A ran 7 ga wata, bi da bi ne, shugaban kasar Gabon Mr. Hadj Omar Bongo, da shugaban majalisar jama'ar kasar Mr. Guy Nzouba Ndama, da kuma shugaban majalisar dattawa ta kasar Mr. Rene Radembino Coniquet suka yi shawarwari da ganawa da shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo.
A ganawar Bongo da Wu Bangguo, Mr. Bongo ya ce, kasar Gabon tana mai da hankali sosai kan raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin, tana sanya ran ganin kara hada kai irin na moriyar juna da kasar Sin a fannoni daban daban, ta yadda za a iya sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu.
Mr. Wu Bangguo ya isar da kyakkyawar gaisuwa da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi wa Mr. Bongo. Mr. Wu ya ce, kasar Sin tana son kara fahimtar juna da sada zumunta ga juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kuma inganta hada kansu a fannoni daban daban, da kuma samun daidaici da kasar Gabon kan manyan lamuran duniya da na shiyya shiyya.
A ganawar Mr. Ndama da Wu Bangguo, Mr. Wu ya ce, kasar Sin tana son ci gaba da ingiza hadin kai da ke tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni, ta yadda za a iya samar da rayayyen karfi ga dangantakar abokantaka da hadin kai da ke tsakanin kasashen biyu.
A ganawar Mr. Coniquet da Wu Bangguo, Mr. Wu ya ce, Sin da Gabon dukkansu kasashe ne masu tasowa, suna da ra'ayi daya a manyan lamuran duniya da na shiyya shiyya, haka kuma su kan samu daidaici da juna, sun taka wata muhimmiyar rawa wajen kiyaye da kare iko da moriya ta kasashe masu tasowa.(Danladi)
|