Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-05 20:48:23    
Kasar Sin ta kara karfinta na raya aikin wasan kwallon kafa na yara da matasa

cri
A matsayin wasan motsa jiki mafi samun karbuwa a duniya, wasan kwallon kafa ya sami karbuwa daga mutanen da shekarunsu ya sha bamban a sassa daban daban na duniya. Har kullum, bunkasuwar wasan kwallon kafa na yara da matasa ya jawo hankulan kasashen duniya sosai, har ma sun dade suna nazari a wannan fanni. Shirin wasan kwallon kafa na gasar wasannin Olympic yana matsayin dandamalin da 'yan wasan kwallon kafa matasa da shekarunsu bai kai 23 da haihuwa ba a wurare daban daban na duniya suka iya nuna kwarewarsu. Bayan rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, kasar Sin ta kara dora muhimmanci kan raya wasan kwallon kafa na yara da matasa. A kwanan baya, wakilinmu ya zanta da Zhu Heyuan, shugaban sashin kula da yara da matasa na hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin.

Dukkan 'yan wasan kwallon kafa suna Alla-Alla wajen samun nasara., amma a maimakon samun maki mai kyau, an fi dora muhimmanci kan gano wadanda za a iya habaka kwarewarsu, don su zama nagartattun 'yan wasa a nan gaba. A cikin wasu muhimman gasannin wasan kwallon kafa na yara da matasa a Asiya, ko da yake 'yan wasan kasar Sin yara da matasa ba su shiga karon karshe ba, amma sun ji dadin wasa da kwallon kafa. Zhang Jian, dan wasa ne daga kungiyar wasan kwallon kafa ta matasa ta kasar Sin ya kyautata zato kan makomarsa a filin wasan kwallon kafa. Ya ce,"Ina tsammani sakamako mafi kyau da na samu daga wajen shiga wannan gasa shi ne kyautata fasahohina na shiga gasannin duniya. Bayan gasar, mun takaita sakamakon da muka samu a fannonin mu kanmu da dabarorin kungiyarmu na yin gasa da dai sauransu. Bayan shiga wadannan gasanni, bayan da muka kwatanta mu da saura, mun gano bambanci mafi girma a tsakaninmu shi ne tunani."

A ganin Mr. Zhu, nuna fara'a ga makoma bayan da wadannan 'yan wasa yara da matasa suka sha kaye a cikin gasa yana matsayin babban ci gaba ne mai daraja. Shiga wadannan muhimman gasannin duniya na kasancewa wata dama ce ta horar da wadannan kananan 'yan wasa. A idon masu horas da wasanni kuwa, sakamako mafi kyau da suka samu shi ne gano wasu 'yan wasa matasa masu kwarewa. Mr. Zhu ya bayyana cewa, a yayin da ake zaben 'yan wasa yara da matasa, idan an mai da hankali kan yanayin jikunansu kawai, an kyale fasaharsu, yau da gobe za a sha kaye.

A yayin da muka kwatanta matsayin wata kasa a fannin bunkasuwar wasan kwallon kafa, tilas ne mu mai da hankali kan yawan lambobin yabo da kungiyoyin wannan kasa a matakan shekarun 'yan wasa daban daban suka samu, sa'an nan kuma, ya kamata mu zura ido kan yaduwar wasan kwallon kafa a wannan kasa. Mr. Zhu yana ganin cewa, yaduwar wasan kwallon kafa a wata kasa ya fi muhimmanci. Saboda a matsayin wani wasan motsa jiki, wasan kwallon kafa ba kawai ya iya sa a motsa jiki ba, har ma ya taka muhimmiyar rawa ta fuskar zaman al'ummar kasa, ya iya jagoranci yara da matasa da su nemi bin hanyar zaman rayuwa mai kyau. Mr. Zhu ya ce,"Alal misali, a cikin tsarin mulkinta, hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya ta nuna a bayyane cewa, wasan kwallon kafa yana iya jagorantar yara da matasa da su nemi samun koshin lafiya da nisantar da su daga miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka. Muhimmiyar manufarmu ita ce jagorantar yara da matasa da su yi kishin wasan kwallon kafa da samun koshin lafiya a jiki da tunani da nisantar da su daga dukkan abubuwan marasa kyau. Wasan kwallon kafa na iya taka muhimmiyar rawa ta fuskar zaman al'ummar kasa a wadannan fannoni."

A shekarun baya, a karkashin taimako daga hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin tana yada wasan kwallon kafa a kasar Sin. Mr. Zhu ya nuna cewa,"Yaya za a kara raya wasan a kasar Sin? Yanzu muna nan muna hada gwiwa da kwamitocin ilmi na wurare daban daban na kasar Sin domin neman samun hanyoyin da suka fi dacewa wajen yada wasan, ta haka wasan kwallon kafa zai kara samun karbuwa a kasar Sin."

Mr. Zhu ya kara da cewa, domin bai wa yara da matasa masu kwarewar wasan kwallon kafa damar shiga gasanni, yanzu hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sin tana nan ta dukufa wajen inganta raya hadaddun gasannin wasan kwallon kafa a matakai daban daban.

Ya ci gaba da cewa, ta hanyar kara karfin horar da 'yan wasa yara da matasa, a karshe dai, kasar Sin za ta kyautata karfinta na yi takara a filin wasan kwallon kafa, wannan shi ne makasudin da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sin ke tsayawa tsayin daka kan tabbatar da shi.(Tasallah)