Sabo da bukatar musamman da tarin musulmi ke yi wajen abinci, shi ya sa sana'ar yin abincin musulmi kullum take jerin gaba daga cikin sana'o'in da musulmi suke gudanarwa. Kamfanin Yili shi ne kamfani mafi girma na kasar Sin wajen yin kayayyakin madara na musulmi, Mr. Song Bing, jami'in reshen shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin na wannan kamfani wanda ya halarci taron ya bayyana cewa,
"Abincin da muke yi su ma na musulmi ne, mun zo nan ne don yin shawarwari tare da sauran mutane domin samun damar yin hadin gwiwa tare da su wajen harkokin kasuwanci. Na 2 kuma domin fadakar da kanmu kan al'adun 'yan kasuwa na kabilar Hui, ta wannan taro ne muka fahinci 'yan kasuwa na kabilar Hui sosai wajen tunani da shirin kungiya da kuma makomarsu."
Jihar Ningxia jiha ce mai cin gashin kanta ta kabilar Hui ta matakin lardi daya tak ta kasar Sin, inda mutane musulmi fiye da miliyan 2 suke zaune. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Ningxia ta kaddamar da manufofi da yawa domin ba da taimako ga bunkasa sana'o'in musulmi wadanda sana'ar yin abincin musulmi ke wakiltarsu. Madam Hong Xiangmei, shugabar karamar kungiyar shugabanci ga bunkasa sana'o'in yin abinci da kayayykin masarufi na musulmi ta birnin Yinchuan ta bayyana cewa,
"Gwamnatin wurin da musulmin ke zaune ta lura kuma ta mai da hankali sosai kan wannan sana'a wato sana'ar yin abincin musulmi, ta mai da ita bisa matsayi mai rinjaye kuma mai sigar musamman, kuma ta kafa kungiyoyi da hukumomi na musamman da ware kudin musamman domin bunkasa wannan sana'a, sa'an nan kuma gwamnatin wurin ta tsai da manufofi masu nagarta, da yin jagoranci, da samun daidaici, da nuna goyon baya, da kuma ba da hidima ga wannan sana'a daga fannoni daban-daban, ta yadda za a kara inganta masana'antu masu tafiyar da wannan sana'a." 1 2
|