Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-10 15:22:03    
Mahalarta taron Davos sun yaba wa tattalin arzikin kasar Sin

cri
A gun taron tattaunawa na Davos na lokacin zafi na shekara ta 2008 da aka rufe kwanan nan, matsalar ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya sannu a hankali sakamakon rikicin ba da lamunin gidaje na kasar Amurka ta zama daya daga cikin batutuwan da ke jawo hankalin jami'ai da masu tafiyar da tattalin arziki da masanan tattalin arziki na kasar Sin da na kasashen waje. Sun bayyana cewa, ko da yake ya kasance da hadari sosai wajen gudanar da tattalin arziki a sakamakon rikicin kudi na duniya, amma har yanzu sun yaba wa tattalin arzikin kasar Sin. Sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, za mu karanto muku wani bayani kan yadda suka samu wannan ra'ayi.

A cikin wasu watannin da suka gabata, tattalin arzikin muhimman yankunan duniya ya hadu da tafiyar hawainiya. A bayyane yake, wannan yana ta kawo illa ga tattalin arzikin duk duniya. Ko shakka babu, kasar Sin wadda ke hada tattalin arzikinta da sauran kasashen duniya a kai a kai ba ta iya tsirar da kanta ita kadai. Yawan kayayyakin da muhimman kasashe da yankuna suke saye daga kasar Sin ya ragu, a waje daya kuma, yawan jarin da kasar Sin take zubawa a cikin gida ya ragu. Tabbas ne irin wadannan abubuwa za su sanya a rage samun saurin cigaban tattalin arziki. Dattijo Cheng Siwei, wani masanin tattalin arziki, kuma tsohon mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin ya yi hasashen cewa, saurin cigaban tattalin arzikin kasar Sin zai ragu da kimanin kashi 10 cikin kashi dari a shekarar da muke ciki. Dattijo Cheng ya ce, "Ko shakka babu, yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasuwannin kasashen waje zai ragu sabo da yadda saurin cigaban tattalin arzikin duniya ke raguwa sakamakon rikicin kudi. Yawan rarar kudaden cinikin waje da muke samu ma zai ragu. Yanzu ana samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ta hanyar zuba jari da raya kasuwannin gida da neman rarar kudaden cinikin waje. A shekarar da muke ciki, muna kuma aiwatar da manufar manufar tsuke bakin aljihu game da harkokin kudi, an rage yawan jarin da ake zubawa, kasuwannin gida sun samu cigaba kadan, amma a waje daya, yawan rarar kadaden cinikin waje da kasar Sin ta samu ya ragu. Sakamakon haka, saurin cigaban tattalin arzikinmu zai ragu. A ganina, raguwa za ta kai kimanin kashi 10 cikin kashi dari a shekarar da muke ciki."

Amma, kasar Sin ba ta bukatar nuna damuwa sosai kan raguwar saurin cigaban tattalin arziki. A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin tana kokarin canza hanyar neman cigaban tattalin arziki da kayyade saurin karuwar tattalin arziki fiye da kima da kuma sassauta raguwar darajar kudi. Don saurin cigaban tattalin arziki ya ragu kadan ba mummunan abu ba ne. Mr. Liu Mingkang, shugaban kwamitin sa ido kan bankunan kasar Sin ya amince da wannan ra'ayi. Mr. Liu ya ce, "A ganina, wannan wani kyakkyawan abu ne ga kasar Sin. Yanzu kasar Sin tana bukatar inganci, amma ba sauri ba wajen neman cigaban tattalin arzikinta."

Masanan ilmin tattalin arziki wadanda suka halarci taron tattaunawa na Davos na lokacin zafi na shekara ta 2008 sun nuna cewa, lokacin da aka samu ragin saurin cigaban tattalin arziki, kasar Sin za ta iya magance hadarin tattalin arziki ta hanyar nuna wa masana'antunta goyon baya wajen kirkiro sabbin fasahohi da samar da kayayyakin da ke kunshe da fasahohin zamani da kansu domin karuwar darajar kayayyakinsu. A waje daya kuma kasar Sin za ta iya canja tsarin kayayyakin da take fitarwa da kuma kara raya kasuwannin gida da sai kaimi ga masana'antu da su zuba jari a kasashen waje. Mr. Jiang Jianqing, shugaban bankin masana'antu da kasuwanci na kasar Sin ya ce, yana sa rai kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Mr. Jiang ya ce, "Idan an kwatanta kasuwannin kasashen da ke makwabtaka da kasar Sin, ina tsammani, karfi da kuma manufar kayyade raguwar darajar kudi da kasar Sin ke aiwatar da su suna aiki kamar yadda ya kamata. A ganina, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun karuwa cikin hali mai kyau, kuma za ta iya kayyade raguwar darajar kudi a cikin halin da ya dace."

A waje daya, a ganin Schwab, shugaban taron tattauna tattalin arzikin duniya yana ganin cewa, a cikin 'yan shekaru masu zuwa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun karuwa sosai. Mr. Schwab ya ce, "Ko da yake yanzu saurin karuwar tattalin arzikin duniya yana ta raguwa, amma kasar Sin na daya daga cikin yankunan da suka fi samun saurin karuwar tattalin arzikinsu."

Sabo da ana da imani sosai ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin, wasu manyan masana'antu da kamfanoni na kasashen duniya suna sha'awar kasuwar kasar Sin sosai. Lokacin da aka samu jan kafa game da karuwar tattalin arzikin duniya, suna fatan za su iya samun moriya a kasuwar kasar Sin. Mr. Tom Enders, jami'in farko na kamfanin Airbus na Turai ya bayyana cewa, wani muhimmin shirin da kamfanin Airbus zai aiwatar shi ne kara yin hadin guiwa da masana'antun jiragen sama na kasar Sin. Mr. Tom Enders ya ce, "Muna fatan za mu iya kara yin hadin guiwa a kasar Sin sabo da wannan wata babbar kasuwa ce. A cikin shekaru 20 ko 30 masu zuwa, kasuwar kasar Sin tana da muhimmanci kamar kasuwanninmu a kasar Amurka da Turai. Sabo da haka, ina tsammani, za mu iya cimma burinmu na raya kasuwar kasar Sin kamar yadda muke raya kasuwarmu a kasar Amurka. Za mu iya samun maki mai kyau sabo da mun riga mun soma kara yin hadin guiwa da kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin. Shi ne wani muhimmin shirin da za mu aiwatar a nan gaba."

Ba ma kawai an mai da hankali kan makomar tattalin arzikin kasar Sin ba a gun taron tattaunawa na Davos a lokacin zafi na shekara ta 2008, har ma yadda rikicin ba da rancen kudin sayen gidaje na kasar Amurka yake yin tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin ya zama wani batun da ke tsone idon mahalarta taron. Game da wannan batu, Mr. Cheng Siwei, wani masanin tattalin arziki na kasar Sin ya bayyana cewa, sabo da hukumomin kudi na kasar Sin sun taka tsantsan sosai wajen zuba jari a kasashen waje, rugujewar manyan hukumomin kudi na kasar Amurka ba za ta kawo babbar hasara ga hukumomin kudi na kasar Sin ba. Mr. Cheng ya ce, "Yawan takardun ba da lamunin sayen gidaje da kasar Sin ta saya daga hukumomin kudi na Amurka, ciki har da kamfanin Lehman Brothers ya yi kadan, wato adadi na 'yan miliyoyin daruruwan dalar Amurka kawai ne. Sabo da haka, mai yiyuwa ne ba zai yi mummunan tasiri sosai ga tattalin arzikin kasar Sin ba."

Haka kuma, Mr. Liu Mingkang, shugaban sa ido kan bankunan kasar Sin ya bayyana cewa, sabo da hukumomin sa ido kan bankunan kasar Sin sun kayyade hukumomin kudi na kasar Sin da su sayi takardun ba da lamunin sayen gidaje na kasar Amurka, lokacin da aka gano ana samar da rancen kudin sayen gidaje cikin sauri fiye da kima a shekara ta 2006, nan da nan ne kwamitin sa ido kan bankunan kasar Sin ya aiwatar da sabuwar manufa game da rancen kudin da ake samarwa domin sayen gidaje. Alal misali, idan ana son samun rancen kudi daga banki domin sayen wani gida na biyu, dole ne mutum ya biya kudin da yawansa ya kai kashi 40 cikin kashi dari bisa na jimlar kudin wannan gida lokacin da ake sa hannu kan kwangilar sayen gida. Amma a da, an biya kudin da yawansa ya kai kashi 20 cikin kashi dari ne kawai bisa jimlar kudin wani gida. Sakamakon haka, an yi rigakafin aukuwar hadarin kudi a nan kasar Sin. Irin wadannan manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa za su iya tabbatar da cewa, rikicin ba da rancen kudin sayen gidaje da ya auku a kasar Amurka ba zai auku a kasar Sin ba. (Sanusi Chen)