Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-19 17:55:45    
Nasarorin da muka samu cikin shekaru 30 da suka wuce wajen yin mu'amalar al'adu tsakanin Sin da kasashen waje

cri
Tun sa'ilin da Sin ta aiwatar da tsarin bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 30 da suka gabata har zuwa yanzu. Al'adu sun riga sun zama tamkar wata gada ce da ta hada Sin da kasashen waje. Nasarorin da aka samu wajen mu'amalar al'adu tsakanin gwamnati da jama'ar Sin da kasashen waje sun kai wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba.

To, masu saurarommu, wannan wasan da kuka saurara shi ne wasannin Opera na Beijing mai suna Sha Jiabang, kuma a cikin wannan wasa, an nuna mana labarin da aka rubuta a lokacin yakin basasa a kasar Sin, kuma ya sami karbuwa a kasar Sin a shekaru 60 da shekaru 70 na karnin da ya wuce. A wancan lokaci, ba a samu hanyoyin jin dadi kamar yadda muke da su yanzu ba. Matasan Sin na yanzu ba za su iya fahimtar zaman rayuwar da ba, a gidajen jama'a babu telebiji, haka kuma a cikin garin, babu dakunan rera waka kuma babu dakunan raye-raye, kuma abin da mutane ke iya samuwa kawai shi ne dakunan wasannin kwaikwayo, an nuna wasannin "Sha Jiabang" har na tsawon shekara daya a dakunan wasannin kwaikwayo.

Mr. Zhang Yu mai shekaru 50 da haihuwa, ya ganewa idonsa nasarorin da aka samu wajen yin mu'amalar ala'du tsakanin Sin da kasashen waje. Yanzu ga shi ya riga ya zamanto babban manaja na kamfanin al'adu wajen yin mu'amala tare da kasashen waje, haka kuma shi ne daya da ke cikin fitattun mashawarta kuma masu tsara shirin wasannin kwaikwayo na Sin, haka kuma, da ma, ya taba zama jami'i mai kula da harkokin mu'amalar al'adu tare da kasashen waje. A shekarar 1982, bayan da ya gama karatu a jami'a, sai aka ba shi aiki a hukumar tuntubar kasashen waje ta fannin al'adu ta ma'aikatar al'adu ta kasar Sin, a farkon shekaru da dama, ya dauki nauyin karbar bakuncin kungiyoyin mu'amalar al'adu na gwamnatocin Asiya da Afrika da Latin Amurka da suka kawowa kasar Sin ziyara. A shekarar 1990, ya yi murabus daga mukaminsa daga ma'aikatar gwamnati, kuma ya yi aikin wasan kwaikwayo a ketare kuma ya kula da aikin yalwata wasannin kwaikwayo na Sin.

"A cikin shekaru 30 da suka gabata, mun nuna wasanni da dama, a ko wane zamani, ko wane wata, ko kuwa ko wane mako, haka kuma mun nuna wasanni masu kayatarwa a biranen Sin da dama. Alal misali, a birnin Beijing, mun nuna wasanni a katafaren dandalin wasan kwaikwayo da sauran muhimman dakunan wasannin kwaikwayo da dai makamantansu, kuma a ko wane dare, muna nuna wasanni na Turai da Amurka da Asiya da Latin Amurka da kasashen Larabawa. Wasanni da yawa sun kara ciyar da mu'amalar al'adu tsakanin Sin da kasashen waje, kuma wannan babbar nasara ce da muka samu cikin shekaru 30 da suka gabata.

Zhang Yu ya bayyana cewa, yanzu kasuwar wasanni ta Sin tana ci ba kamar a lokacin da ba.

Wannan wakar da kuka saurara ita ce "Taurari" da shahararen makida na Japan Shinji Tanimura ya rubuta. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, an gayyace shi da ya kawowa kasar Sin ziyara don halartar "wasannin Daren Asiya". A hakika dai, tun daga shekaru 27 da suka wuce, a gun taron wake-wake na Beijing na "Hand In hand" da aka yi a dakunan da filayen wasannin motsa jiki na ma'aikatan Beijing, Shinji Tanimura ya fara nuna wasanni tare da sauran mawakan Sin tare.

A lokacin gasar wasannin Olympic. Ma'aikatun da abin ya shafa sun shirya bukukuwa da dama ta fannin ala'du, kuma ya jawo hankulan kungiyoyin wasanni 100 da suka zo daga kasashe da yankunan fiye da 80, kuma masu fasahohi kimanin dubu sun kawo wa kasar Sin ziyara. Kafofin yada labaru sun bayyana cewa, Sin ta zama wani yankin da ya bunkasa sosai wajen nuna wasan kwaikwayo na duniya da kuma yin mu'amala wajen fasahohi. Yawan masana'antu masu sana'ar al'adu na kasashen waje da ke kasar Sin da masu fasaha sun fara karuwa.

Lisa Cliff mai shekaru 41 da haihuwa da ta taba kawowa kasar Sin ziyara a shekarar 1991, kuma a wancan lokaci ta zama wata marubuciya, daga bisani kuma ta canja aikinta, ta zuba jari a kan zane-zane da fasahar sassaka, ta bude kamfanoni guda biyu masu suna OKO a unguwar kasuwanci da ta fi wadata ta Beijing ta Soho da unguwar fasaha da ta shahara wajen fasaha ta 798. Lisa Cliff ta shiga cikin wannan sana'a har shekaru da dama, kuma ta san kasuwar fasaha ta Sin, kuma tana cike da imani a kan makomar al'adu na Sin.

"Ina sha'awar kasuwar fasaha ta Sin, bayan da na iso kasar Sin, na ga kasuwar fasaha ta Sin ta cimma nasara sosai. Musamman ma ta yadda gwamnatin kasar Sin ta yi hakuri ga bambancin ala'du, sabo da haka muna cike da imani a kan makomar sana'ar al'adu. Musamman ma bayan da aka yi gasar wasannin Olympic ta Beijing, a ganina, gaskiya lokaci ya yi da na kara sana'ata.

Shagon Lisa yana unguwar fasaha ta 798, kuma yana arewa maso gabashin birnin Beijing, da ma, wannan wuri, shi ne wani rumfunan masana'antu da ba safai a kan yi amfani da su ba. Amma tun daga shekarar 2002 har zuwa yanzu, sai hukumomin fasaha da dakunan studio na masu fasaha suka fara shiga ciki, daga bisani kuma, sai wannan wuri ya zama wata unguwa ce da ta cike da dakunan zane-zane da kamfanoni fasali da shagunan da ta sayar da abubuwan fashion da dakunan cin abinci, haka kuma ta kasance wata unguwar fasaha da ta shahara a duniya, ba ma kawai ta jawo hankula masu fasaha na Sin ba, haka kuma ta jawo hankulan mutanen kasashen waje kamar Lisa. Hukumomin fasaha da 'yan kasuwa na kasashen waje da suka zuba jari a nan sun yi yawa,.

Kamfanin tsara wasanin kwaikwayo na kide-kide na duniya watau kamfanin Cameron Mackintosh ya fara shirya kafa wani kamfani a kasar Sin a shekarar bara, don su yi wasannin kwaikwayo a nan kasar Sin, kuma da ma a shekarar 2003, kamfanin Cameron Mackintosh ya bayar da sanannen rubutunsu na "kyanwa" a kasuwar Sin, kuma ya cimma nasara sosai. Babban jami'i mai zartaswa na wannan kamfani Mackintosh yana ganin cewa, yanayin zuba jari na Sin da ya yi sasauci ya jawo hankalinsa.

"Ina farin ciki sosai, sabo da gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon baya gare ni, don ingiza bunkasuwar sana'ar wasannin kwaikwayo na kide-kide, don sanya su cikin ala'du na Sin, gare ni, bayan da aka nuna wasan kwaikwayo na Sin ya yi kamar ya zama tamkar wani iri, ina fatan nan ne zai zama dajin itace na Opera. Bisa daya da ke cikin mutane masu sana'ar yin wasannin kwaikwayo cikin kide-kide, babban kalubalen da ke gabammu wajen yin wasannin kide-kide a kasar Sin ya fi burge ni.(Bako)