Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-22 15:20:39    
Bikin bude wasannin Olimpic na Beijing ya bayyana wayewar kasar Sin da ke da zurfaffiyar ma'ana da kuma kunshe da abubuwa mafi yawa

cri

Kwanan baya, bisa gayyatar da gidan rediyon kasar Sin ya yi masa, babban manajan kamfanin watsa labaru na kasar Kenya Mr David Waweru ya zuwa nan birnin Beijing don halartar bikin bude wasannin Olimpic, lokacin da ya karbi ziyarar da wakilin gidan rediyon kasar Sin ya yi masa, ya bayyana cewa, bikin shi ne abun mamaki da aka kawo mana, kuma wasanni ne da aka yi na hada shahararrun al'adu na zamani aru aru da kimiyya da fasaha na zamanin yau na kasar Sin. Ba za mu manta da shi ba har duk rayuwarmu.

A shekarar 2005, bisa babban taimakon da kamfanin watsa labaru na Kasar Kenya ya yi, gidan rediyon kasar Sin ya kafa tasharsa ta FM ta farko da ke kasashen waje a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. Mutane miliyan 2 na birnin Nairobi sun iya samun alamar tashar, a kowace rana, ana watsa labaru cikin sa'o'i 19 ta hanyar yin amfani da harsunan Ingilish da Sinanci da Siwahili a tashar. Kyakkyawar dangantakar da gidan rediyon kasar Sin da kamfanin watsa labaru na kasar Kenya suka kulla a tsakaninsu ta zama abun misali ga yin hadin guiwa da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu. A ranar 8 ga watan Augusta, bisa matsayinsa na babban bakon da gidan rediyon kasar Sin ya yi masa, babban shugaban kamfanin watsa labaru na kasar Kenya ya halarci bikin bude wasannin Olimpic na Beijing, ya bayyana cewa, ba kowane mutum ne ke iya samun damar kallon bikin bude wasannin Olimpic kai tsaye ba, wannan ne karo na farko da na sami damar shiga aikin nan a duk rayuwata, game da wannan, na yi farin ciki da alfahari sosai .

Mr Waweru ya bayyana cewa, a birnin Beijing a ko'ina, ina ganin tutar da ke da alamar zobe biyar da tutar wasannin Olimpic na Beijing da suke karkadawa a babban tituna da kananan unguwoyi. Takardun yin farfaganda kan wasannin Olimpic da zane-zanen da aka yi don bayyana 'yan wasan motsa jiki na kasashe daban daban, sa'anan kuma ya ce ya ga wasu kananan motocin da ke sanya tutar kasar Sin da tutar wasannin Olimpic da suka yi zirga-zirga a birnin, dukkan wadannan da ya ji ya gani sun bayyana farin ciki da himmar da wasannin Olimpic suka kawo wa birnin Beijing, ya bayyana cewa, muna kan mai da hankulanmu a kan aikin share fagen da birnin Beijing ya yi domin wasannin Olimpic, duk saboda hadin guiwa mai kyau da muke yi da gidan rediyon kasar Sin. Ba sau daya ba ba sau biyu ba na kai ziyara a kasar Sin, amma a wannan gami, na gano cewa, birnin Beijing ya sami manyan sauye-sauye, birnin na da tsabta sosai, kowane mutum yana murmushi domin wasannin Olimpic.

amon gangunan gargajiya na kasar Sin da 'yan wasan da yawansu ya kai 2008 suka buga tare da fasahar nuna sauti da haske ta zamani a gun bikin bude wasannin Olimpic don bayyana lokacin karshen da zai yi don bude bikin, ya jawo hankulan dukkan 'yan kallo, Mr Waweru shi ma hakan ya yi. Ya bayyana cewa, bikin ya hada tsabi'un gargajiya da fasahar zamanin yau, ya sa mutane su ji mamaki sosai, filin wasan motsa jiki ya cika da mutane , aminanmu na kasar Sin sun yi farin ciki sosai da sosai, kuma sun yi tafi raf rafi da sowar farin ciki ba tare da katsewa ba, kai, abin da na ji na gani mafi kyau ne sosai. Kodayake kasar Sin da kasar Kenya suna da nisa sosai a tsakaninsu, kuma suna da bambancin al'adu, amma Mr Waweru ya ji al'adun kasar Sin da ke kunshe da abubuwa masu yawa sosai daga cikin wasannin da aka nuna a gun bikin, ya ce, wasannin da aka yi a gun bikin, abun mamaki ne, suna cike da abubuwan da aka kago cikin hazikanci, a cikin wasannin da aka nuna, mun more idonmu kyawawan tufaffi da saurarar kide-kide da wake-wake masu dadin ji, kasar Sin ta bayyana wa duk duniya al'adunta mai wadata.

A gun bikin, a karo na farko ne Mr Waweru da idonsa ya ga 'yan wasan kasarsa da suka shiga babban filin wasan motsa jiki na wasannin Olimpic, ya burge sosai da cewa, da ka saurari sunan kasarka a cikin filin wasan motsa jiki, ko shakka babu ka ji burgewa da farin ciki daga zuciyarka. A lokacin, na tashi na jinjina hannuna ga 'yan wasan kasarmu tare da karkada tutar kasarmu, sai na ji ma'ana mai muhimmanci da ni kaina na shiga wurin yin bikin bude wasannin Olimpic, ba ka iya jin hakan nan ta hanyar kallon TV ba, na yi farin ciki sosai da sosai.

Kasar Kenya babbar kasa ce mai yin wasan motsa jiki a Afrika, musamman ma tana da karfi sosai wajen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, , Mr Waweru ya bayyana cewa, kasar Kenya tana da karfi sosai wajen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, mun sa ran cim ma burinmu na samun lambobi a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

Mr waweru ya kara mai ga 'yan wasan motsa jiki na kasarsa, a sa'I daya kuma ya bayyana cewa, ko shakka babu 'yan wasan motsa jiki na kasar Sin za su sami lambobi da yawa a gun gassanin da ake yi a gun wasannin Olimpic na Beijing. Ya bayyana cewa, muna sa ran alheri ga 'yan wasan motsa jiki na kasar Sin wajen samun lambobi, kuma ina fatan 'yan wasan kasar Sin za su sami sa'a .(Halima)