Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 19:17:49    
Wu Bangguo zai kai ziyara kasashen Afirka 5 nan ba da jimawa ba

cri
Shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Wu Bangguo, zai fara rangadinsa na sada zumunta a hukunce a kasashen Afirka biyar daga ranar Litinin din nan ne bisa goron gayyatar da shugabannin majalisun dokokin kasashen suka yi masa, ciki har da Aljeriya, da Gabon, da Habasha, da Madagascar tare kuma da Seychelles. Haka kuma, zai ziyarci kungiyar tarayyar Afirka wato AU mai hedkwata a Addis Ababa, babban birnin Habasha. Jami'an kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na ma'aikatar harkokin wajen kasar na ganin cewa, ziyarar Wu Bangguo a wannan gami ta kasance wani muhimmin matakin diflomasiyya da kasar Sin ta dauka kan nahiyar Afirka bayan da ta shirya taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2006.

A cikin ziyararsa a kasashen Afirka biyar, Wu Bangguo zai yi shawarwari tare da shugabannin majalisun dokokinsu, inda za su yi musayar ra'ayi kan inganta da fadada hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin hukumomin tsara dokokin shari'a na bangarorin biyu, kuma Wu Bangguo zai gabatar da dimbin nasarorin da Sin ta samu a fannin raya tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da tsarin dimokuradiyyarta. A ganin mataimakin babban magatakardan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Cao Weizhou, ta hanyar yin cudanya tsakanin majalisun dokoki ne, labuddah ziyarar Wu Bangguo a wannan gami za ta daukaka cigaban dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin Sin da wadannan kasashen Afirka biyar. Cao ya ce,"Majalisar dokoki, hukumar koli ce ta tsara dokokin shari'a ta kowace kasa. Inganta mu'amala da hadin-gwiwa tsakanin hukumomin tsara dokokin shari'a zai yaukaka dankon aminci a tsakaninsu. A waje daya kuma, koyon nasarorin da majalisun dokoki na kasashe daban-daban ke samu na da muhimmiyar ma'ana wajen bunkasa huldar bangarorin biyu. Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na fatan cigaba da zurfafa mu'amala da cudanya a tsakaninta da majalisun dokokin kasashen Afirka biyar daga dukkan fannoni, da gudanar da aikin cude-ni-in-cude-ka tsakanin majalisun dokokin Sin da Afirka."

A hukumance, Wu Bangguo zai soma rangadinsa a ranar 4 ga wata. Ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar 2006, rana ce da aka kaddamar da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka. A wajen taron, shugabanin Sin da Afirka sun cimma daidaito kan kafa da raya sabuwar dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Afirka bisa amincewar juna a fannin siyasa, da hadin-gwiwa da neman cimma moriyar juna a harkokin tattalin arziki, da yin mu'amala a fannin al'adu. A daidai wannan lokaci na cika shekaru biyu da bude taron koli na Beijing, Wu Bangguo ya sake yada zango a nahiyar Afirka. A ganin madam Xu Jinghu, shugabar ofishin kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ziyarar sada zumunta da Wu Bangguo zai kai kasashen Afirka, za ta amfana wajen ciyar da dangantakar Sin da Afirka gaba cikin kwanciyar hankali. Madam Xu ta ce,"A shekarar 2006 a Beijing, an kaddamar da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka. Shekarar da muke ciki, shekara ta biyu ce wajen tabbatar da dimbin nasarorin da aka samu a gun taron kolin. Ziyarar Wu Bangguo a wannan gami, ba ma kawai za ta sa kaimi ga bunkasar huldar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin Sin da wadannan kasashen Afirka biyar ba, hatta ma za ta zurfafa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa mai sabon salo da aka tabbata a gun taron koli na Beijing."

Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin ziyarar Wu Bangguo a kasashen Afirka biyar a wannan gami, ba ma kawai zai yi shawarwari tare da shugabannin majalisun dokoki da na gwamnatocin wadannan kasashe ba, hatta ma zai halarci bikin rattaba hannu kan takardun yin hadin-gwiwa tsakanin Sin da kasashen da abun ya shafa a fannin tattalin arziki da fasahohi, da ganema idonsa yadda ake gudanar da ayyukan cude-ni-in-cude-ka tsakanin Sin da Afirka. Madam Xu Jinghu ta kara da cewa,"A cikin ziyarasa a Afirka a wannan gami, Wu Bangguo zai je ganema idonsa da duba yadda ake yi don tabbatar da nasarorin da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, da daukaka cigaban sabuwar dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin bangarorin biyu. A waje daya kuma, zai fadada hadin-gwiwar bangarorin biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya."(Murtala)