Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-09 15:37:01    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Likitan jabu ya samu daurin shekaru goma a gidan wakafi.kwanakin baya an yanke hukuncin daurin shekaru goma a gidan kurkuku kan wani mutum da ya samar da magani ba bisa doka ba.mutumin nan shi ne Zhan Changkui mai yawan shekaru 46 da haihuwa ya ba da magnin wanda ya haddasa mutuwar wata mata.Zhan ya kafa wani dakin magani a wurin Qingzhen ba tare da samu izni daga hukumar kula da lafiyar jama'a ba. Da wata mata mai suna Xiong da ke da shekaru 55 da haihuwa ta zo daki neman magani domin ciwon hakora.sai ya ba ta ta sha bayan kwanaki kadan matar ta mutu.wani jami'I na hukumar da abin ya shafa ya tabbata cewa matar ta mutu ne saboda maganin da ta sha ba daidai ba.

Wata tsohuwa ta sami diya. An sami wata tsohuwa a birnin Guiyang,babban birni na lardin Guizhou dake kudu maso yammancin kasar Sin,tana da shekaru 87 da haihuwa, ba ta da da ko diya ko daya,amma ta yi farin ciki da ta samu wata diya a shekara ta 1998,diyarta makwabciyarta ce dake zama kusa da ita.tun daga wannan shekarar wannan makwabciya da ta dauka a matsayin diyarta tana kula da ita kamar mamarta ta haihuwa.ta shirya mata abinci da tufafi da gidan kwana ta biya bukatunta yadda ya kamata,shi ya sa wannan makwabciya ta samu yabo daga mutanen wuri da gwamnatin.

Kadanci ya sa mai laifi ya tuba.Wani mutum mai suna Li Weidong a birni Xi'an,babban birni na lardin Shaanxi dake arewa maso yammancin kasar Sin ya mika kansa ga 'yan sanda na wuri a ranar talata da ta shige a karkashin rakiyar 'yan jarida biyu da suka shawo kansa da ya amsa laifinsa. Li Weidong ya aikata laifi ne na cin hancin kudin da ya kai kudin Sin Yuan dubu dari hudu yayin da yake aiki a matsayin mai kula da kudi a wata tashar samar da timba a shekara ta 1986.A ran 15 ga watan Mayu na shekara ta 1990 da ya samu labarin binciken kudi,sai ya gudu zuwa Wuhan,babban birnin lardin Hubei na kasar Sin,ya yi zaman gudun hijira na shekaru 18. bayan da ya koma gidansa a ranar talata da ta shige,ya buga waya zuwa ga ofishin wata jaridar wurin,nan take aka tura 'yan jaridu biyu zuwa gidansa.Li ya gaya wa 'yan jaridun cewa "na yi shekaru 18 na yi zaman kadanci ina tsoron yin mu'amala da 'yan iyalina,ina begensu ainun ina so in sa aya ga zamana na gudun hijira."

Wani yaro yana fama da rashin lafiya saboda abinci. Wani yaro mai yawan shekaru goma yana neman magani domin yana sha wahala wajen yin numfahi a asibitin jama na birnin Nanjing,babban birni na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin a ranar alhamis da ta wuce. Yaron yana kwadayin abinci sosai musamman yayin da yake kallon talabijin ya kan ci abincin kara-kara kamar chocolate da barasa mai dadi.kwanakin baya ya sha wahala wajen yin numfashi a yayin da yake hawan gini mai benaye.da ganin haka iyayensa sun kai shi asibiti. Bayan da aka yi masa bincike,likitan ya gano cewa yaron yana fama da ciwon hauhawar jini da na sukari.