Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-31 14:38:35    
An tattauna kan yadda za'a tinkari matsalar kudi a gun babban taron musamman na MDD

cri

Babban taro a karo na 63 na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya zama na musamman a ranar 30 ga wata a New York, inda mahalarta taron daga kasashe daban-daban, da sanannun kwararru a fannin tattalin arziki suka yi tattaunawa kan yadda za'a shawo kan matsalar hada-hadar kudi da ta zama ruwan dare a duniya, Mahalarta taron suna ganin cewar, ya kamata a yi garambawul ga tsarin hada-hadar kudi na duniya.

A cikin jawabin da ya yi a gun bikin kaddamar da taron, shugaban babban taron MDD a wannan zagaye Miguel D'Escoto Brockman ya bayyana cewar, kamata ya yi a yi kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudade na duniya daga tushensa. Yana ganin cewar, ya kamata gamayyar kasa da kasa su dauki nauyin dake bisa wuyansu na tattaunawa kan matakan da za su dauka cikin dogon lokaci, amma ba ma kawai su tattauna kan matakan da za su dauka na kankanin lokaci ba, kamar su kiyaye bankuna, da tabbatar da dorewar kasuwannin bada rancen kudi da dai sauransu.

Brockman ya jaddada cewar, hanyar da za'a bi wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya ita ce, kafa wani sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya, wanda zai samu halartar dukkanin kasashen duniya a ciki ta hanyar dimokuradiyya.

Wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel a fannin tattalin arziki, kana kuma shi ne tsohon kwararre na farko kan harkokin tattalin arziki na bankin duniya, Joseph Stiglitz ya nuna cikakken goyon-bayansa ga matsayin Brockman, yana ganin cewar, lokaci ya yi na kafa wani "Tsarin Bretton Woods" na daban. Ya kuma jaddada cewar, ya kamata a mutunta muhimman ka'idoji hudu yayin da ake kokarin tinkarar matsalar kudi, ciki har da tabbatar da adalci da hadin-kan al'umma, da inganta hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kiyaye daidaito tsakanin gwamnati da kwasuwanni, na karshe kuma a gudanar da harkoki ta hanyar dimokuradiyya kuma ba tare da rufa-rufa ba.

A cikin jawabin da ya yi, Stiglitz ya nuna kushewa kan kura-kuran da gwamnatin Amurka da sauran gwamnatin kasashe suka yi a lokacin da, ya ce, da yake kasashe daban-daban suna daukar matakai iri-iri don ciccibo kasuwannin hada-hadar kudadensu, amma sun gaza biyan diyya ga wadanda suka rasa kadarorin gidajensu da guraben aikin yi.

A waje daya kuma, Stiglitz ya nuna cewar, wasu sabbin kasuwannin hada-hadar kudi masu tasowa a duniya ba su da hannu sosai cikin haddasa wannan mummunan rikicin kudi, amma suna jin radadin rikicin a jikinsu. Shi ya sa, Stiglitz ya bada shawarar cewa, dole ne a yanke muhimman shawarwari kan harkokin hada-hadar kudi na duniya a wata halattacciyar hukumar kasa da kasa wadda ke kunshe da wakilanta da dama, kamar ita Majalisar Dinkin Duniya.

A waje daya kuma, mahalarta taron sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwa da dama, ciki har da yadda za'a yi don yin kwaskwarima ga tsarin hada-hadar kudi na duniya, da fadada hadin-gwiwa tsakanin bangarori daban-daban da dai sauran makamantansu. Wakilin kasar Faransa wanda ya wakilci kungiyar tarayyar Turai ya yi jawabi cewar, kada kasashe daban-daban su yi kokarin yiwa tubkar hanci kawai kamar yadda suka yi a lokacin da domin daidaita wannan rikicin kudi, ya kamata su dukufa ka'in da na'in wajen kafa wani sabon shirin sa ido kan harkokin kudade na kasa da kasa. Kazalika kuma, a cikin jawabin wakilin kasar Antigua da Barbuda wanda ya wakilci rukunin kasashe 77 da kasar Sin, ya bayyana cewar, yayin da kasashe daban-daban suka maida hankulansu kan shawo kan matsalar hada-hadar kudaden duniya, kamata ya yi su yunkura wajen tada komadar tattalin arzikin duniya wanda ke tafiyar-hawainiya a halin yanzu.

Bugu da kari kuma, kwararru da wakilai mahalarta taron sun nuna rashin gamsuwa game da tsarin dudduba da sa ido kan harkokin tattalin arziki na yanzu. Kasashe masu tasowa sun bukaci da a kafa wani sabon dandamali domin samun cikakken tabbaci da goyon-baya wajen raya kansu. Haka kuma, wakilai daga kasashe da dama sun nuna cewar, ya kamata MDD ta fito fili don jagorantar aikin kafa sabon tsarin hada-hadar kudi na duniya.(Murtala)