Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-14 14:30:16    
Wu Bangguo ya ziyarci masu aikin sa kai a Seychelles

cri

Masu sauraro, ko kuna sane da cewa, ran 13 ga wata a birnin Victoria, hedkwatar kasar Seychelles, shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo, wanda ke ziyarar sada zumunci a Seychelles, ya ziyarci masu aikin sa kai na kasar Sin a kasar, inda ya sheda musu cewa, kamata ya yi su kula da lafiyar kansu da kuma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin samun babban yabo ga kasar Sin.

A wannan rana da safe, masu aikin sa kai na kasar Sin a Seychelles su 12 sun rera waka mai suna "Wakar masu aikin sa kai" domin maraba da zuwan Mr Wu, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda suka rera cewa,

Masu aikin sa kai sun rera cewa, hannu cikin hannu, zuciya da zuciya, muna dangi ne. Ka zo daga nan, na zo daga can, mun yi taro a wuri daya. Masu aikin sa kai sun bayyana fatansu na kara fahimtar juna tsakanin jama'ar Sin da Seychelles da kara sada zumunta tsakanin kasashen biyu. Mr Wu ya yi farin cikin ganin haka, ya ce,

"Ina jin farin ciki domin saduwa da ku a yau. Dazun nan na saurari rahotonku, ya faranta mai rai sosai, kuma ina jin alfahari gare ku. Yau na ziyarce ku a madadin jama'ar kasar Sin, kuma na gode muku da ayyukan da kuka gabatar domin tabbatar da manufar da kwamitin tsakiyar kasar Sin ke aiwatar ga nahiyar Afirka. Aikinku ya yi kyau sosai."

Kungiyar masu aikin sa kai ta kunshi membobinta 12, kuma dukkansu sun fito daga lardin Guangdong, ciki da akwai likita da nas da malami da mai horar motsa jiki da sauransu, shekarunsu sun kama daga 21 zuwa 42. Kuma za su yi aiki a Seychelles har tsawon shekara daya. Ko da yake masu aikin sa kai sun fito daga sana'o'i daban daban, amma sun sami karbuwa da babban yabo daga wajen jama'ar kasar Seychelles domin ayyukan da suka yi. Shugaban masu aikin sa kai Duan Xi ya gabatar wa Mr Wu cewa, a cikin watan Yuli na shekarar da muke ciki, ma'aikatar motsa jiki da ta al'adu da ta tarbiyya ta Seychelles sun gudanar da wani babban aikin musamman domin nuna godiya ga masu aikin sa kai da masu ba da agaji na kasar Sin. Hukumomin Seychelles sun bayyana fatansu na tsawaita wa'adin masu aikin sa kai da shekara guda.

Mr Wu ya nuna gamsuwa sosai bayan saurarar bayanin da Duan Xi ya yi. Yana tsammani cewa, ayyukan masu aikin sa kai suna muhimmanci sosai, kuma sun sami babban yabo ga jama'ar kasar Sin.

Game da wadannan masu aikin sa kai a nahiyar Afirka, Mr Wu ya bayyana cewa,

"Kuna isar da kulawar jama'ar Sin biliyan 1.3 ga jama'ar Afirka. Yanzu muna sanya ran kafa wata duniya cikin yanayi mai kyau, kamata ya yi kasar Sin ta ba da gudummowar kanta, wadda ta kunshi ayyukan masu aikin sa kai.

Zuwan Mr Wu ya faranta zuciyar masu aikin sa kai sosai, sun bayyana cewa, za su kara kokari da kuma ba da gudummowa domin zurfafa zumunci tsakanin Sin da Seychelles da inganta hadin gwiwa tsakaninsu. (Fatima)