Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 18:32:00    
Bikin baje kolin kayayyakin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya na kasar Sin a birnin Zhuhai

cri
Yau aka bude bikin baje kolin kayayyakin zirga-zirgar sararin samaniya karo na bakwai na kasar Sin a birnin Zhuhai da ke kudancin kasar Sin. A gun bikin, an nuna jerin sabbin jiragen saman yaki da kasar Sin ta kera, kuma muhimman kamfanonin kera kayayyakin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya na kasar za su daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da kasashe da dama.

A kan gudanar da bikin sau daya a ko wadanne shekaru biyu, kuma bikin da ake gudanarwa a wannan karo ya fi kasaita. Za a shafe kwanaki shida ana bikin, wanda ya jawo kamfanoni kusan 600 da suka zo daga kasashe da yankuna 35. Sun zo ne tare da fasahohin zamani da kayayyakin zamani a fannin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya, kuma jiragen sama da aka nuna a gun bikin sun kai kusan 60.

Abin da ya jawo hankulan jama'a shi ne a gun bikin, an nuna sabbin kayayyaki da fasahohi da Sin ta samu a fannin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya. A gun bikin, manyan kamfanonin kera kayayyakin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya na kasar Sin sun zo tare da kayayyakin zamani da suka kera. Mr.Jia Ke, wani jami'in kamfanin fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin ya ce, bikin ya samar da wani dandali na nuna nasarorin da Sin ta samu a wajen zirga-zirgar sararin sama da na samaniya, da kuma yin musanyar ra'ayoyi da jama'a. Ya ce,"Kayayyakin da muka zo da su suna shafar fannoni daban daban, ciki har da tsarin zirga-zirgar sararin samaniya da tsarin makamai masu linzami da fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya da dai sauransu. A wannan karo, mun gabatar da wani sabon hasashe, wato kungiyar ba da agaji cikin sararin samaniya, don biyan bukatun bunkasuwar tattalin arziki, musamman domin yaki da bala'u da ba da agaji cikin gaggawa."

A lokacin bikin, muhimman kamfanonin kera kayayyakin zirga-zirgar sararin sama da na samaniya na kasar Sin za su daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da na sayayya tare da kasashe da dama. Abin da ya jawo hankulan jama'a shi ne kamfanin kera jiragen saman haya na kasar Sin zai samar wa kamfanin GE na Amurka jiragen sama 25 na sabon salo da Sin ita kanta ta kirkiro, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 5, wato a karo na farko Sin za ta fitar da jiragen saman fasinja zuwa kasuwannin Amurka da na Turai.

Kwanan baya, wani jami'in ma'aikatar masana'antu da fasahar bayanai ta kasar Sin ya bayyana cewa, za a fitar da manyan jiragen saman fasinja da Sin ta kirkiro da kanta zuwa kasuwanni kafin shekarar 2020. Yanzu kamfanin jiragen saman haya na kasar Sin na daukar nauyin kirkiro manyan jiragen saman fasinja, Madam Xue Li, wata jami'a a kamfanin ta ce, yanzu ana gudanar da ayyukan nazari yadda ya kamata. Ta ce,"muna kafa wata kungiyar nazari da za ta kunshi masana sama da 300, kuma yanzu an shiga mataki na tabbatar da yiwuwar aikin manyan jiragen sama da aka kirkiro. Mun kafa wani kwamitin masana, kuma za mu kafa wani kwamiti na sa ido."

Ban da wadannan, ana kuma nuna jiragen sama na sabon Salo da manyan kamfanonin kera jiragen sama na duniya suka kera, ciki har da Boeing da Airbus da kuma Bombadier. (Lubabatu)