Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-14 18:47:07    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kaddamar da ziyararsa a Latin Amurka da Turai

cri

A ran 14 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi daga birnin Beijing domin kaddamar da ziyararsa ta makwanni biyu. Kuma a lokacin ziyararsa, shugaba Hu zai halarci taron koli na G-20 da taron koli na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen Asiya da Pacific wato APEC, haka kuma zai ziyarci kasashen Costa Rica da Cuba da Peru da Girka. Ta wannan ziyarar shugaban kasar Sin, ba kawai za a iya bayyana matsayin Sin da kuma ra'ayoyin da take dauka a kan matsalar kudi da kuma sauran muhimman batutuwan da ke jawo hankalin mutane ba, a'a har ma za a iya nuna hadin gwiwar Sin da kasashen da abin ya shafa a nan gaba. To yanzu ga cikakken bayani.

Birnin Washington zango ne na farko na wannan ziyara ta shugaba Hu Jintao, inda za a kira taron koli na kasuwannin kudi na G-20 da kuma tattalin arzikin duniya a ran 15 ga wata da safe. Ana sa ran alheri sosai kan hadin gwiwar kasashe masu ci gaba da masu tasowa da za su halarci taron wajen daukar matakai kan ceton kasuwa, kuma ana sa muhimmanci sosai kan gyare-gyaren tsarin kudi na kasa da kasa da za a tattauna a kai a gun taron. Kuma a matsayinta na wata kasa mai tasowa mafi girma a duniya, an nuna kulawa sosai kan matsayin kasar Sin a gun taron.

Kafin wannan, He Yafei, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya yi wa wakilinmu bayani kan matsayin bangaren Sin a gun taron. Kuma ya ce,

"Za mu mai da hankali kan halin da kasashe masu tasowa musamman ma kasashe masu fama da talauci ke ciki. Haka kuma za mu jaddada cewa, ya kamata bangarori daban daban su sauke nauyin da ke bisa wuyansu. Alal misali, ya kamata muhimman kasashe masu ci gaba su yi la'akari da tasirin da za su bayar ga tattalin arzikin duniya da kuma sauran kasashe musamman ma kasashe masu tasowa lokacin da suke aiwatar da manufofinsu na tattalin arziki bisa manyan fannoni."

Ban da wannan kuma Mr. He ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su tsara aikin gyara tsarin kudi na kasa da kasa bisa budaddiyar zuciya da kuma hangen nesa. Kuma ya ce,

"bangaren Sin yana fatan za a iya yin kwaskwarima ga tsarin kudi na kasa da kasa daga dukkan fannoni ta yin shawarwari sosai, kuma a karshe dai za a iya kafa wani tsarin kudi na duniya mai adalci da oda, wanda ake bukatar kokarin bangarori daban daban a tsanake."

Bugu da kari kuma, daga ran 22 zuwa ran 23 ga wata, za a kira kwarya-kwaryar taron koli a karo na 16 na kungiyar APEC a kasar Peru. Mr. He ya bayyana cewa,

"A gun wannan kwarya-kwaryar taron koli, shugaba Hu Jintao zai bayyana ra'ayoyin kasar Sin kan halin tattalin arziki da hada-hadar kudi da duniya ke ciki da kuma ingancin abinci da makamashi da dai sauran muhimman batutuwan da za a tattauna a kai, da kuma gabatar da shawara kan kara inganta hadin gwiwar kungiyar APEC a fannoni daban daban. Ban da wannan kuma a gun taron tattaunawa tsakanin shugabanni da wakilan kwamitin ba da shawara kan kasuwanni na APEC, shugaba Hu da sassan kasuwanni za su yi musanyar ra'ayoyi kan tattalin arziki da kudi da ake nuna kulawa sosai a kai."(Kande Gao)