Domin gudanar da ayyukan yadawa da kiyaye fasahar "Daolang Mukam" kamar yadda ya kamata, a 'yan shekarun da suka wuce, gundumar Maigaiti ta jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur ta kafa fayil ga wadannan masu aikin fasahar "Daolang Mukam", da kuma kyautata halin zaman rayuwarsu. A waje daya kuma, gwamnatin gundumar ta bayar da kudin musamman, don horar da masu gadon aikin fasahar mafi nagarta.

A da, an yada fasahar "Daolang Mukam" ga maza ne kawai, amma yanzu, wasu 'yan mata su ma sun shiga ayyukan fasahar, ta hakikanan ayyukan da suka yi kuma sun nuna cewa, suna kaunar garinsu, suna kaunar "Daolang Mukam", ta yadda za su iya zama masu aikin yada "Daolang Mukam".