Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-10 15:11:43    
An yi taron shugabannin shiyyar manyan tabkuna don daidaita matsalar Kongo Kinshasa

cri

Cikin shirin yau, bari mu mai da hankali kan wani taro dangane da batun Kongo Kinshasa da aka kammala shi a Nairobi, hedikwatar kasar Kenya a ran 7 ga watan Nuwamba,inda shugabannin kasashen shiyyar manyan tabkuna sun yi kira ga bangarorin kasar Kongo Kinshasa da su tsagaita bude wuta. Haka kuma, an ce, za a kafa wata kungiyar daidaitowa don neman bakin zaren warware rikicin kasar.

Ya kama daga karshen watan Augusta, Laurent Nkunda, madugun 'yan tawayen kasar Kongo Kinshasa da sojojinsa sun kai farmaki ga sojojin gwamnatin kasar da ke lardin Noth Kivu, sun mamaye garuruwa daya bayan daya. Zuwa yanzu, a kalla dai 'yan kasar kimanin dubu 250 suka bar gidajensu suna gudun hijira sakamakon barazanar wutar yaki. Bisa mawuyacin halin da ake ciki ne, an kira taron shugabannin shiyyar manyan tabkuna, inda mahalartar taron suka hada da shugabannin kasashen Kongo Kinshasa da Ruwanda, da Uganda, da Tanzania, da Kenya, da dai sauran kasashen shiyyar manyan tabkuna, da sakataren janar MDD, da manyan jigogin kungiyar tarayyar Afirka ta AU. Cikin sanarwar da aka bayar bayan taron, bangarorin masu halartar taron sun sa kaimi ga masu makamai da ke lardin North Kivu na gabashin kasar Kongo Kinshasa da su tsagaita bude wuta nan da nan. Har wa yau kuma, masu halartar taron sun samu ra'ayi daya kan cewar, kamata ya yi, an shimfida aiwatar da aikin jin kai a wurin da ake fama da juna, ta yadda za a sasanta rikicin wurin.

Ban da wannan kuma, an yi kira ga MDD da ta kara danka wa tawagarta dake kasar Kongo Kinshasa ta MONUC iko, kuma ta kara rufa mata baya da samar da karfin mutum da kayayyaki. Haka kuma, an bukaci bangarorin da abin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar da aka sa hannu a kai, don tabbatar da samun kwanciyar hankali mai dorewa a shiyyar.

Manazarta na ganin cewa, abubuwan da ake cikin sanarwar da aka bayar su ne abun da aka fi mai da hankali a kai cikin taron, kuma su ne batutuwan da zarafi ya kama don daidaita matsalar Kongo Kinshasa.

Da farko, arangamar ta tiga ta haddasa bala'in jin kai mai tsamari, shi ya sa, abin da aka fi mai da hankali a kai yanzu shi ne samun tsagaita bude wuta. Mista Ban Ki-moon, sakataren janar MDD ya yi hasashe a wajen taron, inda ya ce aiki na farko shi ne an dauki matakai don shawo kan hargitsin da ke kara tsamari da aka samu a gabashin kasar Kongo Kinshasa. Yayin da Jakaya Kikwete, shugaban kasar Tanzania, kuma shugaban kungiyar AU na wannan karo, ya nuna ra'ayi daya kan cewar, abin da ake bukatar an yi da farko shi ne kawo karshen halin da ake ciki na nukura da juna a kasar Kongo Kinshasa.

A baya ga haka kuma, lokacin da ake kokarin neman samu tsagaita bude wuta a Kongo Kinshasa, kada a yi jinkiri wajen aiwatar da aikin jin kai don ceton mutanen wurin. Cikin sanarwar da aka bayar, shugabannin kasashen daban sun bukaci cewa, a shimfida tsarin da ake bi don aiwatar da aikin jin kai, ta yadda za a gudanar da aikin cikin sauri ba tare da gamu da shinge ba.

Na uku, kamata ya yi, a dauki mataki don aiwatar da yarjejeniyar da aka sa hannu a kai. A ran 23 ga watan Janairu na shekarar bana, gwamnatin kasar Kongo Kinshasa da 'yan tawaye sun sa hannu kan yarjejeniyar Goma, inda suka kuduri niyyar tsagaita bude wuta, da daina yin adawa da juna. Amma, duka da haka, 'yan tawayen kasar sun yi fatali da yarjejeniyar, sun fara kai farmaki ga sojojin gwamnatin a karshen watan Augusta na bana. Har zuwa yanzu ba a daina yake-yake sosai ba.

Na hudu, kamata ya yi, a kara danka wa tawagar MDD ta MONUC iko. Yanzu ana samu sojojin MDD masu wanzar da zaman lafiya dubu 17 a Kongo Kinshasa. Shugabannin kasahe daban na bukatar MDD da ta kara mika wa tawagar iko, ta yadda ba ta tsaya kan kiyaye kwanciyar hankali ba, har ma ta soma aikinta na kokarin neman wanzar da zaman lafiya a wurin.(Bello Wang)