Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-17 16:41:15    
Taron koli na G20 ya kara aniyar duk duniya ta tinkarar rikicin da take fama da shi

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an kawo karshen taron koli na shugabannin G20 kan kasuwannin hada-hadar kudi da yanayin tattalin arzikin duniya a ranar Asabar da ta gabata. Wasu kwararru na kasar Sin a fannin tattalin arziki sun bayyana ra'ayoyinsu cewa, ko da yake taron kolin bai kaddamar da wani kyakkyawan shirin tinkarar rikicin hada-hadar kudi ba, amma duk da haka, sanarwar da bangarori daban-daban mahalarta taron suka bayar ta kara aniyar kasashe daban-daban na duniya ta tinkarar rikicin da suke fama da shi; A lokaci guda, sun cimma daidaito bisa manufa kan yin kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya.

A gun taron kolin, gaba dayan shugabannin da suka zo daga kasashen da suka fi samun arziki da kuma kasashe masu tasowa sun jaddada cewa, ya zama dole a kara daukar kwararan matakai ta fuskar manufa bisa tushen kara kyautata harkokin tattalin arziki daga dukkan fannoni, da zummar rage tasiri da rikicin hada-hadar kudi da kuma tafiyar hawainiyar harkokin bunkasuwar tattalin arzikin duk duniya suke yi, da kuma tallafa wa kasashe masu tasowa. Ban da wannan kuma, taron kolin ya yi kira ga kasashe daban-daban da su aiwatar da manufar da ta wajaba a fannin kudade da nufin goyon bayan karuwar tattalin arziki da kiyaye kwanciyar hankalinsa.

Mista Zhang Jun, daraktan cibiyar nazarin tattalin arzikin kasar Sin daga Jami'ar Fudan ya furta cewa: " A ganina, wata alama mafi girma da muka samo daga taron kolin, ita ce karin aniya. Shugabannin G20 sun taru ne domin sanar da duk duniya cewa suna so su kyautata ayyukansu da kuma tsara shirin aiwatarwa, ta yadda za a kara magance karin matsanancin rikicin hada-hadar kudi, musamman ma koma-bayan tattalin arziki na dahir".

Jama'a masu sauraro, wata muhilmmiyar manufa da kasashe masu hannu da shuni ke aiwatarwa wajen goyon bayan bunkasa tattalin arziki ita ce rage yawan ruwa. Amma taron kolin ya yi tayi a fili ga kasashe daban-daban da su kaddamar da manufar da ta wajaba a fannin kudi. Tuni a gabannin kiran taron kolin, gwamnatin kasar Sin ta fito da shirin farfado da tattalin arziki, wanda jimlar kudinsa ya kai kudin Sin wato Renminbi biliyan 4,000. Hakan ya yi kyakkyawan tasiri a fadin duk duniya. Mista Zhang Jun ya kara da cewa: " Kasaitaccen shirin da gwamnatin kasar Sin ta fito da shi ya fi janyo hankulan mahalarta taron kolin; Wannan dai ya kuma samar da wata alama ga kasashe masu tasowa da dama wajen yin koyi da shi. Labuddah hakan zai yi kyakkyawan tasiri ga tattalin arzikin duk duniya".

Aminai 'yan Afrika, shugabannin kasashe daban-daban mahalarta taron kolin sun cimma daidaito bisa manufa kan wassu ka'idoji dangane da yadda za a yi kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya. Wadannan ka'idojin sun tanadi cewa, za a sake gyaran fuskar kungiyoyin kudi na kasa da kasa ,wato ke nan za a shigo da karin sabbin mambobin kungiyoyin dahir na tattalin arziki da suka hada da kasashen Sin da Brazil da kuma India, wadanda za su kara taka muhimmiyar rawa a cikin sabon tsarin kudi na duniya.

A matsayin wata abar dahir ta tattalin arziki, wadda ta zo ta hudu a fannin sikelin bunkasuwar tattalin arziki a duniya kuma tana kan gaba a fannin yawan ajiyar kudin waje, mahalarta taron sun yi begen kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a yunkurin gyare-gyaren tsarin kudi na duniya. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya alkawarta a gun taron kolin cewa, kasar Sin tana so ta cigaba da sauke nauyin da ke bisa wuyanta na shiga yunkurin zaunar da kasuwannin hada-hadar kudi na duniya da kuma ingiza hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasa da kasa domin bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. Mista Gong Fangxiong, masanin ilmi na farko a fannin tattalin arziki na shiyyar Asiya da tekun Pasicic ya furta cewa: " Kamata ya yi mu nuna himma da kwazo wajen neman matsayi da kuma hujjoji da ya kamata mu samu. Sai dai muka yi haka ne za mu iya samun sakamakon da muke so bayan mun biya kudi". ( Sani Wang )