Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-09 15:33:25    
Zaman rayuwar iyalin Na mai dadi

cri

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 50 da aka kafa jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta kasar Sin, da kuma cika shekaru 30 da aka soma gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar. A cikin shekarun nan, musamman ma a kusan shekaru 30 da suka wuce, an samu sauye-suye sosai a nan kasar Sin, musulmi 'yan kabilar Hui fiye da miliyan 1.9 da ke zama a jihar Ningxia suna ta samun kyautattuwar zaman rayuwarsu a kwana a tashi kamar jama'ar sauran kabilu. Kwanan baya, wakilanmu sun kai ziyara a jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui da ke yammacin kasar Sin, tun daga ran Alhamis na wannan mako kuma, za mu soma kawo muku shirye-shirye a jere dangane da zaman rayuwar iyalai musulmi guda hudu na kabilar Hui. A cikin shirinmu na yau kuma, za mu gabatar muku daya daga cikinsu, wato zaman rayuwar iyalin Na mai dadi.

Kamar sauran musulmi na jihar Ningxia, a 'yan shekarun da suka wuce, iyalin malam Na Dianfu da ke birnin Yinchuan na jihar ya samu sauye-sauye sosai kan zaman rayuwarsu. A hankali a hankali malam Na Dianfu ya zama wani babban manaja na kamfanin ba da hayar motoci daga wani manomi. Yanzu, kamfaninsa ya samu babban cigaba, yana da karfi sosai wajen tattalin arziki, saboda haka, ya sabunta gidansu, da kayayyakin gida, da kayayyakin aiki na lantarki, da dai sauransu. Malam Na Dianfu ya gabatar da cewa,

'Na sayi wannan gida ne, saboda akwai mutane da yawa a iyalina, don haka, na sayi wannan babban gida mai muraba'in mita fiye da 180, lallai yana dacewa sosai."

Gidan malam Na Dianfu na da benaye biyu, yana da muhalli mai kyau, ana shuka furani da itatuwa a yadi, an hada da sigar musulmi da ta zamani a duk gidansa.

Malam Na Dianfu ya kawo wa wakilanmu baya ni game da sauye-sauyen da aka samu a gidansa a sakamakon yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A halin da ake ciki na gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, gwamnatin wurin ta kaddamar da manufofi da yawa don nuna gatanci ga kananan kabilu wajen raya sana'o'i, kamar su bayar da kananan rancen kudi na raya sana'o'i, da rage haraji, da dai sauransu. A sanadiyar haka, tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, malam Na Dianfu ya soma raya sana'arsa tare da dansa a birane, sun taba zaman magina, bayan da suka samu fasahohi da kudi, sai malam Na Dianfu ya nemi ma'aikata, don soma aikin kwangila. Bayan da suka samu isasshen kudi kuma, iyalin Na ya kafa wannan kamfanin ba da hayar motoci. Yanzu, 'yan shekaru da suka wuce, kamfaninsu ya samu bunkasuwa sosai. Malam Na Dianfu ya gaya wa wakilanmu cewa,

"Kafin aka soma gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, ba mu da isasshen kudi ba. Daga baya, na fita daga gida tare da 'dana, don yin aikin kwangila, tun daga lokacin kuma, yawan kudin da muka samu a ko wace shekara ya kai kusan dalar Amurka dubu 80."

Bisa kyautatuwar zaman rayuwarsu, malam Na Dianfu yana fatan cimma wani buri na babansa, wani tsoho 'dan shekaru kusan 70, wato tafi Makka, don yin hajji. A shekarar 1997, Na ChangJin, wato baban malam Na Dianfu ya cimma burinsa a karshe. Na Changjin ya gayawa wakilanmu cewa,

"Bayan da na isa Makka, na yi mamaki sosai, mutane da suka yi hajji a wurin sun kai sama da miliyan 2.8, na gamu da musulmi masu launin fata iri iri daga kasashe daban daban, idan babu manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, to, ba zan isa wurin da jirgin sama ba, kuma ba zan gamu da wadannan mutane da yawa ba, lallai na yi farin ciki sosai a lokacin."

Tsoho Na Changjin ya waiwayo cewa, a shekaru goma da suka wuce, ba a cim ma burin zirga zirgar jiragen sama kai tsaye a tsakanin birnin Yinchuan da kasar Saudi Arabia, tilas ne bayan da aka yi musayar jirage da motoci sau da yawa za a isa Makka. Amma, ya kasance da bambanci sosai a tsakanin tsoho Na Changjin, da malama Ding Xiumei, wato matan malam Na Dianfu wajen hanyar yin hajji. A 'yan shekarun da suka wuce, a kaikashin taimakon da hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin jihar Ningxia suka bayar, kungiyar yin hajji na musulmi na jihar Ningxia sun cimma burinsu na tabbatar da zirga-zirgar jiragen saman shata a tsakanin birnin Yinchuan da Makka. Kungiyar yin hajji na kunshe da masu fassarawa, da masu aikin likitanci, har ma da limamai daga masallatai daban daban na jihar, ta yadda aka samar da sauki ga musulmi. Malama Ding Xiumei ta tafi Makka don yin hajji ne a shekarar 2007, ta waiwayo cewa,

"A shekarar 2007, mun tafi Makka na kasar Saudi Arabia daga filin jiragen sama na Yinchuan kai tsaye, mun yi amfani da kwanaki fiye da 30 kan aikinmu, likitoci, da masu fassarawa dukkansu sun fito daga majalisar musulunci ta birnin Yinchuan, ban da wannan kuma, akwai limamai daga masallatai daban daban. "

Idan ana cewa, musulmi da yawa suna iya cimma burinsu na yin hajji, wannan na nuna canjewar zaman rayuwarsu, to, bikinsu shi ma ya nuna canjewar zaman rayuwarsu a fanni daban. Ranar da wakilanmu suka kai ziyara ga iyalin Na Dianfu, rana ce ta biyu ta ibada azumin Ramadan, duk iyalin Na suna sa sabbin tufafi, dukkansu suna jin farin ciki. Thoho Na Changjin ya gayawa wakilanmu cewa,

"Jiya ranar shagulggullan karamar salla, masallatai na cike da mutane, mun kashe wasu shannu. Bayan haka kuma, gwamnatin jiharmu ta ba mu shinkafa, da taliya , da kuma mai da yawa."

Ta iyalin malam Na Dianfu, muna iya ganin halin da duk iyalan musulmi na kasar Sin ke ciki, a yankunan da musulmi ke taru a nan kasar Sin, kuma a duk kasar Sin, mutane na ko wane kabila suna jin dadi kan sakamakon da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ke kawowa.