Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 16:25:30    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanmu da wr haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin wanda mu kan gabatar da shi a ko wane lahadi domin shere ku.Muna fatan za ku ji dadin shirin. Sai ku kutso akwatin rediyonku ku saurara.

Binciken lafiyar jiki ya zama wani aikin jama'a a ranaikun hutu a kasar Sin.Ma'aikatan hukuma na birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin sun taru a cikin asibitoci bayan ranaikun hutu na bikin kasa duk domin bincike lafiyarsu,wannan ya riga ya zama sabon yayi a kasar Sin. Wannan ba bakon abu ba ne ga mutanen birane da suka yi amfani da ranaikun hutu da warkar da cututtukan da suke fama da su cikin dogon lokaci kamar su ciwon tumbi da ciwon gabobi.Yanzu mutane masu tarin yawa sun gane muhimmancin lafiya kamar yadda Hausawa suke fada"lafiya uwar jiki ne "saboda matsin lamba na tsananin gajiya da suka kamu da ita..Wani likita ya ce da ya ke mun sha aiki a ranaikun hutu, mun yi farin ciki da ganin mutanen da suka taru a asibitoci domin binciken lafiyarsu,wannan yana shaida cewa ma'aikatan hukuman da suka sha aiki a ofisoshin sun fara dora muhimmanci kan lafiyarsu.

Barayi sun yi wa mai gadi sata. Mr Jing Buchun yana da shekaru sittin da haihuwa,yana aiki a matsayin dan gadi mai sa kai ga kauyen da yake zama a ciki cikin shekaru sama da ashirin da suka gabata domin kare kauye daga barayi. Tun daga shekara ta 1987 ne ya fara yawon sintiri a kauyen da dare tare da wata fitila ya kuma yi kuwwa ga kauyawa da su sa hankali kan barayi. Cikin shekaru sama da ashirin da suka shige,dukkan gidajen kauyen sun sami tsaro mai kyau ban da na mai gadi Jing. A wata rana da dare a watan jiya wasu barayi sun shiga gida mai gadi sun yi masa sata yayin da yake yin sintiri a waje.

Ashe bom ne na iya tashi. An sami wani mutum a birnin Shijiazhuang,babban birnin lardin Hebei dake arewancin kasar Sin da ya gano wani abin cylinder yana tsammanin abin cylinder na daukar iskar Oxygen sai ya tafi da shi gida. Ya ajiye shi a gida yana neman sayar da shi. A ranar lahadin da ta shige,wani abokinsa mai arziki ya zo gidansa ya gano wani abin cylinder a kwance a dakin barci.nan take ya sanar da 'yan sanda. Da 'yan sanda sun isa wurin,sun yi bincike cikin nituswa. Daga baya sun gane cewa ashe wani bom ne da ke iya tashi ko wane lokaci. 'Yan sanda sun sanar da jama'a idan sun sami wani abun da ba su iya gane shi mene ne ba sai su kira 'yan sanda.