Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-29 17:39:41    
Kasar Sin ta kaddamar da muhimmiyar takardar manufofi da matakai don tinkarar sauyawar yanayi

cri

Ran 29 ga wata, a nan Beijing, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata muhimmiyar takarda wato 'manufofi da matakai da kasar Sin ta dauka don tinkarar sauyawar yanayi', inda aka yi karin bayani kan illar da sauyawar yanayi ke kawo wa kasar Sin, da manufofi da matakai da kasar Sin ta dauka domin sassauta da dacewa da sauyawar yanayi, da kuma ayyukan da kasar Sin ta yi na kafa tsare-tsare a fannin. Wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta gano muhimmancin daidaita sauyawar yanayi sosai, haka kuma, tilas ne a tinkari sauyawar yanayi cikin gaggawa. Tana son ta gama kanta da kasashen duniya su yi kokari wajen tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa.

Bisa wannan muhimmiyar takarda mai suna 'manufofi da matakai da kasar Sin ta dauka domin tinkarar sauyawar yanayi', an ce, a shekarun baya da suka wuce, kasar Sin tana ta sa himma sosai domin sassauta da samar da dacewa da sauyawar yanayi. A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 29 ga wata, Xie Zhenhua, mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta sami kyakkyawan sakamako bisa kokarin da take yi. Mr. Xie ya ce,"Tun daga shekarar 1990 zuwa ta 2005, kasar Sin ta kyautata yin amfani da makamashi wajen samar da jimlar GDP ko kuma irin kayayyakin da gdia ta samar da kashi 47 cikin dari. Kasar Sin ta kuma gabatar da makasudi daban, wato bisa shekarar 2005, kasar Sin za ta tabbatar da rage yin amfani da makamashi wajen samar da jimlar GDP da kashi 20 cikin dari a shekarar 2010. A shekarar 2007, yawan makamashi da kasar Sin ta yi amfani da shi wajen samar da jimlar GDP ya ragu da kashi 5.38 cikin dari bisa na shekarar 2005, wato kasar Sin ta rage fitar da iskar carbon dioxide mai yawan ton miliyan 335. "

Game da batun fitar da iska mai dumama yanayi, Mr. Xie ya jaddada cewa, kamata ya yi a daidaita yawan iskar carbon dioxide da kasar Sin ke fitarwa daga dukkan fannoni cikin adalci bisa abubuwa yadda suke kasancewa kuma bisa abubuwan da suka faru a tarihi. Ya kara da cewa, yanzu kasar Sin tana matakin raya masana'antu da birane. Bisa halin da kasashe masu sukuni suka taba kasancewa, a cikin wannan mataki, kasar Sin ta kan sami saurin karuwar yawan iska mai dumama yanayi, wannan na matsayin wata ka'idar da aka saba bi. Sa'an nan kuma, a cikin jimlar iskar carbon dioxide da kasar Sin ke fitarwa, an samu kashi 20 cikin dari daga masana'antun sarrafa kayayyakin da ake fitarwa. Shi ya sa aka dauka cewa, kasashe masu sukuni sun yi amfani da kayayyaki, amma kasar Sin tana fitar da iskar carbon dioxide daga wajen kera wadannan kayayyaki.

Mr. Xie ya yi bayani cewa, ko da yake wadannan dalilai suna iya kasancewa, amma kasar Sin tana dora muhimmanci kan rage fitar da iska mai dumama yanayi. Yana kuma ganin cewa, dole ne kasashe masu sukuni da masu tasowa su dauki alhakin daukar matakai domin sassauta da samar da dacewa da sauyawar yanayi, amma yanzu ya kamata kasashe masu sukuni su dauki karin alhaki. Mr. Xie ya ce,"Bisa bukatun da 'yarjejeniyar UNFCCC da kuma 'takardar shawara ta Kyoto' suka bayar, dole ne kasashe masu sukuni su dauki jagoranci wajen rage fitar da iska mai dumama yanayi. Muna fatan kasashe masu sukuni su biya bukatun 'takardar shawara ta Kyoto', za su ci gaba da rage fitar da iska mai dumama yanayi da kashi 25 zuwa kashi 40 cikin dari a shekarar 2020, bisa na shekarar 1990. Sa'an nan kuma, muna fatan kasashe masu sukuni za su dauki alhakin da ya kamata su dauka a fannonin yin musayar fasaha da bayar da kudi bisa yarjejeniyar da kuma takardar shawarar. Bayan da kasashe masu sukuni suka cika alkawarinsu, to, wajibi ne kasar Sin da kasashe masu tasowa su dauki matakai cikin kwazo, za su rage saurin karuwar iska mai dumama yanayi bisa halin da suke ciki."

Dadin dadawa kuma, Mr. Xie ya nuna cewa, matsalar kudin da ta ratsa duk duniya a yanzu ba za ta lalata shawarwari a tsakanin kasashen duniya kan tinkarar sauyawar yanayi ba.(Tasallah)