Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-23 15:08:42    
Malama Li Guihua, da 'ya'yanta

cri

Garin Sanying yana birnin Guyuan na jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Akwai kantuna daban daban da ke bakin babban titin da ke garin, kantin kayan gado na malama Li Guihua yana daya daga cikinsu. Bayan da wakilinmu ya shiga kanti na Li Guihua, mijinta Yang Mingjun ya nuna wani hoton da ke bango kuma ya yi alfahari cewa,

"Li Guihua ita 'yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 8 ce, tana wakiltar manoma na duk jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta."

A cikin hoton, shugabannin kasar Sin suna yin musafaha tare da Li Guihua. Madam Li Guihua 'yar shekaru 58 ta taba zaman 'yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na takwas, da kuma shugaban majalisar masu masana'antu da 'yan kasuwa na zaman kansu ta jihar Ningxia. Ta taba sa kaimi ga wani aiki na shigar da ruwan da ke rayayen kogi zuwa birnin Guyuan, ta yadda aka warware matsalar rashin ruwan sha na jama'ar wurin.

A matsayinta na 'yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, madam Li Guihua ta fi mayar da hankali kan aikin ba da ilmi, wannan na da nasaba da zaman rayuwarta a zamanin kuruciyarta. Iyalin Li Guihua na fama da talauci sosai, kuma babansa ya mutu a lokacin da shekarunta na haihuwa suka kai kusan 2. Madam Li Guihua ta shedawa wakilinmu cewa, saboda tasirin da ake samu ta fuskar talauci da ra'ayin gargajiya, 'yammatan da ke kauyuka, musamman ma 'yammata na kabilar Hui kadan ne ke iya samun damar shiga makarantu. A lokacin da shekarunta na haihuwa suka kai 11, saboda Li Guihua ta tsaya kan ra'ayinta na shiga makaranta, babu makawa sai iyalinta suka amince da wannan. Li Guihua ta mai da hankali sosai kan wannan damar koyon ilmi mai daraja, ta yi kokari sosai kan karatunta, har ma a karshe dai ta yi amfani da shekaru uku kawai don gama duk darussan firamare na shekaru biyar, bisa maki mai kyau da ta samu an aika da ita zuwa jami'ar horar da malamai ta Guyuan. Madam Li Guihua na ganin cewa, samun ilmi na da muhimmanci sosai, kuma tana adawa da halin ba da ilmi da ake ciki a kauyuka, ta daurar aniyar ta kara matsayin samun ilmi na kabilarta ta fannin ilmin da ta samu. Ta ce,

"Idan yaran da ke kauyuka ba su koyi wasu fannonin ilimi ba, to za su ja da baya sosai. Na taba karatu a jami'ar horar da malamai, lallai ina jin nauyin da ke bisa wuyana, tilas ne zan horar da wasu dalibai mafi nagarta."

A shekaru 60 na karnin da ya wuce, Li Guihua ta gama karatunta a jami'ar horar da malamai ta Guyuan, kuma ta kafa makaranta a wani kauyen da babu malamai da kayayyakin karatu. Ta karbi duk yaran da ke son samun ilmi, kuma ta yi iyakacin kokarinta don ta taimake su. Ba kawai Li Guihua ta ba su ilmi ba, har ma ta yi amfani da kudin da ta samu don sayen littattafai. A cikin wannan makaranta ta irin haka, Li Guihua da wani malami daban sun horar da dalibai na firamare 147 a cikin shekaru hudu.

A lokacin da makarantar Li Guihua ta soma samun cigaba, a waje daya kuma, kasar Sin ta soma gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, haka kuma, aikin ba da ilmi na kauyuka ya samu bunkasuwa sosai. A cikin wannan halin da ake, madam Li Guihua na ganin cewa, lallai ilmin da ta samu bai iya biyan bukatun dalibai. Saboda haka, a shekarar 1980, Li Guihua ta shigar da makarantar da ta kafa cikin wata makarantar firamare mai inganci.

Madam Li Guihua, wadda ta bar makaranta, ta soma mayar da hankalinta kan 'ya'yanta. Ta tsayar da niyyarta ta shigar da 'ya'yanta shida cikin makaranta, har ma su samu ilmi a jami'ai. Niyyarta ta samu goyon baya sosai daga mijinta.

Li Guihua da mijinta sun kafa wani kantin tuffafi a garinsu, don samun kudin karatu ga 'ya'yansu. Ko da ya ke sun sha wahalhalu daban daban, amma 'ya'yansu ba su bar makaranta ba. Ban da wannan kuma, dukkansu sun shiga jami'ai bisa fatansu. 'Yarsu ta biyar Yang Shuying ta ce,

"Mamata ta mai da hankali sosai kan karatunmu, bisa kwarin gwiwar da ta ba mu, dukkanmu mun yi gasar karatu. Gaskiya ne ana iya cewa da ba mu samu goyon baya daga mamanmu ba da ba za mu samu sakamako mai kyau kamar na yanzu ba."

Bisa tasirin da Li Guihua ke kawowa, yawancin 'ya'yanta sun zabi jami'ai na horar da malamai. Bayan haka kuma, a lokacin kusantowar gama karatu a jami'ai, Li Guita ta bukaci 'ya'yanta su aiwatar da aikin ba da ilmi a kauyuka. Li Guihua na ganin cewa,

"Ana rashin kwararru a fannin ba da ilmi a kauyuka, saboda haka, yin aikin ba da ilmi a kauyuka na da ma'ana sosai, kuma ta yadda za a iya kwarewa da su."

Karatu ya canja zaman rayuwar madam Li Guihua, kuma ya canja zaman rayuwar 'ya'yanta, kazalika sauran mutane suna bukatar canja zaman rayuwarsu ta hanyar karatu. Yanzu, 'ya'yan madam Li Guihua sun gane, akwai ma'ana sosai da mamansu ta shigar da su cikin jami'ai, wato samar da damar samun ilmi ga mutane mafi yawa. A shekarar 2002, 'yarta ta biyar Yang Shuying ta gama karatunta a jami'ar horar da malamai ta Yinchuan, kuma ta zama wata malama a wani kauye mai fama da talauci. Yang Shuying ta ce,

"Na fito ne daga kauye, ya kamata na sake komawa kauye, ko da ya ke halin zaman rayuwa na birane na da kyau, amma a ganina, yanzu lokacin saka wa kauyuka ya yi."

Yanzu, 'ya'ya hudu na madam Li Guihua suna aikin ba da ilmi. Kuma Li Guihua ba ta manta da kulawa da aikin ba da ilmi ba, kullum tana cewa,

"Idan da zan iya komawa lokacin tashe na, to, zan zama wata malama, don ba da ilmi."