Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-27 21:12:32    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga hukumar kayayyakin tarihi ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, ya zuwa ran 26 ga watan Agusta, cikin ayyukan binciken kayayyakin tarihin da aka yi a wannan shekara a duk kasar, an gano sabbin wuraren tarihi 739 a jihar Tibet.

An ce, daga watan Maris na wannan shekara, kungiyar masu binciken kayayyakin tarihi ta jihar Tibet ta fara yin bincike cikin gundumomi 12, kuma ta yi rajistar ni'imomin wurare 979 wadanda ba a iya gusar da su ba, daga cikin su kuma da akwai wurare 739 wadanda sababbi ne, kuma mutane masu binciken kayayyakin tarihi sun gano gine-ginen tarihi da kaburburan tarihi da kogunan duwatsu da sassakakkun kayayyakin duwatsu da sauran muhimman wuraren tarihi na zamanin baya-bayan nan da gine-gine masu ma'anar wakilci wadanda yawansu ya wuce 70 a jihar birnin Ali na jihar Tibet.

---- Kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga hukumar kudi ta jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, daga shekarar 2006 zuwa ta 2010, kasar Sin ta riga ta ware kuma za ta ci gaba da ware kudin Sin da yawansu ya kai Yuan miliyan 420 musamman domin ba da kariya ga muhimman wuraren tarihi 21 bisa "hanyar siliki" da ke jihar Xinjiang.

An ce, muhimman ayyukan da za a yi domin kiyaye kayayyakin tarihi bisa hanyar siliki suna gabas da na arewacin kwarin Tarim, da kwarin Turpan da birnin Hetian da na Kashi.

Cikin shekaru 3 da suka wuce, hukamar kudi ta jihar Tibet ta riga ta ware kudin Sin fiye da Yuan miliyan 80 musamman domin ba da kariya da yi gyare-gyare ga ni'imomin wuraren tarihi 19 da ke bisa "hanyar siliki".

Hanyar siliki wata hanyar zirga-zirga ta ciniki ce da marigayi Zhang Qian ya bude yau da shekaru fiye da 2,000 wato lokacin da ya je aikin manzanci a zamanin daular Xihan ta kasar Sin zuwa kananan kasashe 36 da ke bangaren Xiyu, hanyar nan ta tashi daga birnin Xian na lardin Shanxi na yanzu, kuma ta ratsa lardin Gansu da jihar Xinjiang har zuwa nahiyar Asiya ta tsakiya da ta yamma, kuma ta hada kasashe daban-daban da ke kewayen bahar Rum. Kasar Sin ta fitar da kayayyaki daban-daban ta wannan hanya don yin ciniki, amma silikai ne sun fi yawa, shi ya sa ana kiran ta "hanyar siliki".