Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-24 14:55:01    
Sha'anin wasannin Olympics na nakasassu yana samun cigaba da saurin gaske

cri

Aminai 'yan Afrika, kamar yadda kuka san cewa, shekanjiya ne aka gudanar da gagarumin bikin rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing a shekarar 2008. 'Yan wasa nakasassu daga kasashe da yankuna daban-daban na duniya sun yi fafatawa a fannonin wasa iri daban-daban cikin halin aminci. Mista Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa yana fama da aiki, ya taba yin rangadin duba aiki a wuraren gasa daban-daban, inda ya mai da hankali sosai kan ci gaban gasar wasannin nakasassun. Kwanan baya dai, ya yi farin ciki matuka da karbar ziyarar da wakilinmu ya yi masa, inda ya fadi albarkacin bakinsa kan ayyukan share fage da gwamnatin birnin Beijing ta yi ga gasar wasannin Olympics da gasar wasannin Olympics ta nakasassu da kuma kyakkyawan makomar sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu. Ya ce, domin gudanar da gasar wasannin Olympics da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu cikin nasara, gwamnatin birnin Beijing ta yi aiki tukuru wajen raya aikin muhimman gine-gine da kuma bada garanti ga yin tafiye-tafiye ba tare da samun shinge ba. A ganin Mr.Craven, wadannan filaye da dakunan wasannin sun cancanci har sun zarce ma'aunin bukatun kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na kasa da kasa. Yana mai cewa: " Ko shakka babu, wadannan filaye da dakuna sun cimma burin kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na kasa da kasa. Idan ka je kauyen 'yan wasa nakasassu, inda ka yi hira da su ko duba su, to za ka ga dukkansu sun nuna gamsuwa ga gine-gine marasa shinge, da abinci da kuma zirga-zirga. In wani ya gamsu da samun kyakkyawan muhalli, to lallai zai ji dadi ainun lokacin da yake shiga gasa. Ga 'yan kallo masu yawan gaske suna kan dandalin kallon wasanni, inda sukan sa kaimi ga 'yan wasa. Shin ko wannan ba abu ne da muke so ba? Babu tantama, Beijing kuma tare da Qingdao da Hongkong sun yi nasarar gudanar da wannan gagarumar gasa".

Jama'a, shin ko 'yan wasa nakasassu suna iya samun tallafi kamar yadda 'yan wasannin Olympics suke yi ko a'a , wannan dai abu ne dake janyo hankulan mutane. Mista Philip Craven ya bayyana ra'ayinsa cewa, irin salon cigaba da kasashe da dama suke bi a halin yanzu ya cancanci a yi koyi da shi. Mr. Craven ya furta cewa: " Bari in bada misali kan kasar Burtaniya: kafin shekarar 2001, har kullum ina rike da mukamin daraktan sashen kula da harkokin kungiyar wasan kwallon kwando ta nakasasu ta Burtaniya. A ganina, muddin 'yan wasa suka yi namijin kokarin gwada boyayen karfin da suke da shi a gun gasar wasannin Olympics da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu, to 'yan wasannin Olympics da kuma 'yan wasa nakasassu na Olympics dukkansu za su iya samun kudin taimako. A yanzu haka dai, kasashen Ukraine, da Australiya da kuma Canada da dai sauransu haka suke yi. Lallai sha'aninmu na nakasassu yana nan yana samun bunkasa da saurin gaske. Gwamnatoci da 'yan kasuwa masu bada taimako sun soma kallon gasar wasannin Olympics ta nakasassu kamar yadda suke yi ga gasar wasannin Olympics.

Mista Craven ya kara da cewa, wani muhimmin dalili daban da ya kawo ci- gaban wasannin Olympics na nakasassu, shi ne kamfanoni da masana'antu ko mutane masu zaman kansu sukan bada taimakon kudi ga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu. Yana mai cewa: " Wata manufar da muke aiwatarwa a zahiri, ita ce ya zama wajibi a bada gudummowa ga kwamitocin wasannin Olympics na nakasassu na kasashe mambobin kwamitin da kuma hadaddun kungiyoyin wasan motsa jiki guda hudu da aka kafa tun da farko. Mun yi imanin cewa, a yanzu haka ana ta kyautata sharadin gabatarwa a kasuwanni dangane da wasannin motsa jiki na nakasassu, da gasar wasannin Olympics ta nakasassu da kuma kwamitin wasannin Olympics na nakasassu.

A matsayin wani tsohon dan wasan kwallon kwando kan kujera mai tayoyi, a karshe dai, Mista Philip Craven ya bayyana yadda yake ji a cikin zuciyarsa yayin da yake halartar wannan gagarumar gasa. Yana mai cewa:

"Domin halartar gasanni, ka kan nuna himma da kwazo wajen yin horo na tsawon shekaru hudu har na fiye da haka ; Ka zo nan wurin, ka zo kauyen 'yan wasannin nakasassu ; Ga filaye da dakunan wasanni masu kayatarwa ; Ga kyakkyawan yanayin zirga-zirga tare da wani kyakkyawan birni kama haka dake gabanka. Lallai za ka ji dadi ainun tare da nuna gwaninta wajen gasar wasannin.'' (Sani Wang)