An bude wani wurin musamman domin mutanen da ba su yi aure ba tukuna. Bisa labarin da aka buga a cikin wata jarida da aka buga a birnin Guangzhou ko wace rana,an ce an bude wani wurin musamman domin wadanda ba su yi aure ba tukuna a garin Shunde kusa da birnin Foshan na lardin Guangdong a ranar jumma'a da ta gabata, shi ya sa aka kira wannan ranar biki ga wadanda ba su yi aure ba tukuna. Wanda ya bude wannan wurin musamman tare da nufin taimakon mutanen da suka kai balagai ba su yi aure ba wajen samun aure. Wurin nan ya shimfidu ne a wani yanki mai kyakkyawan gani a lardin nan, an samar da dakunan musamman ga wadanda suka nemi aure. A cikin dakunan dake ciki wurin an samar da bayanai na mutanen da suke neman aure ciki har da hoto, suna,jinsin mutum, yawan shekaru,kamfanin da yake aiki a ciki,matsayin aure, albashi da sha'awarsa da tarihinsa na karatu. Ana iya tanadin bayanai na tsawon shekara daya, idan ya kasa samun masoyiyyarsa, zai iya ci gaba da samar da bayananasa in yana so. Haka kuma ga duk wanda ya na so ya tsawaita lokacin bajen bayanansa. Ban da wannan kuma an shirya tarurruka da wasanni ta yadda za a kawo dama ga wadanda ba su yi aure ba da su samu masoyinsu.
An zambaci wata mata dake neman mummunan miji. Kwanan baya an zambaci wata mata da kudin Sin Renminbi Yuan dubu 13 a birnin Haikou na lardin Hainan yayin da take neman mummunan miji. Bisa labarin da aka samu, an ce matar tana da shekaru 41 da haihuwa, a ganinta mummunan namiji amintaccen mutum ne bayan da mijinta ya rabu da ita yan shekarun baya. Mr Wang mutumin ne da ya zambaci matar yana da shekaru 50 da haihuwa, ya sadu da matar ne ta wata kungiyar daure aure. Mutumin nan ya ce ya zo ne daga lardin Hunan dake tsakiyar kasr Sin,ba shi da kyaun ganin gaske, ya biya bukatun matar sosai. Matar ta kasa saduwa da shi sau da dama ta kuma samu labari cewa wannan mutum mazambaci ne zalla ya zambace ta da kudi mai yawa ta hanyoyi daban daban, daga baya ya bace.
An gano wani katon macijin da ya mutu a matarin ruwa. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar kudu ta gabas ta kasar Sin a makon da ya shige, an ce an gano wani katon macijin da ya mutu a matarin ruwa na Mawei na lardin Fujian a ranar jumma'a da ta gabata. An ce tsawon macijin ya kai mita 4 da digo sha takwas,nauyinsa ya kai kilo 75,fadinsa ya kai centimetre 27, mataccen maciji ya jawo hankulan kauye na kusa, da yawa sun zo wurin su duba gawar majici har ma wasu sun dauka hoto tare da shi. Duk da haka bayan da 'yan sanda suka samu labarin, sai sun gaggauta sun sauka wurin sun binne gawar maciji sabada an ce mataccen maciji na iya baza kwayoyin cuta.
|