Tun daga ranar 9 zuwa ta 12 ga wannan wata ne, aka gudanar da cikakken taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin. Kamar dai yadda aka tsinkaya, gyare-gyare kan kauyuka ya zama babban batun da aka tattauna a gun taron. Taron ya gabatar da burin da za a cimmawa a wajen gyare-gyaren kauyuka zuwa shekarar 2020, ciki har da kafa tsarin dunkulewar tattalin arziki da zaman al'umma na birane da kauyuka da tabbatar da samar da isassun abinci da amfanin gona a kasar da kara kudin shiga na hakika ga manoma da dai sauransu.
Yau da shekaru 30 da suka wuce, daga kauyukanta ne Sin ta fara gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. Amma a cikin 'yan shekarun baya, kauyukan kasar Sin sun samu koma baya a fannin bunkasuwa idan an kwatanta su da biranen kasar. Don gaggauta bunkasuwar kauyuka, taron ya tsara shirye-shirye daga fannoni uku, ciki har da inganta tsarin kauyuka da raya kauyuka na zamani da kuma gaggauta bunkasa harkokin jin dadin jama'a a kauyuka.
Mr.Xu Xiaoqing, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin bunkasa kauyuka na cibiyar nazarin harkokin bunkasuwa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, tabbatar da dunkulewar tattalin arziki da zaman al'umma na birane da kauyuka na da muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Sin baki daya, ya ce,"kasarmu ba ta kammala aikin bunkasa masana'antu da birane na zamani ba, kuma kauyuka muhimmin tushenmu ne, sabo da yawancin jama'armu na zaune a kauyuka, tare da bambancin da muka samu a tsakanin kauyuka da birane, a cikin irin wannan hali ne, taron ya yanke wannan shawara dangane da ingiza gyare-gyare a kauyuka, wannan lokaci ne mai kyau."
Don kawar da bambancin da ke tsakanin birane da kauyuka, taron ya kuma yanke shawarar kara ware kudade ga kauyuka, da kara inganta ayyukan kiwon lafiya da ba da ilmi da al'adu da kyautata muhallin zama a kauyuka.
Ta fannin bunkasa aikin gona na zamani, taron ya kuma jaddada muhimmanci kan inganta ayyukan gona da tabbatar da samun isassun abinci da muhimman amfanin gona da gaggauta sauya hanyar bunkasa ayyukan gona da inganta kirkire-kirkiren fasahohin noma da raya manyan ayyuka.
Ban da wannan, taron ya kuma gabatar da cewa, ya zuwa shekara ta 2020, kamata ya yi a kara kudin shiga na hakika ga manoma da ninki daya bisa na shekarar 2008 da muke ciki, a kara karfinsu wajen sayayya, kuma a kawar da talauci. Madam Li Jing, mataimakiyar manazarci a sashen nazarin bunkasuwar kauyuka na cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin, tana ganin cewa, ta hanyar daukar wasu matakai na yin gyare-gyare, ba shakka, za a iya cimma wannan buri a shekarar 2020. Ta ce, "Idan aka tabbatar da farashi daya ga filaye, da kuma farashi daya ga filayen gonaki na manoma da kuma filayen birane, to, za a kara kudin shiga ga manoma a fannin kadarorinsu ke nan. Sa'an nan kuma, ya kamata a kara albashi ga manoma 'yan kwadago, wato manoma 'yan kwadago su zama cikin daidaici da ma'aikata na birane, to, za a iya kara kudin shigarsu sosai. Sa'an nan, a kara farashin amfanin gona, idan an kara farashin sayen amfanin gona, to, za a iya kara kudaden shiga ga manoma sosai, kuma ya zuwa shekarar 2020, za a iya cimma burin kara kudin shiga na manoma da ninki daya."
Masana suna ganin cewa, a yayin da aka samu faduwar tattalin arzikin duniya, idan kauyukan kasar Sin sun iya gaggauta bunkasuwarsu, kuma kudaden shiga sun karu sosai ga manoma, to, abin zai taimaka wajen sauya hanyar samun cigaban tattalin arzikin kasar Sin daga dogara ga fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje zuwa sayayya, wanda kuma zai kawo tasiri sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na kasar Sin cikin dogon lokaci.(Lubabatu)
|