Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-14 16:56:45    
Jihar Ningxia ta kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen shawo kan kwararowar hamada

cri

Ban da daukar wadannan matakai, jihar Ningxia tana dora muhimmanci kan hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen shawo kan kwararowar hamada. Gundumar Yanchi ta samu fa'ida daga wadannan ayyukan hadin gwiwa. A 'yan shekarun nan da suka gabata, daya bayan daya ne kasashen Japan da Jamus suka samar da kudaden kyauta wajen dasa bishiyoyi a gundumar, ta haka muhallin wurin ya samu kyautatuwa a bayyane. Liu Weize, mataimakin shugaban hukumar kula da bishiyoyi ta gundumar Yanchi ya bayyana cewa,

"Muhallin halittu na gundumarmu ya samu kyautatuwa sosai bisa taimakon da kasashen waje suka bayar. Ba kawai kasashen waje sun samar da kudade gare mu ba, har ma sun ba mu fasahohi da sakamako mai kyau wajen fama da kwararowawr hamada. Sabo da haka muna da imani sosai wajen gudanar da wannan aiki."

Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, yanzu an riga an hana kwararowar hamada a jihar Ningxia, kuma muhallin halittu ya samu kyautatuwa sannu a hankali. Wang Junzhong, wani jami'i na ofishin kula da kwararowa hamada na hukumar kula da bishiyoyi ta kasar Sin ya bayyana cewa,

"A shekara ta 2003, na taba zuwa jihar Ningxia don yin bincike kan wasu ayyukan shawo kan kwararowar hamada. Ko da yake an samu wasu sakamako mai kyau, amma ana iya ganin hamada da ke iya motsi. Ta ayyukan da aka gudanar a cikin shekaru 5 da suka gabata kawai, yanzu fadin wurin da aka dasa bishiyoyi ya karu zuwa wajen kashi 60 zuwa 70 cikin dari, kuma ba za a iya ganin hamada da ke iya motsi ba. Ta haka ana iya gano cewa, an samu sakamako mai matukar kyau wajen shawo kan kwararowar hamada, kuma na ji mamaki sosai."


1 2