Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-08 16:33:30    
Birnin Beijing ya soma ayyukan al'adu a jere don maraba da wasannin Olimpic

cri

A ranar 8 ga watan Augusta na shekarar da muke ciki, za a yi bikin budewar wasannin Olimpic na karo na 29 a nan birnin Beijing. Don maraba da zuwan kasaitaccen taron, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin da kwamitin wasannin Olimpic na birnin Beijing sun tsai da kuduri cikin hadin guiwa, inda aka bayyana cewa, daga watan Maris zuwa watan Satumba, birnin Bejing zai shirya manyan ayyukan al'adu domin wasannin Olimpic, da kuma gayyaci masu fasahohi fiye da dubu 20 da za su zo daga kasashe da jihohi fiye da 80 don zuwan birnin Bejing da kuma nuna nagartattun wasanni har da yawansu ya kai 260 ko fiye, a sa'i daya kuma, za a shirya manyan nune-nune na gida da na waje da yawansu ya kai 160. An kimanta cewa, yawan 'yan kallon da za su halarci wadannan aikace-aikace zai kai miliyan 4 ko fiye.

Sa kaimi ga haduwar al'adu da wasannin motsa jiki gu daya kullum yana zama al'adar wasannin Olimpic. Bisa babban tsarin wasannin Olimpic na zamanin yau, an bayyana cewa, manyan bangarori uku na yin wasannin Olimpic sun hada da wasan motsa jiki da al'adu da ba da ilmi. Ta hanyar shirya aikace-aikacen al'adu na wasannin Olimpic, birnin da ke samun damar shirya wasannin Olimpic ya yada al'adun kasarsa zuwa kasashen ketare da kuma shigar da al'adun kasashen waje a cikin kasarsa, wannan na da amfani ga ciyar da ma'amalar al'adun kasa da kasa gaba. Aikace-aikacen al'adun wasannin Olimpic da aka yi a wasannin Olimpic na Sidny na shekarar 2000 da wadanda aka yi a wasannin Olimpic na Athens na shekarar 2004 dukkansu sun sami babbar nasara. Masu fasaha na kasar Sin su ma suna soma busa kahon wasannin Olimpic, suna fatan za su kara haske ga wasannin Olimpic cikin nasara tare da masu fasahohin da suka zo daga kasashe daban daban na duniya.

Manyan ayyukan al'adun na wasannin Olimpic na birnin Bejing na shekarar 2008 sun kasu fannoni biyu na gida da waje, wajen kashin kasar Sin, an riga an soma ayyuka a watan jiya, wajen kashin kasashen duniya, za a soma su ne daga ranar 23 ga watan Yuni. Nuna wasanni iri iri da yawa da nagartattun nune-nune da tattaunawa da shirya taron dandalin tattaunawa da sauran ayyukan da za a yi a karkara za su sa jama'ar Sin da bakin da suka zo daga kasashen duniya za su more nishadi daga wajen al'adu.

Wani jami'in al'adu na kasar Sin da ke kula da harkokin nuna wasannin mai suna Yang Xiong ya bayyana cewa, wasu manyan gidajen nuna wasannin fasaha da wasu kungiyoyi na wurare daban daban na kasar Sin sun nuna himma ga shigar da wasannin da za a shriya, yanzu yawan wasannin da za a zabe su don shiga nuna wasanni ya kai 500 ko fiye. Bayan zaben da aka yi, watakila yawan wasannin da za a nuna su ya kai 150, daga cikinsu da akwai wasannin Opera na kasar Sin da kuma wasannin kwaikwayo na gargajiya na wurare daban daban na kasar Sin da ke da halayen musamman, wato kidan simphony da wasannin kwaikwayo da za a yi cikin kide-kide da wake-wake da sauransu. Kananan kabilu fiye da 50 na kasar Sin su ma za su nuna al'adunsu da ke da halayen musamman. Mr Yang Xiong ya bayyana cewa, a karon nan da za mu nuna wasannin fasaha , da akwai halayen musamman guda uku. Na farko, za a wakilci bangarori da yawa. Na biyu, za a nuna wasanni bisa matsayin koli, na uku, mutane da yawa za su more nishadi daga wajen wasannin da za a nuna.

Daga ranar 10 ga watan Yuni, lardin Fujian da Sichuan da Anhui da Kwangdong da sauran wurare na kasar Sin za su aika masu fasahohinsu zuwa nan birnin Beijing don nuna wasanninsu har karo 12, sa'anan kuma za a nuna Tangka na kabilar Tibet da takardun da aka yanke su ta hanyar yin amfani da almakashi na kabilar Han . Wani jami'in da ke daukar nauyin kula harkokin wadannan ayyuka mai suna Zhang Qingshan ya bayyana cewa, wadannan wasanni suna da halayen musamman na jama'ar wurare daban daban na kasar Sin, kuma an nuna su bisa salon zamanin da sosai, daga cikinsu da akwai raye-raye da wake-wake na gargajiya da wasannin mutum mutumi da sauran wasannin kwaikwayo, yawancinsu wasanni ne na tarihi na al'adu ba kayayyaki ba.

Ban da kashin wasannin Olimpic da za a yi a cikin gidan kasar Sin, sa'anan kuma da akwai sauransu da za su zo daga kasashen waje, wato wasunsu da za su zo daga kasar Rasha da Amurka da Spain da Italiya da sauran kasashe. Wani manajan kamfanin kula da harkokin wasannin da za su zo daga kasashen waje mai suna Zhagn Yu ya bayyana cewa, wasannin Olimpic biki ne na duk duniya. Mun shirya wasannin raye-raye da wake-wake da suka zo daga wurare daban daban na duniya tare da halayen musamman daban daban a dakalin nuna wasanni na kasar Sin, wato za mu shirya shagalin dare na irin Asiya da na Afrika da na Latin Amurka da na Larabawa da dai sauransu.

Kasar Greece kasa ce da ta soma shirya wasannin Olimpic, kuma ita ce babbar bakuwar wasannin Olimpic na aikace-aikacen al'adu na kasar Sin. Jakadan kasar da ke wakilci a kasar Sin Michael Cambanis ya bayyana cewa, an mayar da kasar Greece bisa matsayin babbar bakuwar ayyukan nan, wannan ba ma kawai na da mama'a sosai gare ta ba, hatta ma ya zama abin shaida ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.(Halima)