Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 16:28:41    
Wani bayani game da raya sana'o'i da Wang Jie ya yi

cri
A shekaru 24 da suka wuce, Wang Jie, 'dan shekaru 13 a lokacin, wanda ke zaune a wurin da ke kan tudu da ke kudancin jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, ya rasa iyawar ganin abubuwa a sakamakon ciwon idanu, ta yadda ba zai iya cimma fatansa na zama wani matukin jirgi. Amma, yanzu Wang Jie shi wani mutumi ne da ya kafa makarantar koyon sana'o'i ta nakasassu ta farko a jihar Xingxia. A cikin shirinmu na yau kuma, za mu kawo muku wani bayani game da raya sana'o'i da Wang Jie ya yi.

Wang Jie ya karbi ziyarar da muka kai masa ne a cibiyar tausa ta makafi ta Ai De da ya kafa a birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui. A cikin ziyarar, muna iya ganin cewa, cikin sauki ne Wang Jie na iya fuskantar sauye-sauyen da makanta ke kawo masa wajen zaman rayuwarsa.

"A hakika dai, na iya karbar nakasar jikina ne a lokacin da nake karatu a makarantar sakandare ta koyon sana'o'i, inda na gamu da dalibai makafi da yawa. Bayan da na shiga jami'a kuma, sai na iya fuskantar makanta cikin sauki. A 'yan shekarun da suka wuce, na soma yin godiya ga nakasata. A ganina, saboda daidai wannan wahalar da na sha, sai na samu sabon ra'ayi kan zaman rayuwa."

A shekarunsa na haihuwa suka kai 13 kawai, Wang Jie ya samu ciwon idanu, har ma ba zai yi imani kan zaman rayuwarsa ba.

Wang Jie ya ce,

"Duniyata ta canja ba zato ba tsamani bayan da na rasa iyawar ganin abubuwa, na kan yi fushi, kuma ba zan cike da imani kan makoma ba."

Iyalin Wang Jie na fama da talauci, kuma iyayensa sun sha wahaloli sosai kan zaman rayuwarsu. A gani haka, Wang Jie ya yi tunani a zuciyarsa cewa, ba kawai bai taimaka wa iyayensa don kawar da matsaloli ba, har ma ya kara nauyin da ke bisa wuyensu.

Wang Jie ya ce,

"Na samu taimako da kauna sosai daga iyayena, tilas ne na yi kokari kan kula da zaman rayuwata da kaina."

A shekarar 1987, Wang Jie ya shiga wata makarantar koyon sana'o'i ta sakandare da ke jihar Shanxi, don koyon sana'ar tausa. Bayan shekaru uku da suka wuce, ya gama karatunsa bisa maki mai kyau, kuma ya zama wani likita mai aikin tausa a asibiti na garinsa. A lokacin aikinsa, Wang Jie ya gano cewa, fasahohin likitanci da ya samu kadan ne, basu iya biyan bukatu ba, saboda haka, ya tsaida wani kuduri daban, wato a lokacin da yake aiki a asibiti, a waje daya kuma yana share fagen shiga jami'a.

"A lokacin, an zabi dalibai makafi kusan 20 kawai a duk kasar Sin. A wannan shekara kuma na samu nasarar shiga jami'a."

A shekarar 1998, bayan da Wang Jie ya kama karatunsa a jami'a, sai ya je birnin Shenzhen da ke kudancin kasar Sin. Da rana yana neman aikin yi, da dare kuma yana barci a kan titi. Wani 'dan ciniki daga Hongkong yana son fasahar tausa ta Wang Jie, kuma ya gayyace sa da su hada gwiwarsu don kafa wata cibiyar tausa tare a Hongkong. Bayan haka kuma, wannan 'dan ciniki ya yi alkawari cewa, zai ba da hannun jari na kashi 30 cikin dari ga Wang Jie. Amma, Wang Jie ya yi tunani tare da wata-wata cikin dogon lokaci kan wannan gayyatar da aka yi masa. Ya ce,

"Mutane da yawa sun taba taimake ni, saboda haka, ya kamata na yi kokari don taimaka wa makafi da mutane masu fama da talauci da yawa, ta yadda zan iya saka wa zaman al'umma."

Wang Jie ya tsaida kudurin koma garinsa, jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui. Makafi da dama na wurin sun nemi su, kuma suna fata zai ba su damar samun aikin yi. A sakamakon haka, Wang Jie yana son kafa kwasa-kwasan koyon fasahar tausa ta makafi, amma ba ya da iasasshen kudi ba.

"Na gayyaci wasu makafi da sauran makasassu don yin wasanni a gidajen wasan kwaikwayo ko silima, ta yadda za mu samu samu kudi. A ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 1998, wato ranar bikin nakasassu ta duniya, a cikin rana daya kawai mun samu kudin Sin yuan RMB fiye da dubu 10 ta wasannin da muka yi. Haddadiyar kungiyar nakasassu ya gundumarmu ta mayar da wadannan kudi zaman kudin musamman na horar da nakasassu."

A watan Afril na shekarar 1999, kos na farko na horar da fasahar tausa ga makafi a jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ya soma karbar dalibai. A cikin watanni uku na kos din, Wang Jie ya sa makafi da su karfafa fasahar tausa a kan jikinsa.

A watan Yuli na shekarar 2001, a karkashin kokarin da Wang Jie ya yi, da kuma goyon baya da haddadiyar kungiyar nakasassu ya jihar Ningxia, da hukumomin kwadago da jin dadin jama'a na jihar suka yi, an amince da kafa makarantar koyon sana'o'i ta nakasassu ta Ai De ta jihar Ningxia, wato makarantar horar da nakasassu ta musamman daya kawai a jihar.

Yanzu, makarantar koyon sana'o'i ta nakasassu ta Ai De ta roga ta horar da dalibai fiye da 2500, inda sama da kashi 90 cikin dari sun samu takardun shaida na samun aikin ai na kasar Sin, Bayan haka kuma, yawan kananan asibitocin tausa da daliban makarantar suka kafa a karkashin goyon baya daga makarantar sun kai kusan 80. Bugu da kari kuma, sun dalibai da yawa suna aikin tausa a kasashen Japan, da Singapore, da Australian, da dai sauransu.

A karshen ziyarar, Wang Jie ya ce, ya samu kauna daga taimakon da mutanen suka ba shi, wannan kauna ta taimake shi don ya janye jiki daga mawuyancin hali, bayan haka kuma ya yi amfani da kaunar don taimaka wa sauran mutanen da ke shan wahaloli.