Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-29 09:15:23    
Kasar Sin za ta kara shirya gasar duniya ta matsayin koli bayan gasar wasannin Olympic

cri

A watan Agusta na bana, birnin Beijing na kasar Sin ya shirya zama na 29 na gasar wasannin Olympic kuma ya sami cikakkiyar nasara. Amma bayan wannan kuma, ko kasar Sin za ta ci gaba da shirya gasar duniya ta matsayin koli ko ba za ta shirya ba? Game da wannan, babban manajan kamfanin gudanar da gasar duniya na 'Jiushi' na birnin Shanghai kuma mai shirya gasar mota ta ba da babbar kyauta ta kasar Sin ta F1 da gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis ta Shanghai Jiang Lan yana ganin cewa, ko shakka babu kasar Sin za ta kara shirya gasar duniya ta matsayin koli. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani kan wannan.

A ran 19 ga wata, an fara gasar mota ta ba da babbar kyauta ta kasar Sin ta F1 ta shekarar 2008 a filin gasar mota ta duniya na birnin Shanghai, bisa matsayinta na gasar duniya ta matsayin koli ta karo na farko da ake shirya a kasar Sin bayan da aka kawo karshen gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, wannan tasha ta gasar ta jawo hankulan masu sha'awar wasannin motsa jiki dubu gomai, wato yawansu ya yi kusa da na 'yan kallo na gasar wasannin Olympic. Wannan ya alamanta cewa, sinawa suna kara sha'awar gasar duniya ta matsayin koli a kwana a tashi. Jiang Lan, babban manajan kamfanin gudanar da gasar duniya na 'Jiushi' na Shanghai ya hakake cewa, huldar dake tsakanin sinawa da gasar duniya ta matsayin koli za ta kara karfafuwa. Ya ce,  "Ina tsammani huldar nan za ta kara ingantuwa a kai a kai, tun karo na farko da muka shirya gasar wasan kwallon tennis, shekaru goma sun wuce ke nan, yanzu dai tushen kasuwa a kasar Sin yana kara kyautatuwa a bayyane. Na biyu kuma, kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, shi ya sa ana iya cewa, gasar duniya za ta taimake mu wajen kara habaka tasirinmu a duniya. A sabili da haka, ko daga bukatun kasuwa ko daga hakikanin halin kasuwar da kasar Sin ke ciki yanzu, ana iya cewa, kamata ya yi mu ci gaba da shirya gasar duniya ta matsayin koli."

Kamar yadda kuka sani, gasar F1 da gasar wasannin Olympic da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa su ne gasa mafi muhimmanci uku a duniya, kawo yanzu, tarihinsu ya riga ya kai shekaru fiye da 50, ana watsa labaran kowacen tasha ta gasar F1 ta gidan rediyo mai hoto kai tsaye a kasashe fiye da 180 kuma 'yan kallon gasar sun kai fiye da miliyan 300. Kasar Sin ta fara shirya gasar F1 a shekarar 2004, a sanadiyar haka, Shanghai ya kara yin suna a duniya, ana iya cewa, gasar F1 ta ciyar da bunkasuwar sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin gaba bisa babban mataki. Jiang Lan ya ce, "Ana iya ganin tasirin da gasar F1 ta haifa a kasar Sin da sauki, a hakika dai, yanzu a kasar Sin, gasar F1 da gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis sun fi jawo hankulan kasashen duniya. Ana iya cewa, gasar nan biyu suna daukan nauyin bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin bisa wuyansu."

Jiang Lan ya ci gaba da cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ba gasar duniya ta matsayin koli daya kadai da kasar Sin ta shirya ba, sai dai ta bude wani sabon shafi ga kasar Sin wajen shirya gasar duniya ta matsayin koli a nan gaba. Ya ce, "Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne domin kuzari da sha'awa na sinawa kan wasannin motsa jiki suna kara habaka bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ban da wannan kuma, manyan masana'antu daban daban su ma sun tarar da amfanin musamman na kasuwar wasannin motsa jiki, duk wadannan sun kago wajababbun sharuda ga yalwatuwar gasar duniya ta matsayin koli a kasar Sin a nan gaba."(Jamila Zhou)