Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-07 15:43:47    
Wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa

cri

Masu karatu, in kuna sha'awar yin wasa da ruwa a cikin ruwa mai tsabta, to, wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa da ke gundumar Shunyi ta birnin Beijing wuri ne mafi dacewa a gare ku.

Wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa, wani filin wasa ne da za a yi shirye-shiryen tseren kwale-kwale da tseren kanan kwale-kwale da wasan ninkaya na gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma shirin tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic ta Beijing ta nakasassu a watan Agusta na shekarar da muke ciki. Za a fito da lambobin zinariya 32 a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 a nan, wadanda yawansu ya kai misalin kashi daya cikin kashi goma bisa jimlar lambobin zinariya da za a samu a gun gasar. Shi ya sa a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa zai zama na uku da za a fi samun yawan lambobin zinariya a nan, ban da cibiyar wasanni ta kasar Sin da kuma cibiyar wasan ninkaya ta kasar Sin. Wannan wurin yawon shakatawa a kan ruwa yana cikin gundumar Shunyi na arewacin birnin Beijing. A kan bukaci misalin rabin awa domin zuwa wannan wurin yawon shakatawa daga cibiyar birnin Beijing cikin mota.


1 2