Masu sauraro, yanzu bari in kawo muku wani labari kan gasar wasannin Olympic ta zamani. An shirya gasar wasannin Olympic a karo na farko da na 2 a kasashen Turai, dalilin da ya sa haka shi ne domin an fara shirya gasar wasannin Olympic ta zamanin da a Turai. Amma a zuciyar Mr. de Coubertin, ya kamata a sauya sannu wajen shirya gasar wasannin Olympic a duk duniya. Duk da haka, a idon Mr. Coubertin, ma'anar duk duniya ita ce nahiyoyin arewacin Amurka da kuma Turai a hakika.
Saboda 'yan wasan Amurka sun yi fintikau a gasar wasannin Olympic a karo na farko da na biyu, sa'an nan kuma, Mr. Coubertin ya fito da makasudin shirya gasar wasannin Olympic a duk duniya, shi ya sa kwamitin wasan Olympic na duniya ya ba birnin Chicago na kasar Amurka damar shirya gasar wasannin Olympic a karo na 3.
Da jin wannan labari mai farin ciki, mazauna birnin Chicago sun yi murna sosai, har ma sau daya kawai suka ba da kudin taimako mai yawan dalar Amurka dubu 120. Sun yi niyyar shirya gasar wasannin Olynmpic ta karo na 3 mai kayatarwa, in an kwatanta ta da ta karo na farko da na 2.
Amma mazauna Chicago ba su yi farin ciki a cikin dogon lokaci ba, lamarin ya sami babbar sauyawa. Wani birni na daban Amurka wato St. Louis shi ma ya yi matukar fatan samun karbar bakuncin gasar wasannin Olympic a karo na 3, sa'an nan kuma, ya sami goyon baya daga shugaba Theodore Roosevelt na Amurka a wancan lokaci kai tsaye, wannan shugaba ya kuma aika da sakon taligram zuwa ga kwamitin wasan Olympic na duniya, inda ya bukaci a bai wa St. Louis damar karbar gasar wasannin Olympic a karo na 3 a maimakon Chicago, ya kuma tabbatar da cewa, Amurka za ta koyi darasin da aka samun daga wajen gasar wasannin Olympic a birnin Paris, za ta shirya gasar wasannin Olympic da ta sami gamsuwa sosai. Bayan da kwamitin wasan Olympic na duniya ya yi tattaunawa, a karshe dai, ya yarda da bukatar Mr. Roosevelt.
Birnin St. Louis babban birni ne na 8 a Amurka. Akwai tsarin zirga-zirga na ci gaba a wannan birni. Amma a wancan lokaci, an hada nahiyar Turai da ta Amurka ta hanyar jirgin ruwa ne kawai. Tikitin jirgin ruwa na da tsada sosai, haka kuma, a kan dauki kwanaki 10 cikin jirgin ruwa daga Turai zuwa Amurka, shi ya sa 'yan wasa da yawa na Turai ba su so su je nahiyar Amurka ba. A karshe dai, ko da yake birnin St. Louis ya yi alkawarin shirya gasar wasannin Olympic mafi karbuwa a tarihin gasar wasannin Olympic, amma yawan 'yan wasa da mazauna St. Louis suke zura ido don karba bai fi yawan 'yan wasa da suka kiyasta ba, 'yan wasa fiye da dari 6 kawai suka shiga gasar wasannin Olympic ta karo na 3, sa'an nan kuma, a cikin wadannan 'yan wasa sama da dari 6, yawancinsu sun zo daga kasar Amurka, yawan wadanda suka zo daga kasashen waje ya kai 107. Shi ya sa mutane masu yawa suke ganin cewa, a hakika wannan gasar wasannin Olympic ta zama gasar wasannin Olympic ta Amurkawa, 'yan wasa da suka zo daga sauran kasashe sun kasance abun ado ne kawai. Ko da yake wannan ya sa bakin ciki, amma gasar wasannin Olympic ta fita daga nahiyar Turai, wannan yana matsayin muhimmiyar ishara ce a tarihin raya gasar wasannin Olympic.(Tasallah)
|