A ran 25 ga wata, an rufe taron shugabannin kasashen Asiya da Turai na karo na 7, wato taro mafi girma cikin tarihin tarurrukan shugabannin kasashen Asiya da Turai a nan birnin Beijing. Lokacin da ake fuskantar matsalar hada hadar kudi a duk duniya, membobi 45 na taron kasashen Asiya da Turai dukkansu sun bayar da manufofi da shawara kan yadda za a tinkari wannan matsala tare. Tabbas ne wannan mataki zai yi muhimmin tasiri ga kokarin shawo kan matsalar hada hadar kudi a duniya.
Jimlar GDP na dukkan membobi 45 na taron kasashen Asiya da Turai ya kai kashi 50 cikin kashi dari bisa na jimlar yawan GDP na duk duniya, a waje daya, jimlar kudaden cinikin waje da ake yi a wadannan kasashe ya kai kashi 60 cikin kashi dari bisa na dukkan kasashen duniya. Kamar yadda Mr. Nicolas Sarkozy ya fadi a gun taron, kasashen Asiya da Turai sun hada kan juna sun yi fama da matsalar hada hadar kudi ta duniya tare, ko shakka babu yana da ma'ana mai muhimmanci. Mr. Sarkozy ya ce, "Yawan mutanen kasashen Asiya da na Turai ya kai kashi 2 cikin kashi 3 bisa na duk duniya, kuma yawan dukiyoyinsu ya kai rabi bisa na duk duniya. Ko kasashen Asiya da Turai za su iya tinkari kalubalen da ke kasancewa a gabansu tare ita kuma wata matsala ce da ke kasancewa a gabansu. Yin hadin guiwa a tsakaninmu ba wani zabi ne kawai ba, hatta ma wani nauyi ne da ke bisa wuyanmu. Kasashen Turai suna bukatar cigaba da hazikanci da karfin kirkire-kirkire na kasashen Asiya, a waje daya, kasashen Asiya suna bukatar fasahohin kimiyya da fasahohin daidaita harkoki daban daban da kwanciyar hankali na kasashen Turai."
A cikin "Sanarwa game da halin sha'anin kudi da kasashen duniya ke ciki yanzu" da aka zartas a gun taron, an yi kira ga bangarori daban daban da su sauke nauyin da ke bisa wuyansu, kuma su aiwatar da manufofin kudi da na kasafin kudi da na sa ido kan sha'anin kudi da za su zauna bisa halin da ake ciki. A waje daya, an bukaci a daidaita wannan matsalar kudi kamar yadda ya kamata domin tabbatar da cigaban tattalin arziki da kasuwar hada hadar kudi na kowace kasa. Sannan shugabannin kasashen Asiya da Turai sun dauki alkawari cewa, za su dauki matakan da suka wajaba cikin lokaci domin tabbatar da tsarin hada hadar kudi.
Lokacin da ake tinkari matsalar hada hadar kudi ta duniya, gudummowar da kasar Sin take takawa ta jawo hankalin bangarori daban daban. Mr. Danilo Turk, shugaban kasar Slovenia wanda ya halarci wannan taro ya bayyana cewa, "Kasar Sin na daya daga cikin muhimman karfin da ke raya tattalin arzikin duk duniya. Sabo da haka, a ganina, da farko dai a tabbatar da ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. Muddin manufofin da za a dauka suna yin kyakyawan tasiri ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin, za su kuma amfana wa duk duniya. Alal misali, kasashen Turai za su iya samun moriya a kasuwar kasar Sin wadda take ta samun cigaba."
Ko da yake "Sanarwa game da halin sha'anin kudi da kasashen duniya ke ciki yanzu" da aka daddale a gun wannan taron shugabannin kasashen Asiya da Turai ba za ta iya canja halin kasuwanin hada hadar kudi na duniya ba, amma tana da muhimmanci sosai. Madam Chen Fengying wadda ke nazarin tattalin arzikin duniya a cibiyar yin nazarin huldar kasashen duniya ta kasar Sin ta ce, "A ran 15 ga wata mai zuwa, za a yi taron shugabannin kungiya mai kasashe 20, wato G20 kan sha'anin kudi na duniya a Washington na kasar Amurka. Mai yiyuwa ne za a tattauna batun yin gyare-gyare kan tsarin kudi na duniya da matsalar hada hadar kudi da ake fuskanta yanzu a gun wannan taro. Sabo da haka, mai yiyuwa ne wannan taron shugabannin kasashen Asiya da Turai zai yi tasiri ga taron shugabannin kungiya mai kasashe 20 kan batun sha'anin kudi da za a yi." (Sanusi Chen)
|