Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-11 09:40:30    
Irina yarinya daga Rasha mai son wasan karate na kasar Sin

cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, a birnin Shiyan na lardin Hubei dake kudancin kasar Sin, an yi zama na 3 na bikin nuna wasan karate na gargajiya na duniya. A gun bikin, 'yan wasa kusan dubu biyu da suka zo daga kasashe da shiyyoyi sama da 60 na duk duniya sun yi taro kuma sun yi hira domin yin musanyar ra'ayoyi kan wasan karate. Wadannan 'yan wasa wadanda ke da launukan fata da harsuna daban daban sun zo wuri daya daga wurare daban daban na duk duniya musamman domin neman samun mafarki daya na wasan karate dake cikin zukatansu. Daga wajensu, ana iya ganin kishin wasan karate na gargajiyar kasar Sin, kuma ana iya tarar da cewa, wasan karate wanda ke nuna mana al'adun kasar Sin sosai da sosai yana canjawa zaman rayuwar jama'ar kasar Sin, har ma yana canjawa zaman rayuwar jama'ar kasashen duniya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wata yarinya da ta zo kasar Sin daga kasar Rasha, sunanta shi ne Tolstopyatova Irina, wannan yarinya ta sa niyyar yalwata wasan karate na gargajiyar kasar Sin a duk duniya.

Irina tana da shekaru 20 da haihuwa kawai yanzu, amma ta riga ta yi atisayen wasan karate na gargajiyar kasar Sin da shekaru biyar. A kullum tana fatan za a kafa manyan makarantun koyar da wasan karate na gargajiyar kasar Sin a wurare daban daban na duk duniya don yalwata wasan karate. Domin wannan, Irina ta zo kasar Sin daga garinta kafin shekaru biyu, yanzu tana karatu a birnin Beijing.

Irina tana da kwarewar wasan motsa jiki, kuma ta taba koyon wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe da raye-raye tun take yarinya karama. Amma ta daina saboda ba ta son irin wadannan wasanni. Daga baya kuma ta fara koyon wasan karate, ta dauka cewa, wasan karate wasa ne da ya fi ban sha'awa, tana kaunar wasan karate kwarai da gaske, kuma ta yi iyakacin kokarin koyon wasan karate.

Kafin ta zo kasar Sin, Irina ta koyi wasan karate bayan karatun makatanra, wato kowace rana ta fara koyon wasan karate daga karfe biyar na yamma har zuwa karfe tara ko goma na dare. Kodayake ta gaji sosai, amma ba ta daina ba saboda tana kaunar wasan karate kwarai kuma tana jin dadi. Irina ta gaya mana da sinanci cewa,  "Idan kana son wasan, sai ba gajiya."

Yayin da ake koyon wasan katare, ana iya tarar da cewa, lallai wasan karate ba shi da wuya, amma fasaha mai rushe ta wasan ta fi wuya, alal misali salon 'tsaya' da salon 'tsuguna' wato 'mabu'. Lokacin da Irina ta fara koyon wasan karate, ba ta iya salon tsugunar 'mabu' yadda ya kamata ba, sai mai horaswar wasan ya koyar mata sau tarin yawa. Irina ta ce, "Dole ne a nuna tsugunar 'mabu' mai kyan gani, kuma dole ne a nuna tsugunar 'mabu' mai karfi, wato a kalla a yi tsuguna ba tare da motsi ba cikin mintoci biyar. Amma na nuna salo mai muni, sai mai horaswa ya ce, 'me ya sa ba ki nuna mana salo mai kyan gani? Sai ki kara kokari.' Sai na kara kokari na samu ci gaba."

Domin kyautata salonta na tsugunar 'mabu', Irina ta kashe lokaci da yawa har ya kai shekaru uku. A cikin wadannan shekaru uku, Irina ta kara fahimta da cewa, tsawon lokaci yana da muhimmanci sosai ga masu atisayen wasan karate, kuma ta kara gane cewar ba mai iyuwa ba ne ga kowanen mutum da ya sarrafa fasahar wasan karate na gargajiyar kasar Sin cikin gareren lokaci. A kasar Rasha, abokan Irina da yawa su kan koyar da masu sha'awar wasan karate a cikin makaranta bayan da suka gama aiki, amma dukkansu ba su taba koyar da wasan damben gargajiyar kasar Sin wato 'taiji' ba, dalilin da ya sa haka shi ne domin wasan 'taiji' bai dace da yara ba. Irina tana ganin cewa,  "Tsoffi sun fi dace da wasan damben gargajiyar kasar Sin wato 'taiji', saboda sun fi gane tunanin zaman rayuwa kuma sun fi gane me suke bukata, idan yara kanana sun koyi wasan 'taiji', to, za su gamu da wahala saboda ba su gane ba."

Bayan Irina ta sauka a kasar Sin, ba ta ji sinanci ba, shi ya sa dole ne ta kashe awa takwas ko tara wajen koyon sinanci a kowace rana, ban da wannan kuma, dole ne ta yi karatu a jami'a, saboda haka, ba ta da isashen lokacin koyon wasan karate, amma Irina ba ta so ta daina koyon wasan karate, sai ta yi tunani, daga baya kuma ta tsai da cewa, za ta yi atisayen wasan karate da rabin awa bayan da ta koyi sinanci da awa biyu. Daga nan, matsayin sinanci na Irina ya dada daguwa, matsayinta na wasan karate shi ma ya dada daguwa a kwana a tashi.

Yanzu, kowace rana, Irina tana jin dadin zaman rayuwa, wato kowace rana ta kan je karatu a jami'a, bayan karatu kuma, ta kan yi atisayen wasan karate tare da mai horaswarta, a karshen mako kuwa, Irina ta kan je klub din wasan karate da mai horaswarta ke aiki domin koyar da dalibai wasan karate tare da mai horaswarta. Ban da wasan karate na gargajiyar kasar Sin, Irina ita ma tana sha'awar dafa abinci. A garinta dake Rasha, wato kafin Irina ta zo kasar Sin, ta taba dafa abinci a cikin dakin cin abinci na otel na babanta, ba ma kawai Irina tana iya dafa abinci sosai ba, har ma tana kaunar fasahar dafa abinci. Ta gaya mana cewa, tana iya dafa dukkan ire-iren abinci na Rasha. Amma yanzu, tana shan karatu kuma tana shan aiki, shi ya sa ba ta da isashen lokacin dafa abinci, amma Irina ta ce, "Ina kaunar dafa abinci, kuma ina kaunar nazarin sabon salon dafa abinci, zan yi kokari, ko shakka babu, zan sami lokaci."

Game da dafa abinci, Irina tana ganin cewa, irin wannan aiki wato dafa abinci zai ba da amfani ga wasan karate. To, ko mene ne dalilin da ya sa ta fadi haka? Game da wannan, Irina ta gaya mana cewa, "Lokacin da na dafa abinci, na kan shiga shafin da abin ya shafar dafa abinci kan internet, daga baya kuma, zan yi nazari kansu, sa'an nan kuma zan dafa abinci iri daban daban bisa hanyoyi daban daban, a karshe dai, zan zabi daya daga cikinsu, wato zan zabi daya wanda ya fi dadin ci, zan dafa irin wannan abinci ga abokana domin su dandana, idan sun ji dadin cin abincin da na dafa, to, zan ji dadi kamar yadda suke. Bayan wannan kuma, na kan yi tunani cewa, idan na yi nazari kan wasan karate kamar yadda nake yin nazari kan fasahar dafa abinci, wato na yi nazari sosai da sosai kan wasan karate bisa mataki daban daban, to, fasahar wasan karate za ta samu kyautatuwa, matsayina na wasan karate na gargajiyar kasar Sin shi ma zai dada daguwa a kai a kai, a karshe dai, zan ba da amfanina wajen yalwata wasan karate a duk duniya."

Domin tabbatar da mafarkinta wato Irina tana fatan za ta kafa manyan makarantun koyar da wasan karate na gargajiyar kasar Sin a wurare daban daban na duk duniya, ta yadda za a yalwata wasan karate na gargajiyar kasar Sin, Irina tana sanya matukar kokari, muna fatan za ta cimma burinta tun da wur wuri, mu ma muna fatan wasan karate na gargajiyar kasar Sin zai sami yalwatuwa lami lafiya kuma cikin sauri a duk fadin duniya. (Jamila Zhou)