Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-27 14:24:43    
Reshen ofishin MDD da ke Kenya ya ba dan sanda kyauta

cri

Ran 24 ga watan Oktoba na bana, rana ce ta cika shekaru 63 da kafa MDD. Tun daga shekarar 2002, a wannan rana, Hukumar kula da muhalli ta MDD ta UNEP da Hukumar kula da wuraren zama na mutane ta MDD ta UN-HABITAT, su kan yi bikin taya murna a hedikwatocinsu da ke Nairobi babban birnin kasar Kenya, inda za a bayar da kyautar "Mutum na wannan shekara na kasar Kenya" ga mutum wanda ya yi gudummawa sosai don raya zamantakewa da tattalin arziki na kasar Kenya cikin watanni 12 da suka wuce. Kuma kyautar bana, an mika wa wani sufeton dan sanda ita. Shi wannan sufeto sunansa Joseph Musyoka Nthenge.
A wajen bikin taya murna da aka yi, jami'I mai kula da aikin jin kai na MDD Aeneas Chuma ya sanar da cewa, an ba Joseph Nthenge kyautar mutumin shekarar 2008 na kasar Kenya. Bayan wannan, ya mika wa Mista Nthenge takardar shaida, ya taya masa murna. Mista Chuma ya ce,
"Muna farin ciki sosai kan bayar da kyautar bana ga Joseph Musyoka Nthenge,wani babban sufeto na rukunin 'yan sanda na kasar Kenya. Lokacin da ake tashin hankali kan babban zaben da aka shirya a kasar Kenya a farkon shekarar bana, Mista Nthenge ya nuna jarumtakarsa kan hana tarzomar da aka yi, kuma ya lalashi masu zanga-zangar da su daina tunzura wuta da ta da tarzoma. Ya yi gudummawa kan kiyaye zaman kwanciyar hankali a kasar Kenya, "
Har zuwa yanzu, zukatan mutanen kasar Kenya na dar-dar, idan sun tuna da tarzomar da aka yi a farkon shekarar bana. Cikin makonni, mutane fiye da 1500 sun rasa rayukansu, yayin da dubban darurruwa sun yi gudun hijira. A ko ina na birnin Nairobi ana samun shingayen hanya da motocin da ake konewa da masu zanga-zanga da mutanen da ke tsere da rayukansu. Mutane da yawa na boye a gida, suna tsoron fitowa. Cikin wannan hali na rashin doka da oda, wani jarumi ya fito, ya lalashi mutane da su ajiye makamansu, su daina amfani da karfin tuwo. Wannan shi ne Joseph Nthenge.
Ko da yake ya samu wannan kyauta, Mista Nthenge bai yi zumudi sosai ba, abin da ya yi shi ne sauke nauyin a bisa wuyansa kawai. Ya ce,
'Ina jin alfahari da samun kyautar. Bisa matsayina na dan sanda, ina sane da cewar nauyin da ke wuyana shi ne kiyaye farar hula da dukiyoyinsu. Kuma ya karfafa mana karfin zuciya ganin MDD na dora muhimmanci kan amfanin da 'yan sanda suke bayar a wajen kiyaye kwaciyar hankali a zaman al'umma'
Lokacin da Mista Nthenge yake aikinsa na kwantar da kurar da ta tashi, bai dauke da makamai ba. Abin da ya yi shi ne umartar mutanensa da su kawar da shingayen da ke kan hanya. An daina tarzoma sau da yawa a wajen zanga-zangar kin yarda da gwamnati da aka yi sakamakon kokarinsa. A kan samu damar ganinsa cikin shirye-shiryen telibijin, wannan ya sa Nthenge ya yi suna a kewayan kasar Kenya.
An tambaye shi kan hanyar da ya bi ta asiri don lalashin masu zanga-zangar da su daina yin tarzoma. Mista Nthenge ya ce, ba shi da hanyar asiri, sai nuna sahihanci, da yin magana da mutane kan abin da ya kamata a yi shi.
'Na yi hira da su. A ganina, hira hanya ce mafi kyau da ake bi don kwantar da tarzoma. Idan ka yi magana kan abin da ya kamata a yi, kuma an gane nufinka, za su kwantar da makamai.'
Ko da yake an sake samun kwanciyar hankali a Kenya yanzu, Mista Nthenge zai ci gaba da yin kokari don kiyaye zaman karko a kasar.
"Abin da nake so in fada wa 'yan uwanmu na kasar Kenya shi ne, muna da nauyin gina wa mutanen kasar muhalli mai kyau,domin ba wanda yana so ya zama cikin dar-dar na rahin kwanciyar hankali."(Bello Wang)