Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-08 16:30:22    
Wani bikin da ke cikin bukukuwa 24 na yanayin sararin samaniya na kasar Sin, wato ranar bikin kawo karshen yanayin zafi da ake cewa "Chushu"

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu yi bayani kan ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya na kasar Sin. Game da ranar bikin yanayin sararin samaniya, an bayyana cewa, bisa sauyawar yanayin sararin samaniya da yawan ruwan sama da ake samu da tsawon lokacin saukar jaura da dai sauran almomin halittu ne, aka raba shekara guda don ta zama da matakan lokutan bayyana al'amomin yanayin sararin samaniya lokaci lokaci. Ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya su ne ranakun somawar wadannan matakan lokutan bayyana al'amomin yanayin sararin samaniya. Tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya shi ne sakamakon da jama'ar zamani aru aru na kasar Sin suka samu a lokacin da suke duddubawa tare da yin nazari kan ilmin yanayin sararin samaniya . Wannan yana da tasiri mai muhimmanci sosai ga harkokin noma. Bisa bayanan da aka tanada, an rubuta cewa, a shekarar 104 kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S), mutanen kasar Sin sun riga sun tsara tsarin ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya, don tunawa da su sosai, mutanen zamanin da sun kuma tsara wakoki dangane da ranakun bukukuwan yanayin sararin samaniya.

Bikin kawo karshen yanayin zafi wato bikin "Chushu" ya kan soma daga ranar 22, ko 23 ko 24 ga watan Augusta a kowce shekara. Bikin kawo karshen yanayin zafi wato "Chushu" na shekarar da muke ciki zai zo ne a ranar 23 ga watan Augusta. Bikin shi ne biki na biyu da ya zo bayan ranar shiga yanayin kaka. Ma'anar kalmar "Chu" a nan cikin Sinanci ita ce karshe. A cikin kalandar gargajiya ta zamani aru aru na kasar Sin, an bayyana cewa, da bikin ya zo, to ranakun yanayin zafi sun kare.

Kafin ranar kawo karshen yanayin zafi ko bayanta, a kudancin kasar Sin, zafin yanayi bai huce ba, har zuwa ranar, zafin rana yana ci gaba da kasacewa da yawansa ya kai centigrade 22, amma iska mai sanyi ya kara saukowa a kudancin kasar Sin, kuma zafin ranaku ya ragu da sauri, sannu a hankali yanayin sararin samaniya ya kara dan sanyi, saboda haka, a zamani aru aru na kasar Sin, an mai da bikin bisa matsayin nuna alamar somawar yanayin sanyi. Muhimmiyar alamarsa ita ce, zafin ranaku yana sanyi a dare. An bayyana cewa, dalilin da ya sa hakan ya faru shi ne saboda ba a sami isasshen zafin rana ba. A arewacin kasar Sin, saboda busasshiyar iska ta taso, kuma hasken rana na da yawan gaske, gizagizai ba su da yawa, sai zafin rana da na dare suna kasancewa cikin banbanci sosai. A dare, zafin ranaku ya kara sanyi, amma ba sosai ba. A kudancin kasar Sin, yanayin kaka ya kan zo ne bayan na arewacin kasar Sin, a lokacin zuwan ranar kawo karshen yanayin zafi, zafin ranaku yana ci gaba da kasancewa cikin zafi. Akwai wani karin magana na shiyar kogin Yangtse da ke kudancin kasar Sin da ya bayyana cewa, a lokacin zuwan bikin kawo karshen yanayin zafi, a kai a kai ne za a sami kwanukan ruwa 18, kuma zafin ranaku yana raguwa a kwana a tashi, wato kamar a ce, bayan wanka da aka yi ta hanyar yin amfani da ruwan sanyi da yawansu ya cika kwanuka 18, sai yanayin zafi ya kan yi dan sanyi a kai a kai, duk saboda lokacin da ya shige bayan kwanaki 18, sai ya shiga wani yanayin sararin samaniya daban, wato bikin "Bai Lu", zafin rana da na dare sun kara banbanci a tsakaninsu, kuma ruwan raba ya daskare, irin wannan sharadin halitta , wato a rana , ana samun dumi, amma a dare ana samun sanyi, wannan na da amfani sosai ga amfanin gona wajen kamawarsu, saboda haka a kasar Sin da akwai wani karin magana da cewa, gonakin da tsire-tsire suka kama ya samu sauyawa jim kadan kawai, wato a lokacin da ya ketare dare kawai, sai ya sami sauye-sauye sosai..

Ya zuwa ranar bikin yanayin kaka, sai ayyuka sun kara yawa ga manoma. Gero da masara da dawa da sauransu sun nuna bi da bi a arewacin kasar Sin, har ma an soma cire auduga, a kudancin kasar Sin, an soma girbar shimkafa, kuma ya kamata ana kara kula da gonakin da aka shuka dankali, manoma suna kan cewa, ayyuka na da yawan gaske a yanayin kaka da yanayin kawo karshen zafi, duk saboda bayan girbar shimkafa, sai a shiga cikin ayyukan shuka sauran amfanin gona.

In ana ruwa a wannan lokaci, to zai kawo tasirin banbanci a tsakanin kudancin kasar Sin da arewacin kasar Sin. A arewacin ksar Sin, in a wannan lokaci an sami ruwan sama, to tsire-tsiren gonaki za su kama sosai, kuma tabbas ne za a sami girbi mai armashi sosai, amma a kudancin kasar Sin, a cikin lokacin yanayin kaka, in ba a sami ruwan sama, to za a sami rabin girbi, amma in lokacin kawo karshen yanayin zafi ya zo, amma ba a sami ruwan sama ba, to tabbas ne ba za a sami girbi mai armashi ba.(Halima)