Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-27 20:05:13    
Sabon hali ya sa kaimi kan Asiya da Turai da su kulla dangantakar abokantaka ta sabon salo

cri

Ran 25 ga wata, a nan Beijing, an rufe taron shugabannin Asiya da Turai a karo na 7. A karkashin babban take na 'yin tattaunawa da hadin gwiwa domin samun nasara tare da kuma moriyar juna', a gun taron, an zartas da takardu da sanarwar yin hadin gwiwa da dama, wannan ya nuna cewa, hali mai sarkakiyya da ake ciki a kasashen duniya ya sanya kasashen Asiya da Turai fuskantar kalubale tare, yanzu suna nan suna kokari wajen zurfafa hadin gwiwa da kuma kulla dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu. Sa'an nan kuma, hadin gwiwa a tsakanin Asiya da Turai zai iya kawo musu da kuma jama'arsu alheri, haka kuma, zai ba da kyakkyawan tasiri kan duniya.

An yi wannan taron koli ne a cikin halin musamman da kasashen duniya suke ciki. Serge Abou, jakadan kungiyar tarayyar Turai a kasar Sin yana ganin cewa, wannan sabon hali ya sanya bangarorin Asiya da Turai su fuskanci kalubale kusan iri daya. Mr. Abou ya ce,"Muna fuskantar dimbin matsaloli kusan iri daya. Nahiyoyin Turai da Asiya suna kan gaba wajen yin amfani da makamashi. Suna kuma fuskantar matsalar kudi da dumamar yanayin duniya da neman kyautata muhalli da kuma samun kwanciyar hankali a harkokin siyasa a gida da sauran kalubale."

Feng Zhongping, shugaban cibiyar nazarin Turai ta kwalejin nazarin dangantaka a tsakanin kasashen duniya a zamanin yanzu na kasar Sin ya nuna cewa,"A shekarun baya da suka wuce, an sami saurin bunkasuwar dinkuwar tattalin arzikin duniya gu daya kuma a matakai daban daban. Asiya da Turai sun kara samun moriya bai daya, suna tinkarar karin kalubale tare. Shi ya sa a hakika suka fi bukatar yin hadin gwiwa da kuma zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu cikin gaggawa."

A ganin Asiya da Turai, matsalar kudi da ke lalacewa a duniya ita ce kalubale mafi tsanani da suke fuskanta. 'Sanarwar taron shugabanni na Asiya da Turai a karo na 7 kan halin da kasashen duniya suke ciki a fannin sha'anin kudi' da aka zartas da ita a gun taron ta nuna imanin da Asiya da Turai suke nunawa wajen yin kokari tare domin tinkarar matsalar kudi ta duniya.

Ban da wannan kuma, a gun taron da suka yi a nan Beijing, mambobin taron shugabanni na Asiya da Turai sun tattauna kan samar da isasshen abinci da yin hadin gwiwa wajen yaki da bala'i da samun bunkasuwa mai dorewa da kuma sauyawar yanayi da yin tattaunawa a tsakanin al'adu iri daban daban, an zartas da 'Sanarwar Beijing kan samun bunkasuwa mai dorewa' da 'Sanarwar shugaba na taron shugabanni na Asiya da Turai a karo na 7' da sauran muhimman takardu da sanarwar yin hadin gwiwa guda 17, wannan ya nuna cewa, Asiya da Turai suna matukar fatan inganta hadin gwiwa a tsakaninsu da jure wahala tare da kuma zurfafa dangantaka a tsakaninsu da kuma kokarin da suke yi.

A matsayin mai bakuncin shirya taron koli na Asiya da Turai a karo na 7, kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummowa wajen samun nasarar shirya taron. Kafin taron, kasar Sin ta yi gyare-gyare kan batutuwan da za a tattauna bisa halin da ake ciki, ta mayar da tattalin arzikin duniya da harkokin kudi a matsayin muhimman batutuwan da za a tattauna. A gun taron, kasar Sin ta gabatar da muhimman ra'ayoyi kan manyan batutuwa. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya jaddada cewa,

"Bisa karfinta, kasar Sin tana bayar da kokari wajen tinkarar wannan matsalar kudi cikin himma, ta dauki jerin muhimman mataka. Bunkasuwar tattalin arzikin da kasar Sin take ci gaba da samu ita ce muhimmiyar gudummowa da kasar Sin take bayarwa wajen zaunar da kasuwannin kudi na duniya da muna raya tattalin arzikin duniya."

Tabbas ne kyakkyawan sakamako da aka samu a gun taron koli na Beijing a watan Oktoba na wannan shekara zai sa kaimi kan kulla dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Asiya da Turai, zai kuma ba da gudummowa wajen shimfida zaman lafiya da samun wadata tare har abada.(Tasallah)