Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-09 15:39:40    
Ma'aikata masu sa kai a wurin gasar wasanni ta Olympics a birnin Beijing

cri

A cibiyar ba da hidima da harsuna da kwamitin wasannin Olympics na Beijing ya kafa da akwai ma'aikata daruruwa masu sa kai wadanda suke iya harsunan waje da su ba da taimako ga baki cikin Turanci da Faransanci da Larabci da sauran harsuna sama da goma.Liu Qing yana daya daga cikin ma'aikata masu sa kai da ke iya Japananci, shi dalibi ne mai nazarin harshen Japananci yana neman samun master digiri a aji na biyu na jami'ar koyon harsunan waje ta birnin Beijing. Da karfe takwas daidai ya shiga ofishinsa ya bude akwatin inji mai kwakwalwa ya fara aiki.Babu wayoyi da dama da ya fara aiki,shi ya say a samu damar yin hira da wakilin gidan rediyo na kasar Sin. Y ace A ganina aikin sa kai yana da muhimmiyar ma'ana. Bayan ka samu aikin yi,ba ka iya samun sararin yin lokacin yin aikin sa kai ba, ban da wannan kuma yin wasannin Olympics a kasar Sin ba al'amari ba ne da aka samu cikin sauki cikin shekaru masu yawa. Domin aikin sa kai,Liu Qing ya yi watsi da shirinsa na da na komawa gidan mahaifinsa da taruwa da iyayensu a lardin Shandong.Liu Qing ya ci gaba da cewa " ba na kan koma gidan mahaifina ba sai lokacin hutu na hunturu da na zafi,domin ni dalibi ne.Tun bayan bikin murnar sabuwar shekara har zuwa yanzu ban koma gida ba, iyalina yana tunar da ni,ban koma gida ba sabo da aikin sa kai. In babu wasannin Olympic a Beijing,tabban ne na koma gida na yi haduwa da 'yan iyalina mun yi wasa tare. Amma ba abin baki ciki ba ne in samu damar yin aikin sa kai a wasannin Olympics na birnin Beijing.

Tun daga watan Afril na bana ne, liu Qing ya mika takardar neman zama mai sa kai a wasannin Olympics na Beijing,daga baya burinsa ya cika. A watan Yuli ya samu horo a fanning tunani da da'a da kuma fasahohin fassarawa da ake bukata a cikin aikin sa kai,ya zama wani cikakken mai aikin sa kai. A ran 24 ga watan Yuli ne ya fara aiki a gurbinsa.Liu Qing ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu abin day a ji a zuciyarsa yayin day a fara aiki a matsayin mai sa kai." Na yi farin ciki kwarai da gasket da samu wannan aiki. Da aka takalo batun masu sa kai,ko aminana ko iyalina dukkansu sun yi alfahari da ganin na samu wannan aiki.

yayin da Liu Qing ke hira da wakilin gidan rediyo na kasar Sin,sai wayar dake cikin ofishinsa ta yi kararrawa.wani dan kasar Japan da ya zo nan birnin Beijing domin kallon wasannin Olympics ya bugo waya. Ta wani mai sa kai ya bugo waya ya yi mana tambaya kan ko a iya canza kudin Japan a cikin injin ATM a nan birnin Beijing.Liu Qing ya ba da taimakonsa wajen fassara,har bakon ya warware matsalarsa. Bayan da ya ajiye wayar,Liu Qing ya yi wa wakilin gidan rediyo na kasar Sin bayani kan yadda ya ba da taimako ga wani dan kasar Japan da ya nemi taimako wajen fassara,daga baya wannan dan kasar Japan ya daidaita matsalar da yake fama da ita a nan kasar Sin. " wani dan kasar Japan dake kwana a wani masaukin baki ya wanke tufafinsa a cikin wani kanti,amma takardar shaida da aka ba shi domin dawo da tufafin ta bace. Yana damuwa in ba ya samu tufafinsa,daga bisani ya bugo mana waya." Daga baya Liu Qing ya bayyana ra'ayinsa kan aikin sa kai na fassara. Ya ce "Babban nauyin da ke bisa wuyanmu shi ne ba da hidima wajen yin fassara.Da japannawa suka sauka a kasar Sin, su kan samu matsalar Magana da sinanci,haka kuma su kan samu matsaloli.Idan sun buga mana waya a wannan lokaci, za mu iya ba da taimako wajen warware matsalolin da suke fama da su,su ma sun yi farin ciki da samu taimako. Abin da muka yi ya kan burge su,su kan samu ra'ayi mai kyau ga kasar Sin.Mu masu sa kai mu ba da taimakonmu yadda ya kamata."

Da karfe daya na yamma,lokaci ne na cin abinci a cibiyar ba da hidima, duk da haka masu sa kai na cibiyar ba su tashi daga aiki su ci abinci ba,aka kawo musu abinci su kan ci a ofis.dalili kuwa shi ne da akwai wayoyi da dama a wannan lokaci, a bukaci ma'aikata masu sa kai su kasance a cikin ofisi. Wannan kuma alkawari ne da kwamitin wasannin Olympics na birnin Beijing ya dauka ga duniya,Liu Qing da abokansa darurruwa masu fassara suna cikin ofishin su tabbatar da alkawarin da aka dauka.

A lokacin da ake yin gasar wasannin Olympics a nan birnin Beijing,babban birni na kasar Sin da akwai ma'aikata masu sa kai dubu dari dake aiki a wuraren gasa,da masu aiki sa kai dubu dari hudu a cikin birni da sauran ma'aikata masu sa kai sama da miliyan ke aiki domin tabbatar da gudanarwar wasannin Olympics lami lafiya,ban da wannan kuma da akwai mutane dubu dari biyu da suke sa kaimi ga 'yan wasa da suke yin takara a filayen gasa, dukkansu sun ba da taimakonsu ga wadanda suka bukata a fannoni daban daban. Sun bayyana wa duniya murmushin kasar Sin da na birnin Beijing.Yin Liang,wani saurayi ne day a zo nan birnin Beijing daga lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin ya yi aikin sa kai cikin birnin

Wani matafiya ya zo gabansa ya yi masa tambaya cewa "ko akwai ofishin da sayar da tikitin lambun yin wasannin nishadi na Shijingshan a wannan wuri?" Yin Liang ya ba da amsa cewa "Lambun yin wasannin nishadi na Shijingshan? Idan ka tafi kai tsaye za ka iya samu."

Yin Liang,wani ma'aikaci kamar sauran ma'aikata na reshen Beijing na kamfanin China Mobile Group. Shekaru biyu kenan da yake aiki a wannan reshen, da ya samu labarin kamfani na daukar masu aikin sa kai domin wasannin Olympics na birnin Beijing. Ba tare da shakku bay a yi rajista nan da nan. Daga farkon watan Yuli zuwa halin yanzu yana yin aikin sa kai a wani shagon da aka kafa a kan gefen tituna. Da aka takalo Magana kan aikinsa na sa kai a cikin birni domin ba da taimako ga wasannin Olympics na Beijing, Yin Liang ya yi farin ciki da cewa "Da na shiga wannan kaya mai launin shudi da aka ba ni domin wasannin Olympics,na yi farin ciki kwarai da gasket. Da ma ba ni da damar shiga harkokin wasannin Olympics,ga shi a yau na samu wannan dama,na sa rigar da sauran ma'aikata masu sa kai suka sa, ina aikin sa kai tare da su. Da na ga baki dake yawon shakatawa a Beijin ko su zo daga sauran wurare na kasar Sin ko daga sauran kasashen dudniya,na isar musu da sakonni game da wasannin Olympics na Beijing, ina farin ciki kwarai da gasket.

A duk lokacin da ake yin wasannin Olympics a nan birnin Beijing, da akwai tasoshin ba da hidima sama da dari biyar da suke shifidu a gefuna titunan birnin Beijing. A cikin kowace tasha da akwai ma'aikata masu sa kai sama da goma da suke ba da taimakonsu wajen fassara da samara da bayanai ga baki masu yawon shakatawa da suka zo daga sauran kasashen dudniya da biya bukatunsu a fannoni daban daban.Ma'aikatan masu sa kai da suke aiki a wannan tasha sun kasu kashi biyu. Kashi na farko,ma'aikata masu sa kai da reshen Birnin Beijing na kamfanin China Mobile group ya zaba,su ba da taimakonsu ne wajen warware matsalolin da baki ke fama da su wajen sadarwa kamar wayoyin salula. Kashi na biyu ma'aikata masu sa kai da suka zo daga manyan makarantun sakandare da jami'o'i. Yin Liang ya bayyana cewa " ma'aikata masu sa kai da suka zo daga makarantu su kan samara da bayanai ga matafiya.kamar su su ba da bayanai kan dakunan wasannin Olympics da gasar wasanni. Aikinmu shi ne mu ba su ilimi na musamman da na sadarwa. Idan sun gabatar da bukatunsu na yin waya,amfani da wayar tafi da gidanka a nan birnin Beijing da wayar zuwa sauran kasashen duniya,za mu iya bas u bayanan da suke bukata.