Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-20 16:49:11    
Marayu 300 da uwarsu

cri
A lokacin da jama'ar kasar Sin suke yin koke-koken "kashe kudi da yawa domin ganin likita", asibitin nuna kauna ga marasa lafiya na birnin Xuzhou na lardin Jiangsu na kasar ya gabatar da sabis bisa makasudinsa na "rishin samun riba" don aikin likitanci ga jama'a matalauta na wurin, matsakaicin yawan kudin da yake karba daga kowane maras lafiya ya kai kudin Sin Yuan 18.7 kawai, wato ya kai kashi 20 cikin 100 bisa na sauran asibitoci. Tun da aka bude wannan asibiti zuwa yanzu, yawan marasa lafiya da wannan asibirin da ke da likitoci 30 kawai ya warkar da su ya kai fiye da dubu 15.

A ran 13 ga watan Agusta, masana'antar samar da hoto ta hanyar haske ta birnin Kunming na lardin Yunnan ta gama aikin samar da fasahar yin amfani da hasken da ake kira infrarend ray kuma ta fara aiki da shi, wannan yana nufin cewa, kasar Sin ta riga ta gina masana'anta mafi girma wajen samar da hoto ta hanyar haske, kuma ta riga ta samu karfin bunkasa irin wannan fasaha cikin 'yanci.

Mr. Su Weifu, sakataren kwamitin J.K.S. na kamfanin samar da fasahar yin amfani da hasken da ake kira infranred ray ta Dongfang ta birnin Kunming ya gaya wa manema labaru cewa, an ware kudin Sin fiye da Yuan biliyan daya domin wannan aiki, kuma an fara yin wannan aikin daga shekarar 2005, yanzu an riga an gama aiki kuma an fara aiki da shi daga duk fannoni, an kimanta cewa, yawan na'urorin samar da hoto da ta hanyar haske da za a kera ya kai 3500 a kowace shekara, yawan kudin da za a samu kuma ya kai fiye da Yuan biliyan 2 a kowace shekara.

Bisa sakamakon kididdigar da hukumar kididdiga ta gwamnatin yankin musamman ta Hongkong ta bayar an ce, zuwa tsakiyar shekara ta 2006, jimlar mutanen Hongkong ta kai 6,994,500. Idan an kwatanta su da na makamancin lokaci na shekarar 2005, sai a ga yawan mutanenta ya karu da 58,600, wato ya karu da kashi 0.8 bisa 100.

Sakamakon kididdigar kuma ya bayyana cewa, karuwar yawan jarirai da aka haife su da kuma mutane makaurata su ne muhimman dalilan da suka jawo karuwar mutanen Hongkong baki daya. Yanzu sai ku dan shakata kadan, daga bisani kuma za mu dawo domin karanta muku wani bayani dangane da Marayu 300 da uwarsu.

A birnin Fuyang na lardin Anhui da ke tsakiyar kasar Sin, da akwai wasu yara wadanda iyayensu suka mutu sabo da ciwon sida, shi ya sa suka zama marayu, suna shan wahaloli da zaman kadaici sosai. Wata rana, an samo wata mace wadda take da sunan "Uwa" ga wadannan marayu, daga nan ne wadannan yara suka fara zaman jin dadi. To, jama'a masu sauraro, a cikin shirinmu na yau na "Zaman rayuwar Sinawa", za mu karanta muku wani bayani game da wannan labari wanda yake da lakabi haka, "Marayu 300 da "uwarsu".

Jama'a masu sauraro, wakar da kuke saurara waka ce da wata yarinya mai suna Nannan ta rera, yarinyar nan kuma tana da shekaru 16 da haihuwa. Yau da shekaru 4 da suka wuce, iyayen Nannan sun rasu daya bayan daya sabo da ciwon sida, shi ya sa ta zama wata marainiya. Abun bakin ciki sosai shi ne, Nannan ita ma ta kamu da cutar ciwon sida daga wajen uwarta.

A daidai lokacin da yarinya Nannan ta fada cikin mawuyacin zama maras mafita, ta gamu da wata malama mai suna Zhang Ying wadda take da shekaru 37 da haihuwa. Yau da shekaru 10 da 'yan kai da suka wuce, madam Zhang ta fara aikin dillancin tufafi masu suna wato shahararru da sayar da abinci da abin sha na birnin Fuyang. Sabo da madam Zhang tana da hikima da zafin nama kumatana himmar aiki, shi ya sa ta yi suna a wurin wajen yin ciniki.

Wata rana da magariba a lokacin kaka na shekarar 2003, wani al'amari ya faru ba zato wato karo na farko ne madam Zhang Ying ta gana da yarinya Nannan, a lokacin kuwa yarinyar tana tsugune ne a kasa tana jin jiki sabo da ciwonta ya tashi. Madam Zhang ta nuna jin kai sosai ga yarrinyar sabo da matsanancin halin da take ciki.

"A lokacin kuwa, ba da jimawa ba ne da na haifi jariri na zama uwa, sabo da haka ina jin cewa yarinyar nan ta yi karama har haka, kuma ta rasa iyayenta daya bayan daya, wannan ya bayar da tausayi wa mutane sosai, ga shi kuma yanzu ita kanta ma tana kamuwa da ciwon sida, ta yi rashin damar zuwa makaranta sabo da ciwon. Lalle yarinyar nan tana bukatar taimako daga sauran mutane sosai."

Kashegari, madam Zhang ta aike wa Nannan wata rigar dari ta ulu da ta auduga, kuma ta kawo mata abinci da yawa, kafin ta tashi kuma ta bar mata da kudin Sin wato Yuan 300. Amma bayan komawarta gida ta nuna damuwa sosai cewa, ramammen jikin yarinyar da kuma wahalolin da take sha yau da kullum suna jawo hankalinta. A karshe madam Zhang ta tsai da kudurin kai yarinyar birnin Beijing don ganin likita.

"Na kai mata birnin Beijing a lokacin da ya rage sauran kwanaki 4 zuwa 5 da za a yi murnar bikin bazara. Sabo da kurewar lokaci, shi ya sa bayan saukawarmu daga jirgin kasa sai mu je asibiti kai tsaye. Bayan da muka isa asibitin, na yi ayyuka da yawa kamar biyan kudin asibiti da yin gwaji da daukar hoto domin ciwon yarinyar, da sayo mata abinci, na yi ta kai da kawowa cikin asibitin."

Bisa warkewar ciwon ya yarinya Nannan ta samu, kuma ta sake samun karfin zuciya ga yin zaman rayuwarta. Wata yarinya mai shiru-shiru a da amma yanzu ta sauya har ta zama mai kwazo da kuzari. Sauye-sauyen da Nannan ta samu sun faranta ran madam Shang sosai.

Irin marayun da suka rasa iyayensu sabo ciwon sida kamar yadda yarinya Nannan take sun yi yawa a birnin Fuyang. Sabo da yanki maras ni'ima, kuma ga wahalokin da suke sha a zaman yau da kullum, shi ya sa wasu manoma sun ga tilas ne su je sayar da jininsu domin samun kudi. Domin cin kazantacciyar biba, wasu mutane masu jan jini ba bisa doka ba sun yi amfani da kayayyakin asibiti masu kazantarwa, sabo da haka aka sa wasu manoma sun kamu da ciwon sida. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ko da yake gwamnatin kasar ta rubanya kokari don magance irin wadannan laifuffukan da aka barkata sosai, kuma ta ba da babban taimako ga mutane masu ciwon sida, amma har ila yau ya kasance da wasu marayu ciki har da yarinya mai suna Nannan.

A karshen shekarar 2003, madam Zhang ta yi biris da kiyewar da sauran mutane suka nuna mata, ta tsaya-tsayin daka ga yin watsi da cinikin da take yi wanda ya kawo mata riba wato ta samu kudin Sin Yuan miliyoyi, kuma ta kafa wata hadaddiyar kungiyar ba da taimako ga yara masu talauci kuma masu ciwon sida, ta dukufa kan aikin ceton marayu.

Zuwa yanzu, jimlar marayun da suka samu taimako daga wajen madam Zhang ying ta kai fiye da 300. A lokacin da take ba da gudummawa ga yara marayu, kuma ta samun kaunar zuci daga wajen wadannan yara sosai, har suna kiran ta "Mama" cikin soyayya.