Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 14:42:52    
Makomar dangantakar da ke tsakanin EU da Amurka bayan da Obama ya hau kujerar mulki

cri

An kawo karshen babban zaben shugaban kasar Amurka bayan da 'dan Jam'iyyar Demokuradiya Mr. Barack Obama ya samu nasara. Bayan da aka sanar da wannan labari, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai wato EU Mr. Jose Manuel Barroso ya bayar da wata sanarwa, domin taya murna ga Obama, haka kuma ya ce, lokacin ya yi ga EU da kasar Amurka da su sake daukar alkawari dangane da dangantakar da ke tsakaninsu. Wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum suna ganin cewa, shugaba na farko 'dan asalin Afirka a kasar Amurka zai kawo sabuwar dama da sabon kalubale ga dangantakar da ke tsakanin EU da kasar Amurka.

Ban da Mr. Jose Manuel Barroso, shugaban kasar Faransa Mr. Nicolas Sarkozy, da firayin ministar kasar Jamus Madam Angela Merkel, da firayin ministan kasar Britaniya Mr. Gordon Brown da shugabannin manyan kasashe daban daban na Turai, da kuma babban wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da tsaro Mr. Javier Solana, da kuma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mr. Jaap de Hoop Scheffer sun taya murna tun can farkon lokacin bayan da Obama ya samu nasara. A ganin wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum, wannan yanayi yana kama da hanyoyin da Turai take bi wajen taya murna a yayin da Mr. John F. Kennedy ya zama shugaban kasar Amurka a shekarar 1960.

A yayin da kasashen Turai suke sanya ran ganin wata kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin Turai da Amurka, a hakika dai, ba a iya tabbatar da cewa, ko Obama zai samar da moriya ga Turawa ko a'a. Wasu jami'ai masu nazarin lamuran yau da kullum suna ganin cewa, ko da yake tunanin Obama ya yi daidai da fatan da kungiyar EU take yi wajen sake kaddamar da wani tsarin kudi a duk duniya, amma a matsayin shugaban kasar Amurka, matsala ta farko da Obama zai daidaita bayan da ya hau kujerar mulki ita ce, maido da tattalin arzikin Amurka, ba ma aikin sake gina wani tsarin tattalin arziki na duk duniya ba. Wasu mutane sun bayyana cewa, Turawa sun nuna goyon baya ga Obama bisa ra'ayinsu kawai. Da farko dai, Obama ya zama wani 'dan siyasa ne, domin neman samun nasara a babban zabe, zai yi gyare gyare kan manufofinsa bisa ga halin da ke canzawa, zai canza ra'ayoyinsa da sauri. Haka kuma babu abun tabbas game da manufofin da Obama zai gudanar bayan da ya hau kujerar mulki. Wasu sun ce, tilas ne Turawa sun farka kome zaton da suke yi kan Obama, haka kuma kada su cuci kansu. Babu sauki ga Mr. Obama da zai yi watsi da ka'idojin da kasar Amurka take aiwatarwa a matsayin wata babbar kasa a gamayyar duniya, ba wani abu mai sauki ne wajen samun babban canji daga dangantakar da ke tsakanin Turai da kasar Amurka.(Danladi)