Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 16:59:55    
Me ya sa aikace-aikacen 'yan fashi na teku suka yawaita a tekun kasar Somaliya

cri

Jama'a masu sauraro. Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na Afirka a yau. A cikin shirinmu na yau za mu gabatar muku da wani rahoto mai lakabi ne kamar haka: Me ya sa aikace-aikacen 'yan fashi na teku suka yawaita a tekun kasar Somaliya.

A kwanakin baya, an samu aukuwar al'amura da yawa na 'yan fashi masu makamai na teku inda suke yin garkuwa da jiragen ruwa da ke wucewa a tekun kasar Somaliya da ke gabashin nahiyar Afirka. Ran 16 ga wata, ma'aikatar harkokin waje da kuma ciniki ta kasar Korea ta kudu ta ba da tabbaci cewa, a ran 15 ga wata da dare ne aka yi garkuwa da wani jirgin ruwa da ke dauki da kayayyaki na kasar Japan a tekun da ke gabas da kasar Somaliya. Kafin wannan kuma a ran 13 ga wata da dare, 'yan fashi sun shiga tekun kasar Kenya sun yi garkuwa da wani jirgin ruwa kamun kifaye na kamfanin kamun kifaye na birnin Tianjin na kasar Sin, wannan jirgin ruwa na kasar Sin na uku ne da suka yi wa fashi a cikin rabin shekara da ya wuce. Masu bincike suna ganin cewa, kasar Somali tana cikin yaki da rudani na dogon lokacin da ya gabata, wannan ya haifar da yawaitar 'yan fashi, dan haka ba za a iya warware matsalar 'yan fashi na kasar Somali ba, sai dai an daidaita mummunan halin da ake ciki.

Bisa kididdigar da hukumar harkokin teku ta kasashen duniya ta yi, an ce, an samu aukuwar al'amura 87 na yin fashi ga jiragen ruwa a tekun kasar Somaliya a cikin watanni 10 na farkon shekarar da muke ciki, wannan ya kai kashi 40 cikin 100 na dukkan aukuwar irin wannan lamari da suka faru a duk duniya a wannan lokaci. Ya zuwa yanzu, akwai jiragen ruwa 11 da ma'aikata fiye da 200 da ke cikin hannun 'yan fashi.

Yanzu, 'yan fashi da ke tekun kasar Somaliya suna da jiragen ruwa masu saurin tafiya, da manyan makamai, da na'urori masu fasaha na zamani, ciki har da wayar da ke yin amfani da kumbo, da GPS, wato tsarin tauraron dan Adam mai nuna matsayin da ake ciki. Ban da haka kuma, 'yan fashi ba su damu da asalin jiragen ruwa da suka yi garkuwa da su, suna neman kudin fansa da yawa. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan kudin fansa da 'yan fashi suka samu a shekaru biyu da suka wuce ya kai da;ar Amurka fiye da miliyan 30. Abu mafi tsanani shi ne, ban da tekun kasar Somaliya, 'yan fashi sun fara yin laifuffuka a tekun duniya, har ma su shiga tekun kasar Kenya da ke makwabtaka.

Masu bincike suna ganin cewa, laifuffukan da 'yan fashi na teku suka yi suna da yawa kwarai saboda da farko, ana yakin basasa da kuma kasancewar cikin halin rashin samun tsayayyar gwamnati cikin dogon lokaci a wannan kasa. Tun daga shekarar 1991, aka fara yin yakin basasa a kasar Somaliya. Na biyu, an samu bangarori daban daban cikin kasar Somaliya sakamakon rashin gwamnati mai karfi. Dakaru masu adawa da gwamnati suna iya sayo makamai idan suka ga dama. Sabo da haka suke yi wa jiragen ruwa fashi domin neman kudin fansa. 'Yan fashi sun nemi kudin fansa na dalar Amurka daga dubu 500 zuwan miliyan 2 a kiyasce ga ko wane jirgin ruwa da suka yi garkuwa da shi.

Laifuffukan da 'yan fashi suke yi sun jawo hankulan kasa da kasa. A watan Yuni na shekarar da muke ciki, kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya zartar da wani kuduri, inda ya yarda da jiragen ruwa na yaki na kasa da kasa, za su iya shiga tekun kasar Somaliya bayan da suka samun amincewar gwamnatin kasar. A farkon watan Oktoba, ya zartar da kuduri na biyu, ya yi kira ga kasashen da ke kula da tsaro kan teku da su dauki matakai su yi hadin gwiwa tare da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya domin kai farmaki ga 'yan fashi da ke tekun kasar. Ban da haka kuma, wannan kuduri ya yi kira ga cigaba da daukar matakai domin kare jiragen ruwa na hukumar WFP, wato shirin samar da abinci na duniya, ta haka domin tabbatar da ayyukan samar da taimakon jin kai ga kasar Somaliya. Ban da haka kuma, kasashen Amurka, da Jamus, da Faransa, da Kungiyar tarrayar kasashen Turai, da India, da Japan da Kenya sun nuna cewa, za su sa hannu cikin ayyukan kai farmaki ga 'yan fashi.