Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-22 16:34:27    
Kasar Sin ta samun manyan nasarori a cikin shekaru 30 da suka wuce a cewar firaminista Lee Hsien Loong na kasar Singapore

cri

Bisa gayyatar da Mr. Wen Jiabao firaministan kasar Sin ya yi, Mr. Lee Hsien Loong firaministan kasar Singapore ya kawo ziyarar aiki ga kasar Sin tun daga ran 22 zuwa ran 27 ga wannan wata, kuma zai halarci taron koli na kasashen Asiya da Turai na karo na 7. kafin Mr. Lee Hsien Loong ya tashi, ya gana da wakilinmu, yana ganin cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori a cikin shekaru 30 da suka wuce, ya ce,

"Ina ganin cewa, kasar Sin ta samu manyan nasarori. A cikin shekaru 30 da suka wuce, kasar Sin ta fara taka muhimmiyar rawa a wannan yanki, kuma mun kafa huldodi da yawa. ban da fannin tattalin arziki, mutanen kasar Sin sun sami cigaba kan fannin tunani, suna mai da hankali kan canje-canje na duniya, suna kokarin neman bunkasuwa. An riga an kafa manyan gine-gine masu inganci a birane."

Mr. Lee Hsien Loong ya nuna babban yabo ga huldar da ke tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN, da muhimmiyar bunkasuwar kasar Sin cikin lumana. Ya ce,

"Bunkasuwar kasar Sin tana da muhimmanci sosai ga kasashen Asiya da duk duniya. Saboda kasar Sin tana da yawan mutane fiye da biliyan 1.3, wannan ya kai kashi 1 cikin kashi hudu na yawan mutanen duniya. Bunkasuwar kasar Sin da huldar da ke tsakaninta da kasashen duniya suna samar da moriya ga kowa da kowa. Ina ganin cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa cikin harkokin duniya, kamar yadda tsohon firaminista Blair na kasar Birtaniya ya ce bayan an kammala wasannin Olympic na Beijing, idan babu hulartar kasar Sin, ba za a iya samun nasara kan ko wane abu a cikin karni na 21. Kamar shawarwarin ciniki na Doha, da shawarwarin yarjejeniyar sauyawar yanani ta Majalisar dinkin duniya, da batun yarjejeniyar rashin habaka makaman nukiliya da matsalar nukiliya ta kasar Korea ta arewa, dukkansu suna bukatar kasar Sin"

Game da yarjejeniyar ciniki ba tare da shinge ba da kasashen Sin da Singapore za su kulla, Mr. Lee Hsien Loong ya nuna cewa,

"Ina jin dadi sosai saboda za a daddale wannan yarjejeniya. Wannan zai zama wani muhimmin al'amari wajen bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu."

Ban da haka kuma, za a bude taron koli na kasashen Asiya da Turai lokacin da ake fuskantar rikicin hada-hadar kudi na duniya, Mr. Lee Hsien Loong ya ce,

"Rikicin hada-hadar kudi zai zama wani muhimmin abin da za mu tattauna. Kasashe daban daban sun dauki matakai domin kwaucewa matsala, a ganina, wannan rikici yana da mummunan tasiri ga kasashen Asiya suna, ciki har da kasashen Sin da India. Saboda haka, yadda za a dauki matakai domin kawar da tabarbarewar tattalin arziki yana da muhimmanci sosai."

Game da babban take na "yin shawarwari da hadin gwiwa, tare da moriyar juna" na taron koli na wannan karo. Mr. Lee Hsien Loong ya ce,

"Wasu kalubali sun shafi duk duniya, kamar rikicin hada-hadar kudi, da tabarbarewar tattalin arziki, da shawarwarin yarjejeniyar ciniki, da shawarwarin sauyawar yanayi. Ko da yake ana yin wasu shawarwari, amma da wuya za a iya samun matsaya daya. Amma muna iya yin hadin gwiwa kan wasu fannoni a zahiri, kamar fannonin al'adu, da ba da ilmi, da kimmiya da fasaha."