Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 16:21:25    
Shugabannin kasar Sin suna samun yabo daga wajen mutane masu amfani da yanar internet

cri

Sanin kowa ne abincin "Shijinbabaofan",abinci ne mai dadin ci kwarai da gaske a kasar Sin, kuma yana daya daga cikin nau'o'in abincin masu dadi da sinawa suke ci a ranakun salla.Amma bayanin da za mu kawo muku a yau ba abincin Shijinbabaofan ba ne,suna ne daban da aka nada wa mutane masu amfani da yanar internet wadanda suke kaunar shugabannin kasar Sin.. Dalili kuwa shi ne a cikin sunan shugaban kasar Sin Hu Jintao da akwai kalmar JIN,a cikin sunan firayim ministan kasar Sin da akwai kalmar BAO da ta hade da Ba,lafazin FAN ya yi daidai da fans na turanci,shi yasa aka kira su mutane masu kaunar shugabannin kasar Sin a yanar internet.

Jama'a masu sauraro,idan ka yi amfani da injin "google",ka rubuta "shijinbabaofan" cikin sinanci,za ka iya samun shafuna sama da dubu dari uku dake da kalmomin din."Shijinbabaofan" ya zama wani muhimmin batun da aka fi yin tattaunawa a kai a yanar internet ta kasar Sin a kwanakin baya. Wadannan mutane sun bude shafinsu na musamman da filin fadi-sonka,sun manna hotunan shugabannin Sin guda biyu a shafinsu na yanar internet,sun kuma bayyana ra'ayinsu.wasunsu kuma sun tsara wata waka domin wannan batun.

Wata rana ta watan Mayu na bana da Mr Ding Yi wanda yake aiki a Zhongguancun,inda kamfanonin injuna masu kwakwalwa suka fi yawa ya gano wani shafin musamman dangane da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao daga Webset Facebook,ya yi farin ciki kwarari da gaske ya ce :"A ganina karo ne na farko da masu amfani da yanar internet suka tsara shafin musamman domin shugabannin kasa da radinsu a kasar Sin.Da farko na yi mamaki da samunsa. Haka kuma a ganina kyakkyawar hanya ce da ake bi."

Ga shi a yau mutane masu kaunar shugabannin kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen kara kwarjinin shugabannin Sin ta hanyar yanar internet. Mutane masu amfani da yanar internet na sauran kasashen duniya su ma sun musanya hotuna da sakonni da ra'ayoyi dangane da shugaban kasar Sin Hu Jintao da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao. Wasun kuma sun shirya kungiyoyin ba da taimako,wasu kuma sun nuna girmamawarsu ga shugabannin kasashensu ta hanyar nan da ake bi a kasar Sin.

A ran 4 ga watan Satumba na bana, Webset na people's daily na kasar Sin ya bude wani filin musamman na fadi son-ka domin mutane masu kaunar shugabannin kasar Sin. Duk wanda yake cikin wadannan mutane ya iya samun takardar shaida mai kaunar shugabannin Sin a yanar internet idan ya rubuta sunansa a yanar internet,kuma ya iya bayyana ra'ayinsa da sakonsa zuwa ga shugabannin Sin Hu Jintao da Wenjiabao da sauran manya.tun daga ranar 4 ga watan Satumban da aka bude wannan shafi,mutane miliyan biyar da dubu goma sun sami takardun shaidu.wannan adadi na karuwa a kwana a tashi,sakonnin da suka aika sun yi yawan gaske.

Bayan da aka bude filin musamman domin masu kaunar shugabannin kasar Sinm,kowace rana da Mr Dinyi ya fara aiki a ofisi,da farko ya karanta labaran da aka bayar a yanar internet,sa'an nan ya shiga wannan shafin musamman da aka bude dominsu,ya karanta sakonnin da sauran masu kaunar shugabanni suka rubuta. Ya ce "Da na samu wannan shafin musamman,da farko na yi mamaki,kuma na yi farin ciki.a ganina wannan hikima ce mai kyau. Nan take na yi rajista,na kuma ga sakonnin da sauran mutane suka aika."

Daga cikin mutane masu kaunar shugabanni a yanar internet,matasa su ne ginshikai wadanda aka haife su bayan shekarun 1980.Malama Fu Mengyao mai shekaru 22 da haihuwa,wata daliba ce a aji na uku na sashen turanci a jami'ar koyon malanta ta babban birni, ta dauka cewa matasa masu dimbin yawa sun shiga wannan filin musamman da aka bude,wannan ya ba da shaida cewa matasa suna kaunar shugabanni biyu na kasar Sin da zukatansu "Dalili kuwa shi ne firayim minista Wen Jiabao,dattijo mai hankali,kuma kamili ne mai nuna kauna ga jama'a,mu matasa muna so mu yi amfani da kalmomi na nuna kauna kai tsaye domin bayyana kaunarmu ga shugabanninmu."

Daliba Wang Ling ta aji na farko wadda take da ra'ayi daya da na Fu Mengyao, a ganinta sharudan zamanta sun fi na kakaninta da iyayenta kyau kwarai da gaske,amma wannan bai kara nisan dake tsakaninsu da shugabannin kasa kamar kakaninsu a zukatansu ba.Da ta takalo batu dangane da shugaban kasa Hu Jintao da firayim minista Wen Jiabao, Wang Ling da sauran 'yan makarantarta dukkansu sun maganta kan girgizar kasar da ta auku a ran 12 ga watan Mayu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin da kuma yadda shugabannin nan biyu suka yi rangadi da kansu a wurin da girgizar kasar ta ritsar da shi. Wang Ling ta ce " Bayan da girgizar kasa ta wakana a gundumar Wenchuan,firayim minista Wen Jiabao ya je wurin domin nuna juyayi ga mutanen da ke fama da bala'in daga indallahi,yayin da ya bayyana ra'ayinsa kan girgizar kasa,hawayensa na zuba,wannan hali ya girgiza kaina.wannan shugaba ya isa a nuna masa kauna."

Ba matasa kawai suke kaunar shugabannin kasar Sin ba hatta ma da tsofaffi.Mr Wen Hongjun,wani babban injiniya mai ritaya dake zama a unguwar Shijinshang dake yammacin birnin Beijing shi ma ya kan shiga shafunan yanar internet ya kan samu labarai daga internet, ban da aikin kula da jikarta mai watani shida da haihuwa,abin da ya fi kauna shi ne shi ne shiga shafunan yanar internet.Mr Wen Hongjun ya ce dalilin da ya sa yana daya daga cikin mutane masu kaunar shugabannin kasar Sin shi ne yana kaunar tafarkin da shugabannin nan biyu suke bi wajen tafiyar da harkokin mulki da kuma halayyar aikinsu.

"Abu mafi muhimmanci shi ne suna aiwatar da manufar siyasa ta gaskiya,manufar da suke bi ta dace da moriyar kasarmu ta yanzu da ta nan gaba da kuma jama'a,suna kulawa da mu talakawa,suna sa mutane biliyan 1.3 a zukatansu.sun nuna kwarewarsu wajen bunkasa tattalin arziki da harkokin waje da kuma raya kasa,sun tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata,kuma sun sami nasara."

Wannan babban injiniya mai ritaya da shekarunsa sun yi daidai da na shugaban kasa Hu Jintao da firayim minista Wenjiabao ya yaba da kaunar da matasa suke nunawa shugabanin nan biyu ta hanyar internet. A ganinsa

Wadannan mutane masu amfani da yanar internet suna da sahihanci sosai.

 "Matasa sun nuna bajimta wajen bayyana ra'ayoyinsu. Wannan wata shaida ce da ta bayyana zaman daidaici da walwala da bude kofa dake kasancewa a kasar Sin. Wannan daidaici ne na sahihanci dake tsakanin talakawa da shugabani.ya kamata a ci gaba da bin wannan hanya."

Kwazo da himma da wadannan mutane masu kaunar shugabanin suka nuna sun jawo hankalin kafofin yada labarai na duniya,ciki har da jaridar "washington daily" da kamfanin dillacin labarai na Reuter da na kasar Sin,sun samar da labarai da bayanai dangane da wannan batu. A kan matsayinsa na kwararre dan jarida kuma shugban ofishin nazarin ilimin labarai da kafofin yada labarai na cibiyar kasar Sin ta ilimin kimiyyar zamantkewa,Mr Yi Yungong ya mai da hankalinsa kan wannan batu. A ganinsa kamanin kaunar jama da kusantar jama'a da shugabannin kasar Sin suke nunawa ya samu kauna daga jama'a da yawansu ke karuwa kowace rana.

"kaunar jama'a,wani halin musamman ne na shugabani na zamanimu,shi ya sa wasu mutane na son kiranshi wana Hu Jintao duk domin bayyana kaunarsu da kusantarwa,wannan ya tabbatar da amincewar jama'ar kasar Sin da shugabaninsu,wannan lakabin da shugabannin suka samu ya ba da shaida cewa shugabanni da jama'a suna kusantar juna."

A hakika,masu kaunar shugabanni daidai suke da sauran mutanen kasar Sin da kuka gani yau da kullum,abin da ya sha banban da sauran mutane shi ne masu kaunar shugabanin suna so su sa lura kan zamansu da wannan kasa da suke zaune a ciki ta hanyarsu ta musamman kamar kalmomin da suke amfani da su a yanar internet.

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na zaman rayuwar Sinawa na wannan mako,mun gode muku saboda kun saurarenmu sai wannan lokaci na mako mai zuwa za mu sake haduwa.(Ali)