Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 15:14:40    
Masana'antun lardin Jilin na kasar Sin sun mai da hankali kan zuba jari a Afirka

cri
A kwanan baya, an rufe bikin baje koli da zuba jari a yankuna masu arewa maso gabashin Asiya a karo na 4 a birnin Changchun, hedkwatar lardin Jilin na kasar Sin. Lokacin da ake shirya wannan biki, an kuma shirya wani taron tattaunawa da ke da take "Shigar masana'antun lardin Jilin a kasashen Afirka, wato damar zuba jari a Afirka da hanyoyin hada-hadar kudi". Hukumomin gwamnatin lardin Jilin da wakilan wasu masana'antu da jakadun kasashen Afirka da ke nan kasar Sin sun halarci wannan taro. Wakilinmu ya samu labari daga wannan taron tattaunawa, cewar yanzu masana'antun lardin Jilin sun mai da hankalinsu sosai kan damar zuba jari da neman cigaba a Afirka, kuma yanzu suna kokarin neman kasuwanci a Afirka.

Lardin Jilin tsohon sansanin masana'antu ne da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kuma lardi ne da ke raya aikin gona kwarai. Wannan lardin da ke da wadataccen albarkatun halitta shi ne wani kyakkyawan sansanin masana'antu. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, wasu masana'antun lardin Jilin sun soma neman damar kasuwanci a Afirka. Sabo da haka, wannan taron "Shigar da masana'antun lardin Jilin a kasashen Afirka, wato damar zuba jari a Afirka da hanyoyin hada-hadar kudi" da aka kira cikin lokaci zai amfana wa masana'antun lardin wajen sani da fahimtar kasashen Afirka, kuma za su iya zuba jarinsu bisa halin da suke ciki. Mr. Wang Gang, direktan ofishin kula da harkokin waje a gwamnatin lardin Jilin, ya ce, "A taki na farko ne masana'antun lardin Jilin suka soma shiga kasashen Afirka. Sabo da haka, mun kira wannan taron tattaunawa na 'Shigar da masana'antun lardin Jilin a kasashen Afirka, wato damar zuba jari a Afirka da hanyoyin hada-hadar kudi domin muna son samar wa masana'antun lardin Jilin ilmi na shigar da su a Afirka."

An labarta cewa, bayan shekara ta 2001, matsakaiicin karuwar cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai fiye da kashi 30 daga kashi dari. A shekara ta 2005, kasar Sin ta riga ta zama abokiyar cinikayya ta kasashen Afirka a matsayi na 3. Ya zuwa yanzu, lardin Jilin ya riga ya kafa masana'antu 19 a Afirka, yawan jarin da suka zuba a Afirka ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 4. Daga cikinsu, kamfanin sufurin wutar lantarki na Jilin yana samar da muhimman ayyukan sufurin wutar lantarki a kasashen Sudan da Habasha da Equatoria Guinea da Nijeriya. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, wannan kamfani ya samu kwangiloli da yawa a Afirka. A shekara ta 2007 kawia, jimlar yawan kudin kwagilolin da wannan kamfani ya samu a kasashen Afirka 4 ta kai fiye da kudin Renminbi yuan miliyan dari 9. Mr. Zhang Bin, shugaban kamfanin sufurin wutar lantarki na Jilin ya sa fatan alheri sosai kan kasuwar Afirka. Ya ce, "Bisa halin da ake ciki yanzu, ina tsammani, makomar kasuwannin Afirka tana da kyau sosai. Haka kuma a gare mu, muna da wata kyakkyawar damar neman cigaba, musamman kasashen Afirka ba su da kyawawan ayyukan yau da kullum na wutar lantarki. Saboda haka, ina tsammani muna da kyakkyawar damar neman cigaba a Afirka."

Bisa kididdigar da hukumar kasuwanci ta lardin Jilin ta yi, an ce, a cikin farkon watanni 7 da suka gabata, yawan darajar kayayyakin da aka fitar da su zuwa kasashen Afirka daga lardin Jilin ya kai dalar Amurka miliyan dari 1, wato ya karu da kashi 46 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen Afirka daga lardin Jilin sun hada da motoci da kayan gyara na motoci da magunguna da injunan asibiti da tufafi da dai makamatansu. Masana'antun lardin Jilin suna kuma shigo da wasu ma'adinan halittu daga kasashen Afirka. A waje daya kuma, masana'antun lardin Jilin na kasar Sin suna kokarin neman samun kwangilolin samar da ayyukan yau da kullum a Afirka. Alal misali, sun gina manyan gadoji da shimfida layin sufurin wutar lantarki da ayyukan samar da wutar lantarki a kasashen Sudan da Habasha.

Sabo da masu zuba jari na kasar Sin suna kokari, kuma su kan sauke nauyin da ke bisa wuyansu, har suna mai da hankulansu sosai kan abubuwan da suke yi kamar yadda ake fata, su kan samu yabo a kasashen Afirka. Kasashen Afirka da yawa suna maraba da su dan zuba jari a kasashensu. Mr. Haile Kiros Gessesse, jakadan kasar Habasha a nan kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, makadashin ziyararsa a wannan biki shi ne yana son jawo wa masana'antun yankunan arewacin kasar Sin da su zuba jari a kasar Habasha. Mr. Haile Kiros ya ce, "Yawan masana'antun kasar Sin da ke zuba jari a kasashen Afirka yana ta karuwa, musamman yawan jarin da suke zubawa a kasar Habasha ya yi yawa sabo da kasar Habasha tana da zirga-zirga mai sauki. A kowane mako, yawan zirga-zirgar jiragen sama da ake yi a tsakanin Habasha da kasar Sin yana da yawa. Masu zuba jari na kasar Sin suna mai da hankulansu kan aikinsu. Yanzu galibinsu suna zuba jari a sana'o'in sarrafawa da hakar ma'adinai a kasar Habasha. Kasar Habasha tana da wadatattun albarkatun halitta da sana'ar jima. A waje daya kuma, yawan dabobbin gida da ake kiwo a kasar Habasha ya kai miliyan 40, wato yana kan gaba a duk fadin kasashen Afirka, kuma yana matsayi na 10 a duk fadin duniya. Gwamnatinmu ta bayar da manufofi masu karanci. Sabo da haka, wannan wata kyakkyawar dama ce ta neman cigaba."

Bugu da kari kuma, lardin Jilin yana hadin guiwa da kasashen Afirka a fannin aikin gona. Bisa shirin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta tsara, cibiyar zayyana kayayyakin yau da kullum ta lardin Jilin tana sauke nauyin horar da kwararrun aikin gona na kasashe masu tasowa da ke bisa wuyanta. Ya zuwa yanzu, wannan cibiya ta riga ta shirya kwas din har sau 8, yawan mutanen Afirka da suka halarci irin wannan kwas ya kai fiye da 200. Mr. Wang Gang, direktan ofishin kula da harkokin waje na lardin Jilin ya ce, "Lardin Jilin yana da kwarewa sosai wajen aikin gona, yana noman masara da sarrafa masara a kullum. Hatsi yana da muhimmanci sosai ga kowace kasa mai tasowa, ciki har da kasar Sin. Kuma yanzu kasashen Afirka da yawa ba su iya samun cigaban tattalin arziki da samun kwanciyar hankali sakamakon matsalar karancin hatsi da abinci. Sabo da haka, ya kamata masana'antun lardin Jilin su sanya aikin yin hadin guiwa a tsakaninsu da kasashen Afirka a wani muhimmin matsayi."

Bugu da kari kuma, lardin Jilin ya tsara wasu manufofi domin sa kaimi kan masana'antunsa da su zuba jari a kasashen Afirka. Bisa manufofin da wannan lardi ya bayar, masana'antun da suke zuba jari a ketare za su iya neman kudin tallafawa domin bude kasuwarsu a ketare. Wang Gang ya ce, "Bisa kididdigar da muka yi, yawan mutanen da suka halarci wannan biki ya yi yawa fiye da kima. Masana'antunmu, musamman masana'antu da kamfanoni masu zaman kansu suna sha'awar neman cigaba a kasashen Afirka. Gwamnatin lardin Jilin za ta tallafawa masana'antu da kamfanonin da suke da shirin shiga kasashen Afirka a fannonin rancen kudi."

Ya zuwa yanzu an riga an kulla "yarjejeniyar kiyaye zuba jari" a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka 29. Kuma an kulla "yarjejeniyar magance buga haraji sau biyu" a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka 9. Wadannan yarjejeniyoyi sun kafa kyawawan sharuda ga kamfanoni da masana'antun da suke da shirin zuba jari. Hukumar kasuwanci ta lardin Jilin ta bayyana cewa, ba ma kawai lardin Jilin yana sa kaimi kan masana'antu da kamfanoni na lardin da su zuba jari da bude kasuwa a Afirka ba, har ma yana maraba da kamfanoni da masana'antu na kasashen Afirka da su yi hadin guiwa irin ta moriyar juna a tsakaninsu da na lardin Jilin.  (Sanusi Chen)