Tun daga ran 4 ga wata da aka sanar da lashe zaben da Barack Obama ya yi na shugaban kasar Amurka, mutanen Afrika suka mai da hankali sosai ga wannan batun, amma sun mai da martani daban daban ga wannan bakin mutumin Amurka wanda asalinsa 'dan Afrika. Galibi dai, mazanan siyasa na Afrika sun sanya fatansu matuka ga Barack Obama, suna fatan zai kara kyautata huldar tsakanin kasar Amurka da kasashen Afrika don neman karin agaji ga kasashen Afrika. Amma masana da manazarta da yawa suna ganin cewa, ba a iya tabbatar da cewa Barack Obama zai kawo wa Afrika moriya bayan ya hau kan kujerar shugaban kasar Amurka ba.
Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya taya murna ga Barack Obama da farko, yana ganin cewa, Mr. Oabama ya lashe zabe nasarar kasar Kenya ce, domin asalin Obama yana a can.
Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela dake da shekaru 90 da haihuwa shi ma ya aika wa Barack Obama sakon taya murna, kuma ya nuna fatansa cewa, Mr. Obama zai kawo wa nahiyar Afrika babbar bunkasuwa. Shugaba mai ci na kasar Afrika ta kudu Kgalema Motlanthe ya bayyana cewa, yana fatan za a kara samun sakamako mai kyau wajen hadin gwiwarsu a cikin wa'adin Barack Obama.
Tun daga shekarar 2002, kasar Amurka ta garkama wa kasar Zimbabwe takunkumi a fannin tattalin arziki na shekaru 6 bisa dalilin rashin daidaituwa a zaben shugaban kasar Zimbabwe, wanda ya sa tabarbarewar tattalin arziki mai tsanani a kasar Zimbabwe, amma a lokacin da Barack Obama ya ci zaben shugaban kasar Amurka, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya gabatar da jawabi a rubuce don taya shi murna. Inda ya ce, kasar Zimbabwe tana son ta yi kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu.
Hakazalika, shugabannin kasashen Nijeriya da Mali da Kongo Brazzaville da Mauritius da kuma Chadi da dai sauransu su ma sun bayar da jawabi don taya murna ga Barack Obama, kuma suna fatan zai ba da gudummawa ta musamman don kyautata huldar tsakanin kasar Amurka da kasashen Afrika.
A bangare daban, ba kamar yadda 'yan siyasa suka yi, masana da manazarta na Afrika sun dauki hakikanin ra'ayi kan wannan batu. Suna ganin cewa, ko da yake, Mr. Obama yana son ya bunkasa huldar bangarorin biyu, amma tare da abubuwan da bangarori daban daban suka kayyade, ayyukan da ya iya yi ba su yi yawa ba.
Dalilan da suka sa su dauki wannan ra'ayi su ne, Na farko, a matsayin shugaban kasar Aurka, Barack Obama ba zai iya kubutar da tsarin Amurka da aka yi da sauki ba, aikinsa dake gaba da kome shi ne kiyaye moriyar kasar Amurka. Alal misali, a kan aikin daidaita rikicin kasar Kongo Kinshasa da halin kaka-nika-yi na siyasa na kasar Zimbabwe, ana nuna damuwa cewa, Barack Obama ba zai iya gabatar da hanyar daidaita batu da mutanen Afrika za su gamsu da ita ba. Galibinsu suna ganin cewa, Barack Obama ya rasa sanin gudanar da aikin diplomasiyya, kuma a bangare daban, a matsayin shugaban kasar Amurka, Mr. Obama zai mai da moriyar kasar Amurka a gaban kome.
Na biyu, masana da manazarta na Afrika ba su dauki ra'ayin faranta rai ga aikin daidaita batun ofishin hafsan-hafsoshin sojojin Amurka dake Afrika ba. Galibin kasashen Afrika sun taba kasancewa karkashin jagorancin mulkin mallaka na kasashen yamma a cikin shekaru darurruwa, shi ya sa, mutane da gwamnatocin Afrika ba su amince da sojojin kasashen waje ba. Sabo da haka, ya zuwa yanzu, aikin kafa ofishin hafsan-hafsoshin sojojin kasar Amurka da shugaba Bush ya gabatar bai samu cigaba ba.
Na uku, sabo da tasirin da rikicin kudi ya kawo wa kasar Amurka, karfinta na ba da agaji ga kasashen waje ya ragu, haka kuma, shugaba Bush ya kara ba da agaji ga kasashen Afrika a shekaru 2 na karshen wa'adin aikinsa. Shi ya sa, manufofi masu gatanci da Barak Obama ya iya dauka a fannin tattalin arziki ba su yi yawa ba.(Lami)
|