Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-08 16:32:05    
An kammala aikin zaben wakokin wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 tare da cikakiyyar nasara

cri

Bayan birnin Beijing ya yi nasarar samun damar shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008 a ranar 13 ga watan Yuli na shekarar 2001 har zuwa yanzu, kasar Sin ta yi ta shirya manyan aikace-aikace dangane da wasannin Olimpic da yawa , aikin tattara wakokin wasannin Olimpic da kuma zaben wasu nagartattu daga wajensu ya zama daya daga cikinsu. Ya zuwa shekarar da muke ciki, an riga an yi nasarar shirya aikin tattara wakoki har sau hudu . A lokacin da ranar da ta rage kwanaki 100 da za a fara wasannin Olimpic na Beijing, an shirya shagalin dare na nuna wasannin fasaha a fadar al'adun jama'a ta birnin Beijing don murnar ranar da ta rage kwanaki 100 da za a shirya wasannin Olimpic na shekarar 2008, kuma an bayar da sakamakon da aka samu wajen zaben wakoki har sau huhu.

Shahararrun mawaki na kasar Sin ne suka rera wakar "Beijing ya maraba da kai" ta hanyar musamman don gayyatar da dukkan mutanen duniya da kuma kara karfi ga wasannin Olimpic ta hanyar wakoki. Mai tsara kidan wakar shi ne Xiao Ke wanda aka haife shi a nan birnin Beijing, ya yi amfani da salon wakar gargajiya da ke da halayen musamman na birnin Beijing wajen tsara kidan da ke da karin sauti 9 a karshen wakar don tayar da himma sosai daga jama'a. A cikin al'adun gargajiyar kasar Sin, alamar 9 alama ce mafi girma, ta wakilci dogon lokaci tare da nuna fatan alheri. Mr Xiao Ke ya bayyana cewa, ana iya rera wakar nan cikin sauki, tsofaffi da yara ma za su iya rerawa, Ya ce, wakar nan waka ce ta gargajiyar kasar Sin sosai, ana yin amfani da salon kasar Sin don tsara wakar mutanen kasar Sin, tsara kidan wakar tamkar yadda aka dinki wata rigar da ke sanyawa a jikin mutum, a ganina, abu mai muhimmanci shi ne ya kamata mutumin kasar Sin ya sanya wata rigar da ke dacewa da kasar Sin, amma ba mutumin ketare ya sanya wata rigar da ke dacewa da kasar Sin ba.

Mawaka da yawansu ya kai 100 su ne suka rera wakar cikin hadin guiwa, wata shaharariyar zabiya ta Hongkong mai suna Mo Wenwei ta yi farin ciki da bayyana cewa, na yi alfahari da samun damar nuna wasanni don murnar ranar da ta rage kwanaki 100 da za a shirya wasannin Olimpic, a ganina, babbar ma'anar nan ita ce, mun iya hada wakoki da wasannin motsa jiki gu daya, sa'anan kuma za mu more su tare da duk duniya.

A cikin wakokin da aka zaba a farkon karo uku , da yawa da aka rubuta cewa, "Birnin Beijing yana maraba da kai !" Tun daga ranar da kasar Sin ta yi nasarar samun damar shirya wasannin Olimpic har zuwa yanzu, jama'ar kasar Sin suna cika alkawarinsu dangane da "Beijing ya maraba da kai".Daga babban filin wasan motsa jiki na kasar Sin da ke da sifar gidan tsuntsaye zuwa cibiyar wasan iyo ta kasa mai sifar tafkin ruwa da ke da kusurwoyi hudu kuma ake kira " water Cube" cikin turanci, su ne sakamakon da jama'ar kasar Sin suka samu ta hanyar hada kai da aminansu na kasashen ketare da bude wa kasashen waje kofa. Ya zuwa shekarar da muke ciki, an riga an yi nasarar shirya gasar zaben wakokin wasannin Olimpic har sau hudu, shugaban sashen kula da harkokin al'adu na kwamitin wasannin Olimpic na birnin Beijing Mr Zhao Dongming ya bayyana cewa, daga shekarar 2003, an soma tattara wakokin wasannin Olimpic, ya zuwa yanzu, an riga an yi aikin har sau hudu, a kowane karo, mun sami wakoki masu dadin ji da yawa.

An yi karo na hudu na zaben wakokin wasannin Olimpic daga ranar 21 ga watan Janairu na shekarar bara zuwa ranar 10 ga watan Maris na shekarar da muke ciki. Yawan kide-kiden da aka samu a karon ya kai 3151, yawan wake-waken da aka samu a karon ya kai 64000, a karshe dai an nuna yabo sosai ga kide-kide da wake-wake da yawansu ya kai 30.(Halima)