Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-19 15:55:15    
Matasa 2 na kasar Sin suna namijin kokari domin samun lambar zinariya ta farko a cikin wasan kankara na salo-salo a gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu

cri
A cikin gasar ba da babbar kyauta ta duniya ta cin kofin kasar Sin ta wasan kankara na salo-salo ta shekara ta 2008 da aka rufe a kwanan baya, 'yan wasa Zhang Dan da Zhang Hao na kasar Sin sun zama zakaru a cikin gasar wasan kankara na salo-salo a tsakanin namiji da mace bisa fasaharsu ta nuna wasan mai kyau sosai. Wadannan 'yan wasa matasa 2 da suka sami lambar azurfa a cikin gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Turin a shekara ta 2006 suna nan suna namijin kokari domin samun lambar zinariya a cikin shirin wasan kankara na salo-salo na gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu, wadda ita ce lambar zinariya ta farko a tarihin kasar Sin.

A ranar gasar, bayan da Zhang Dan da Zhang Hao suka kammala wasansu, a dukkan dakin wasa, 'yan kallo sun jefa abubuwan wasa manya da kanana masu yawa kan kankara don yabawa.

A lokacin gasar, tare da kide-kiden da aka yi da kayan wasa na piano wato 'kogin Yangtse' da kuma 'mahaifarmu kasar Sin' masu halin musamman na kasar Sin, Zhang Dan da Zhang Hao sun sami nasarar kammala wani irin tsalle-tsalle mai matukar wuyar kammalawa a sa'i daya, a cikin dukkan 'yan wasa 14 da suka shiga gasar a waccan rana, su ne kawai suka kammala irin wanann tsalle-tsalle, sa'an nan kuma, sun kammala sauran rassan aikinsu yadda ya kamata ba tare da matsala ba, shi ya sa a karshe dai wadannan 'yan wasan kasar Sin matasa suka zama zakaru tare da samun amincewa daga kowa da kowa. Bayan gasar, Zhang Hao ya bayyana cewa, samun wannan lambar zinariya a dakin wasa na Beijing yana da ma'anar musamman a gare shi. Ya ce,"Yau a wannan dakin wasa, muna matukar farin ciki saboda mun zama na farko. Wannan lambar zinariya tana da ma'anar musamman a gare mu, saboda a ran 20 ga watan Oktoba na shekara ta 1998, a cikin gasar fid da gwani ta wasan kankara na salo-salo ta matasa da yara ta duniya da aka yi a wanann dakin wasa, mun zama zakaru kamar yadda muka yi a yau. Shi ya sa bayan shekaru 10, muka sake zama na farko a nan, muna matukar farin ciki."

Yao Bin, babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kankara na salo-salo ta kasar Sin shi ma ya gamsu da kyakkyawan aiki da Zhang Dan da Zhang Hao suka yi. Ya ce,"Ba su yi babban kuskure ba. Sun sami ci gaba a fannonin kammala wasu muhimman sassa da cikakken nune-nunensu da salon nune-nunensu."

Zhang Dan mai shekaru 23 da haihuwa da kuma Zhang Hao mai shekaru 24 da haihuwa su ne 'yan wasa na matsayin duniya a cikin wasan kankara na salo-salo a tsakanin namiji da mace baya ga Shen Xue da Zhao Hongbo da kuma Pang Qing da Tong Jian a kasar Sin. Kafin wannan kuma, Zhang Dan da Zhang Hao sun taba samun maki mai kyau a cikin wasu manyan gasannin duniya. Bayan da Shen Xue da Zhao Hongbo suka yi ritaya, wadannan 'yan wasan kasar Sin matasa, wadanda wuyar aikinsu ta zama ta farko a duniya, sun zama masu jagora a fannin wasan kankara na salo-salo a kasar Sin. Game da Zhang Dan da Zhang Hao, 'yar wasa Tatiana Volosozhar ta kasar Ukraine da ta zama ta biyu a cikin gasar wasan kankara na salo-salo a tsakanin namiji da mace a wannan karo, ta nuna girmamawa ga nasarar da Zhang Dan da Zhang Hao suka samu, kuma ba tare da boye kome ba tana farin ciki, ta ce,"Ina son nune-nunen da suka nuna mana sosai. A lokacin gasar, sun nuna karfi sosai, haka kuma, su kan kara sabbin abubuwa a cikin nune-nunensu, su kan bi sabon salo, kamar wasu motsin hadewa masu ban sha'awa, shi ya sa in ana cewa, matsayin wasan kankara na salo-salo na duniya na samun saurin kyautatuwa, to, Zhang Dan da Zhang Hao da kuma Pang Qing da Tong Jian su ne suka iya shaida mana wannan zance."

Amma duk da haka, Zhang Dan ta nuna mana cewa, ko da yake yanzu sun sami wasu nasarori, amma suna fatan za su iya kyautata kwarewarsu a fannin nuna ainihin kide-kide da kuma fasahar wasan kankara na salo-salo a tsakanin namiji da mace a sakamakon aiki tukuru. Ta ce,"Bayan da muka sami nasara a wannan karo, to, za mu bar wannan lambar zinariya, za mu ci gaba da aikin horaswa, za mu kyautata abubuwan kasawa domin samun maki mai kyau a nan gaba. Ko da yake mun sami lambar zinariya, amma muna fatan za mu kyautata kwarewarmu ta yin nune-nune masu ban sha'awa a kan kankara."

Domin kyautata kwarewarsu ta nuna fasahar wasan, a shekaru da dama da suka wuce, Zhang Dan da Zhang Hao sun yi ta yin gwaje-gwajen yin amfani da kide-kide na salo daban daban, kuma tare da taimakon kwararru na gida da na waje, suna kokari kan kyautata fahimtarsu da kwarewarsu ta nuna ainihin kide-kide. A cikin gasar da aka yi a wannan karo, sun zabi kide-kiden da ke nuna ruhun al'ummar kasar Sin.

Game da kide-kiden, Zhang Hao ya yi karin bayani cewa,"Mun riga muna wasa tare har tsawon shekaru 10. Mun taba amfani da kide-kide na salo daban daban. Dalilin da ya sa muka zabi wannan kida na Kogin Yangtse shi ne domin muna kishin kasarmu ta mahaifa sosai. A ganina, wannan kida na nuna halin musamman na al'ummarmu sosai, haka kuma, yana da ma'anar musamman."

Baya ga namijin kokari wajen kyauatata kwarewarsu ta nuna ainihin fasahar wasan sosai, domin neman samun lambar zinariya a gun taron wasannin Olympic na lokacin hunturu a shekara ta 2010, yanzu Zhang Dan da Zhang Hao suna himmantuwa wajen inganta tunaninsu. Zhang Hao ya gaya mana cewa,"Wasan kankara na salo-salo ya hada da abubuwa da yawa. Samun nasarar kammala tsalle-tsalle kawai bai iya tabbatar da samun lambar yabo ba. Wasan ya bukaci 'yan wasa su yi fintikau a fannonin wuyar fasaha da kwarewar nuna ainihin fasaharsu da kuma hadewa da sassan nune-nune. Ta haka muna bukatar kyautata tunaninmu bisa babban mataki. A cikin aikin horaswa na yau da kullum, ko da yake ka iya kammala aikin horaswa a saukakke, babu abubuwan kasawa, amma a cikin gasar da take matsayin dama daya tak a gare ka, ba yadda za ka yi, sai ka fuskanci sau daya tak na kammala nune-nunenka. Shi ya sa abu mafi muhimmanci a gare ka shi ne kyautata tunaninka, ta haka, za ka iya kammala nune-nunenka yadda ya kamata, za ka iya nuna ainihin fasahar wasanka."

A gabannin gasar wasannin Olympic ta Beijing, Zhang Dan da Zhang Hao sun shiga aikin mika wutar gasar wasannin Olympic a birnin Harbin da ke arewa maso gabashin kasar Sin a matsayin mai rike da wutar na farko. Kafin a sa aya ga aikin a wancan rana, Zhang Dan tana rike da wutar a hannunta, Zhang Hao kuwa ya daga Zhang Dan a sama kamar yadda ya kan yi a cikin gasanni. Game da wannan, Zhang Hao yana murmushi, ya gaya mana cewa,"Daga ta a daidai wancan lokaci na da ma'ana mai muhimmanci. Wannan yana da kyan gani sosai. Na kara daga Zhang Dan, kana kuma, na kara daga wutar."

To, yanzu mun yi amfani da abubuwan da Zhang Hao ya fada domin nuna fatan alheri a gare su, muna fatan a gun gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu a shekara ta 2010, Zhang Dan da Zhang Hao za su tsaya a kan kolin dandamalin ba da lambobin yabo.(Tasallah)