Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-14 16:54:02    
Fadar Wanshougong

cri

A cikin babban dutse na Xishan da ke gundumar Xinjian ta birnin Nanchang na lardin Jiangxi, yana kasancewa da wata fada mai suna Wanshougong, wadda ta yi suna ne sosai a matsayin gidan ibada na addinin Taoism. Ma'anar Wanshou a Sinanci ita ce tsawon rai. Xu Xun, dan birnin Nanchang, shi ne wani adalin gwamna mai gaskiya na gundumar Jingyang ta lardin Sichuan a zamanin daular Dong Jin (wato daga shekara ta 317 zuwa ta 420 bayan haihuwar Annabi Isa A.S.), ya sadaukar da ransa wajen mulkin gundumarsa yadda ya kamata. Ya taba zuwa nan don kyautata kansa da kuma samar da magani.

An gina gidan ibada na addinin Taosim don tunawa da Xu Xun. An yi masa kwaskwarima da kuma fadada shi a zamanin daular Nanbei, an kuma canja sunansa zuwa Youwei a lokacin nan. A shekara ta 1010 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., wato a zamanin daular Song, an raya shi zuwa wata fada. Sarki Zhenzong na daular Song ya rubuta kalmomi 'Yu Long' domin wannan fada, ya kuma umurci a kera wani allo tare da wadannan kalmomi a kansa. Daga baya kuma, sarki Huizong na daular Song ya ba da umurnin sake yi masa kwaskwarima bisa yadda fadar Chongfu ta birnin Luoyang take, ya kuma rubuta kalmomi 'fadar Yu Long Wanshougong'. Sa'an nan kuma, ya umurci a kera wani allo tare da wadannan kalmomi 'fadar Yu Long Wanshougong'a kansa. An gina manyan dakuna na gaba 3 da kuma na tsakiya 3, da kuma na baya 3 da dakali guda da kuma wani katon kofa a lokacin da ake yin mata gyare-gyare a shekara ta 1867.

A cikin wannan fada, yana kasancewa da tsoffin itatuwan cypress 3 da aka dasa a zamanin daular Jin. Akwai almarar cewa, Xu Xun ne shi kansa ya dasa daya daga cikinsu. Ban da wannan kuma, itatuwan cypress da aka dasa a zamanin daular Tang da ta Song da ta Ming suna ci gaba da rayuwa.