---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bisa kulawa da tallafin da gwamnatin Sin ta yi mata ne, jihar Tibet ta sami babban ci gaba wajen yin magungunan Tibet. Masana'antun yin magungunan Tibet sun samu bunkasuwa daga dakunan sana'ar hannu na farkon lokaci zuwa manyan masana'antu, aikin yin magungunan Tibet ya fara kama hanyar samun bunkasuwa bisa manufar babban sikeli da ma'auni mai kyau.
Ofishin kula da magungunan Tibet na hukumar kiwon lafiya ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, yanzu yawan masana'antun yin magungunan Tibet da ke jihar Tibet ya karu har zuwa 18, kuma dukkansu sun kai ma'aunin da gwamnatin kasar Sin ta tsayar wajen aikin yin magungunan Tibet, yawan ma'aikatan da suke dukufa kan wannan aiki ya wuce 1,400, yawan samfurorin magungunan Tibet da ake fitarwa ya wuce 360.
Bisa budewar hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet, tsarin sayar da magungunan Tibet ya yi ta samun yaduwa, kwararru da kungiyoyi masu sayar da magungunan Tibet suna ko'ina a kasar Sin, har ma ana sayar da wasu magunguna zuwa kasashen waje. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet takan zubar da kudin Sin fiye da Yuan miliyan 200 a kowace shekara don yin kokarin shugabantar masana'antu masu yin magungunan Tebet da su yi gyare-gyare domin kyautata fasahar yin magungunan Tibet na gargajiya. A shekarar da muke ciki kuma za a fara aikin gina muhimmin wurin yin magungunan Tibet na farko na jihar Tibet.
---- Kwanan baya, jihar Tibet ta kasar Sin ta tsai da cewa, za ta mai da aikin raya yankunan masana'antu a matsayin muhimman yankuna wajen bunkasa masana'antu, ya zuwa karshen shekarar 2009, za a ware kudin Sin kusan Yuan biliyan 3.5 domin raya yankunan masana'antu 5.
An ce, daga cikin wadannan yankunan masana'antu 5 har da wani budadden yanki bisa matakin kasa wato budadden yankin tattalin arziki da fasaha na Lhasa, da yankunan masana'antu guda 4 bisa matakin gunduma. Jihar Tibet za ta ba da taimako wajen kudi da manufa domin aiwatar da muhimman gine-gine, da neman kulla kwangiloli da kamfanonin Sin da na kasashen waje domin samun kudi, da sauran ayyukan da za a yi domin gina wadannan yankunan masana'antu. An ce, ya zuwa karshen shekarar 2007, an riga an ware kudin Sin fiye da Yuan biliyan 1.1 domin raya wadannan yankunan masana'antu.
|