Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-18 16:13:46    
Ziyarar shugaba Hu zuwa Latin Amurka za ta ciyar da huldar tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka gaba, in ji kwararru

cri
Ran 16 zuwa ran 17 ga watan Nuwamba, bisa loakcin wurin, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kai ziyararsa a karo na farko zuwa kasar Costarica da ke nahiyar Latin Amurka. Sa'an nan bayan Costarica zai cigaba da ziyarar kasahen Cuba da Peru, kuma zai hallarci kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki ta nahiyar Asiya da tekun Pasific ta APEC na zama na 16, wanda za a yi shi a kasar Peru. Dangane da ziyarar shugaba Hu, wasu kwararru na ganin cewa, ta janyo hankulan bangarori daban daban na nahiyar Latin Amurka, sa'an nan za ta inganta huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka.

Kasashen Sin da Costarica sun kulla dangantakar Diflomasiyya a watan Yuni na shekarar bara, daga baya Oscar Arias Sanchez, shugaban kasar Costarica ya kai ziyara a kasar Sin a watan Oktoba na shekarar bara. Ziyarar da shugaba Hu ya kai wa kasar Costarica ita ma karo na farko ne da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar. Kan batun nan, Mista Xu Shicheng, kwararren kasar Sin manazartar sha'anin Latin Amurka yana da ra'ayin cewa, 'Ziyarar za ta yi nagartaccen tasiri kan dagantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Costarica, sa'an nan za ta inganta huldar tsakanin Sin da nahiyar Amurka ta tsakiya. A lokacin ziyararsa, shugaba Hu ya sa hannu kan yarjejeniya 11 tare da takwaransa na kasar Costarica, haka kuma, bangarorin 2 suka sanar da cewa za su yi shawarwari don neman kulla yarjejeniyar aikata kasuwanci cikin 'yanci.'

Kan halin da wasu kasashen nahiyar Amurka ta tsakiya ke ciki na ba su kulla hulda da kasar Sin ba tukuna, Mista Xu ya ce, 'Cikin takardar nuna manufar kasar Sin dagane da Latin Amurka da yankin Caribbean wadda gwamnatin kasar Sin ta fito da ita a ran 5 ga watan Nuwamba, an ce, kasar Sin tana da nufin kulla dangantaka da kasashen Amurka ta tsakiya, bisa sharadin farko na yarda da kasancewar kasar Sin daya tak. Sa'an nan ba mu kin jinin huldar cinikayya da kasashen Amurka ta tsakiya suka yi da yankin Taiwan.'

A baya ga haka kuma, ziyarar shugaba Hu zuwa Latin Amurka na da sauran ma'ana, bisa mawuyacin halin da kasashen duniya ke ciki na fama da rikicin hada-hadar kudi. Martin A. Rodriguez, wani kwararren kasar Argentina da ke nazarin huldar tsakanin Sin da Latin Amurka, ya ce, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan inganta bunkasar tattalin arziki da cinikayya a nahiyar Asiya da tekun Pasific. 'A ganina, ziyarar shugaba Hu Jintao zuwa latin Amurka aka yi ta ne bisa lokaci mai dacewa, sa'an nan ta kawo wa kasashen Latin Amurka imani da fatan alheri kan bunkasuwarsu cikin shekaru masu zuwa. A hakika kuma, ziyarar shugaba Hu da takardar nuna manufar kasar Sin kan dangantakarta da kasashen Latin Amurka da na yankin Caribbean sun riga suka haifar da hauhawar farashin wake da sauran kayayyakin, wandanda kasashen Latin Amurka suke kan gaba wajen yawan sayar da su zuwa kasuwannin duniya. Wadannan abubuwa sun kawo wa kasashen Latin Amurka imanin cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasahenmu za ta samu cigaba lami lafiya.'

Har wa yau kuma, Mista Rodrigues ya ce,yanzu kasashen Latin Amurka da yawa na kokarin neman samun zuba jarin da kamfanonin kasar Sin suke yi, haka kuma kasar Sin ta kawo wa kasashen Latin Amurka damar bukasa. 'kasar Sin na bunkasuwa kan tattalin arziki, sa'an nan tana kara bukatar shigo da kayayyaki daga waje. Kayayyakin Latin Amurka za su ishe bukatun kasuwannin kasar Sin.'(Bello Wang)