Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-13 16:24:43    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Ya zuwa yanzu, an riga an ware kudin Sin Yuan miliyan 280 don yin gyare-gyare ga manyan kayayyakin tarihi wato gidajen ibada guda 3 wato fadar Potala da Norbu Lingka da kuma ibadan Sakya na jihar Tibet, wadanda da ma an ce jimlar kudin da za a ware don yi musu gyare-gyare ta kai Yuan miliyan 330.

Wakilinmu ya samu wannan labari ne daga wajen taron tattaunawa da aka shirya kwanan baya, wato lokacin da kungiyar bincike na hukumar kayayyakin kasar Sin ta je jihar Tibet don duba ayyukan gyare-gyare ga wadannan manyan wuraren ibada 3.

An fara aikin kiyayewa da yin gyare-gyare ga wadannan manyan ibada guda 3 na jihar Tibet daga watan Yuni na shekarar 2002 a hukunce, dukkan kudaden da aka ware domin wannan aiki sun zo ne daga wajen baitulmalin gwamnatin tsakiya na kasar Sin.

---- Daga ran 20 ga watan Oktoba na wannan shekara, sassan yawon shakatawa na jihar Tibet za su sayar da kayayyakin yawon shakatawa masu araha na yanayin hunturu a birnin Lhasa da na Linzhi da sauran ni'imomin wuraren da masu yawon shakatawa ke sha'awar gani, matsakaicin farashin wadannan kayayyaki ya rugu da kashi 50 cikin 100 bisa na kayayyakin yanayin zafi.

Mr. Wang Songping, mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya gaya wa wakilinmu cewa, a yanayin hunturu na wannan shekarar da muke ciki, jihar Tibet za ta kyautata ayyukan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama, da kamfanonin yawon shakatawa da hotel-hotel da sauran sassan da suka shafi yawon shakatawa, kuma za ta sayar da kayayyaki da yawa masu araha na yawon shakatawa na yanayin hunturu, ciki har da kayayyakin da suka shafi tafiye-tafiye da yin kwana da yawon shakatawa. Ban da wannan kuma kamfanin zirga- zirgar jiragen sama na kasar Sin zai rage kudin tikitin jirgin sama da kashi 50 bisa 100, kamfanonin yawon shakatawa da hotel-hotel kuma za su ba da taimako ga wannan aiki, ta yadda za a sa yawan farashin kayayyakin zai ragu da kashi 50 bisa 100.An ce, za a sayar da kayayyakin yawon shakatawa masu araha na yanayin hunturu musamman a birnin Lhasa da na Linzhi da sauran ni'imomin wuraren da masu yawon shakatawa ke kishin zuwa.