Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-20 14:17:18    
Mahayiya Liu Lina da ke filin gasar wasannin Olimpic

cri

A shekarar 2002 kuma, budurwa Liu ta je kasar Denmark, a can ne ta fara tattba wasa da yin gasanni cikin dogon lokaci. Bayan da ta tashi daga barci wajen karfe 7 na kowace rana da safe, takan shafe awa daya tana share barga, da wanke dawaki, bayan cin abincin safe kuma ta fara tattaba wasa, takan shafe awoyi 10 a kalla tana yin wasa a bayan doki a kowace rana. Bayan haka kuma ta yi wa dokin wanka, ba ta koma dakinta don yin barci ba sai gari ya yi duhu, da haka ne ta yi zamanta har shekaru da yawa.

A shekarar 2003, budurwa Liu Lina ta fara shiga gasar wasannin dawaki tsakanin kasa da kasa, da gasar tace gwanayen da za su shiga gasar wasannin Olimpic, amma abin bakin ciki shi ne ba ta samu nasara a gun gasar ba, wato ba ta saamu iznin shiga gasar wasannin Olimpic ta Athens ba. Ta ce,

"A wancan lokaci ba ni da doki na kaina, sai na ari wani doki daga wajen malamin koyarwa na kasar Denmark, kuma na shafe kwanaki 3 kawai ina tattaba wasa da wannan doki, ban shirya sosai ba ko kusa, kuma ban samu jituwa a tsakanina da wannan doki ba, sabo da haka rawar da na taka a gun gasar ba ta yi kyau sosai ba."


1 2 3 4